BST za ta ci gaba da tallafa wa mata a yankin Arewa maso Gabas – Laftanar Janar T.Y Danjuma
Shugaban Kula da kudaden tallafa wa wadanda rikicin Arewa maso Gabas ya rutsa da su (BSF), Laftnar Janar T.Y Danjuma mai ritaya ya kara nanata cewa za a ci gaba da tallafa wa mutanen yankin Arewa maso Gabas da kudaden hukumar, musamman mata. Janaral danjuma ya sanar da hakan ne a ranar 22 ga watan […]
Shugaban Kula da kudaden tallafa wa wadanda rikicin Arewa maso Gabas ya rutsa da su (BSF), Laftnar Janar T.Y Danjuma mai ritaya ya kara nanata cewa za a ci gaba da tallafa wa mutanen yankin Arewa maso Gabas da kudaden hukumar, musamman mata. Janaral danjuma ya sanar da hakan ne a ranar 22 ga watan Nuwamba a garin Gombi da ke Jihar Adamawa a lokacin bikin kaddamar da shirin tallafawa mata na bana wanda suke daukar nauyi.
danjuma, wanda ya samu wakilcin sakataren bSF, Ambasada John Gana, ya ce za a yi amfani da kudaden ne wajen ganin mutanen da rikicin ya rutsa da su sun dawo garuruwansu kuma sun ci gaba da rayuwa kamar yadda suka saba, sannan kuma ya bukaci matan da suka ci moriyar tallafin da su yi amfani da kudin yadda ya kamata domin su samu jarin da za su fara kasuwanci ko da kanana ne a lokacin da ake ci gaba da samun zaman lafiya a garuruwansu.
Kamar yadda babban daraktan bSF, Farfesa Sunday Ochoche ya sanar, mata 5,000 sun ci moriyar shirin ya zuwa yanzu a Jihar Adamawa, wanda ya hada da mata 2,000 a shekarar 2016, da mata 3,000 bana. Ya ce bSF ta kara inganta shirinta ta hanyar kara kudade da tsare-tsare, inda suke nufin tallafawa mata a garuruwan da suka dawo.
“Mata 3,000 da suka ci moriyar shirin bana, kowa zai samu Naira 30,000, wanda za su yi amfani da shi wajen fara kasuwanci” a nata jawabin, daraktan tsare-tsare na bSF, Farfesa Nana Tanko, ta sanar da cewa wadanda suka ci moriyar shirin, sannan ta bukace su da su yi amafani da tallafin yadda ya kamata, domin su kara samun wani tallafin. Ita kuma madam Martha Hussaini, ta nuna godiya ga bSF bisa wannan tallafin, sannan ta yi alkawarin cewa za su yi amfani da tallafin yadda ya kamata.