Brighton ta doke Manchester City a Firimiyar Ingila
Manchester City na mataki na biyu a gasar da maki 23.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Brighton & Hove Albion ta doke Manchester City da ci 2 da 1 a Gasar Firimiyar Ingila.
Kungiyoyin biyu sun kara da juna ne a gidan Brighton da yammacin ranar Asabar.
- Babu wata addu’a da na shirya kan matsin rayuwa — Remi Tinubu
- HOTUNA: Mayaƙan Lakurawa sun kashe mutum 17 a Kebbi
Erling Haaland ne ya fara jefa wa Manchester City ƙwallo a minti na 23 da fara wasa, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Joào Pedro ya warware ƙwallon a minti na 78.
A minti na 83 ne Matt O’reilly ya ƙara ƙwallo ta biyu a raga Manchester City.
Yanzu haka dai Manchester City na mataki na biyu a teburin Gasar Firimiyar Ingila da maki 23 daga wasanni 11.
Liverpool ce ke jan ragamar teburin gasar da maki 25 daga wasanni 10, idan ta yi nasara a wasanta na ranar Lahadi, za ta bai wa Manchester City tazarar maki biyar.
Ita kuwa Brighton tana mataki na huɗu a teburin Gasar daga wasanni 11 da ta buga da maki 19.