Buba da Ilu
Buba da Ilu Hadejawa ne abokan juna, sai dai Buba ya mallaki godiya. Kullum kwanan duniya in suka hadu sai Ilu ya tambayi Buba: “Ina godiya?” Shi kuma Buba kullum sai ya ce: “Godiya lafiya lau.” Rannan suka hadu, sai Ilu ya tambayi Buba: “Ina godiya?” Buba ya ce: “Yau dai godiya ta yi abin […]
Buba da Ilu Hadejawa ne abokan juna, sai dai Buba ya mallaki godiya. Kullum kwanan duniya in suka hadu sai Ilu ya tambayi Buba: “Ina godiya?” Shi kuma Buba kullum sai ya ce: “Godiya lafiya lau.” Rannan suka hadu, sai Ilu ya tambayi Buba: “Ina godiya?” Buba ya ce: “Yau dai godiya ta yi abin da kake so.” Sai Ilu ya ce: “Ta mutu?” Buba ya ce: “A’a, ta dai haihu.”
Daga Amiru Isa Bakori, 07068147933