BUA ya raba wa asibitoci magunguna a Sakkwato
Nan gaba kaɗan za mu ƙaddamar da rijiyoyin burtsatse guda 7 masu amfani da hasken rana a faɗin Sakkwato.
![BUA ya raba wa asibitoci magunguna a Sakkwato BUA ya raba wa asibitoci magunguna a Sakkwato](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/IMG-20250211-WA0038.jpg)
Kamfanin Siminti na BUA ya raba magungunan cututtuka daban-daban na kimanin naira miliyan 35 a ƙananan asibitoci da ɗakin shan magani 16 da ke cikin Ƙaramar Hukumar Wamakko a Sakkwato.
Yayin da yake rabon magungunan, Daraktan Kamfanin BUA, Injiniya Yusuf Halliru Binji, ya ce suna raba tallafin a asibitoci da ɗakunan shan magani 16 a tsarin da yake da shi na sadaukarwa ga al’ummar da suke kusa da shi, inda a kowace shekara akan bayar da magungunan don saukaka wa jama’ar.
- Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya suya sheka daga PDP zuwa APC
- An kama ’yan ina-da-kisa 47 a Kwalejin Tarayya a Kebbi
Binji ta hannun Alhaji Sada Suleiman da ya wakilce shi ya ce kamfanin BUA a tsarinsa na rama alheri ya ɗauki wannan da muhimmanci domin ƙarfafa dangantaka.
“Babu tantama dole mu bayyana farin ciki ga irin goyon baya da haɗin kai da muke samu ga jama’a tsawon lokaci.
“Nasarar da kamfanin yake samu tana da alaƙa da haɗin kan jama’ar da ake makwabtaka da su. Saboda haka za mu ci gaba da kula da bunƙasa rayuwar jama’a
“Nan gaba kaɗan za mu ƙaddamar da rijiyoyin burtsatse guda 7 masu amfani da hasken rana a faɗin Sakkwato, bayan raba tufafin makarantar firamari biyar da za a yi ga mutanen yankin.
Daraktan ya gargaɗi waɗanda suka samu tallafin a kan kar su sayar da magungunan domin kyauta ne ga kowa.
Ya ce kamfanin zai haɗa kai da gwamnati don tabbatar da waɗanda aka yi don su sun amfana.
Wasu daga cikin asibitocin da aka yi rabon magungunan sun haɗa da Asibitin garin Bakin Kudu da Gidan Bailu da Kalambaina da Sabon Garin Alu da Gidan Boka da Asare da Arkilla da Guiwa da sauransu.