BUA ya bai wa manoma tallafin kayan noma na N100m a Sakkwato
Kamfanin ya ce ya yi haɗin gwiwa da gwamnatin jihar domin bai wa manoma horo kan noman zamani.
Kamfanin Siminti na BUA ya raba wa manoma 211 da ke zaune a ƙauyukan da ke kewayen kamfanin a Jihar Sakkwato, kayan noma na kimanin Naira miliyan 100.
An ƙaddamar da shirin ne domin taimaka wa manoma su ƙara yawan amfanin gona, musamman waɗanda aka sauya musu wajwn zama da gonaki sakamakon ayyukan kamfanin.
- Gidauniyar Dahiru Mangal ta tallafa wa marasa lafiya 30,000 a Katsina
- ’Yan bindiga sun kashe limami da wasu mutum 3 a Sakkwato
A wajen rabon tallafin da ya gudana a ranar Asabar, Babban Daraktan kamfanin, Injiniya Yusuf Binji, wanda Alhaji Sada Suleiman, Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a ya wakilta, ya ce BUA zai ci gaba da tallafa wa al’ummomin da ayyukanta suka shafa.
Ya ce manufar shirin ita ce rage wahalar da mutanen suka fuskanta bayan sauya musu matsuguni tare da ƙarfafe su domin su ci gaba da noma.
Daraktan Lafiya na kamfanin, Ali Gumel, ya buƙaci waɗanda suka amfana su yi amfani da kayan yadda ya kamata.
Ya kuma bayyana cewa BUA ya haɗa kai da Hukumar Bunƙasa Noma ta Jihar Sakkwato (SADP) domin horas da manoman dabarun noma na zamani.
Shi ma Manajan SADP, Alhaji Abubakar Danmaliki, ya tabbatar da cewa za su ci gaba da bai wa manoman shawarwari da kuma ziyartar gonakinsu domin tabbatar da suna amfani da ilimin da suka koya.
A cewar Alhaji Rabi’u Maska, kayan da aka raba sun haɗa da buhunan takin NPK 422, buhunan Urea 211, kwantena 211 na takin zamani, magungunan kashe ciyawa da ƙwari, da kuma irin shinkafa, masara, gero, dawa, gyada da zogale.
Manoman da suka amfana sun gode wa kamfanin BUA, suna mai cewa tallafin ya zo a daidai lokacin da suke buƙatarsa domin fara noman damina.