Browne Jr ya mutu bayan ya sha kashi a damben boksin
Wani dan wasan damben boksin dan kasar Austireliya ya mutu kwana hudu bayan da aka doke shi ya fadi magashiyan a karawar da ya yi a Sydney.Carlo Magali na Philippines ne ya yi wa Dabey Browne Jr mai shekara 28, bugun kwaf daya a turmi na 12.Browne mahaifin ’ya’ya biyu ya kasa farfadowa daga suman […]
Wani dan wasan damben boksin dan kasar Austireliya ya mutu kwana hudu bayan da aka doke shi ya fadi magashiyan a karawar da ya yi a Sydney.
Carlo Magali na Philippines ne ya yi wa Dabey Browne Jr mai shekara 28, bugun kwaf daya a turmi na 12.
Browne mahaifin ’ya’ya biyu ya kasa farfadowa daga suman da ya yi, dalilin da ya sa na’urar da take taimaka masa yin numfashi ta kashe kanta.
kungiyar likitocin Austireliya ta yi kira da a soke wasan damben boksin sakamakon mutuwar da Browne din ya yi.
Browne ya mutu ne wata shida bayan da wani dan damben Austireliya Braydon Smith na kueensland ya fadi a filin dambe ya mutu a gasar cin kambun matsakaita nauyi a garinsa na Toowoomba.