Budaddiyar wasika ga amare

Gaisuwa mai tarin yawa tare da fatar kuna cikin koshin lafiya. Yaya aka ji da dawainiyar biki mai alfarma da dimbin tarihi a cikin zukatanmu da kuma na masoyanmu?Ya ku amare masu dimbin farin jini da tarin albarka, na san za ku yi mamakin ganin wannan takarda a daidai wannan lokaci, to ba komai ba […]

Budaddiyar wasika ga amare
Budaddiyar wasika ga amare

Gaisuwa mai tarin yawa tare da fatar kuna cikin koshin lafiya. Yaya aka ji da dawainiyar biki mai alfarma da dimbin tarihi a cikin zukatanmu da kuma na masoyanmu?
Ya ku amare masu dimbin farin jini da tarin albarka, na san za ku yi mamakin ganin wannan takarda a daidai wannan lokaci, to ba komai ba ne, illa ina so in yi amfani da wannan damar domin kara tunatar da ku abin da kuka sani.
Ku sani, angonku bai nemi aurenku ba har sai da ya tabbatar za ku yi biyayyar aure daidai gwargwado, duk da ban manta da tsabar kyawun halittar da Allah Ya yi muku ba; ban kuma manta nasaba da arzikin da wadansu suke da shi ba, sai dai, ba su ne gabana ba idan aka kwatanta da babban makasudin da ya sa aka aure ku.
Idan za ku iya tunawa auren Ladidi da Illo, ya samu cikas ne sanadiyar son rai ba tare da yin abin shari’a ta tanadar ba. Ya auri Ladidi ne saboda wasu ababuwa daban, wadanda a lokacin da Manzon Rahama ke ba da shawara, bai dauki shawarar ba, sai ya bi kyalykali da wata maslahar  ta daban.
Don haka na rubuto wannan takardar ne saboda mahimmancin da kuke da shi a wurina, a cikin takardar zan sanar da ku abubuwan da ya kamata ku yi yanzu da kuka zama amare, inda kiyaye su ne za su kara ba mijinku damar sauke hakkokin da Allah Ya dora masa.
Na farko dai, ku kara kaimi wajen bautar Allah da kuma yin da’a ga ma’aikinsa Annabi Muhammad (SAW). Abu na biyu kuma, ku mutunta mijinku tare da daukacin ‘yan uwansa, musamman ma mahaifiyarsa. Idan kun yi wannan, lallai kun gama komai.  
Kada ku rika kai ruwa rana da mijinku a kan abin da ya shafi ibadar Allah. Ku rika tsayar da Sallah, sannan ku lazimci karatun Alkur’ani mai girma.
Ku rika hakuri da mahaifiyar mijinku, ina fata mijinku ma zai tattauna da mahaifiyarsa don ta rika yi muku uzuri, ta kuma yafe muku idan kun yi mata laifi.
Idan kuka yi haka ina da yakinin mijinku zai iya yi muku alkawarin samun duk abin da kuke so wurinsa ba tare da bata lokaci ba, in dai bai fi karfinsa ko ya saba wa shari’a ba. To idan bai yi muku ba wa zai yi wa? Ku din nan fa, ku ne Allah Ya dora nauyinku a kansa. Kuma wajibin kowane Musulmi ne sauke nauyin da Allah Ya dora masa.
Ya ku amare, ku kasance kusa da mijinku a duk lokacin da yake bukatar hakan, ku share hawayensa; ku haskaka zuciyarsa. Kada ku bari wani abu ya cutar da shi, ma damar kuna da iko a kan hakan. Ku kare mutuncinsa da martabarsa.   
Ina fata za ku gargadi kawayenku, sannan ku bukaci su yi amfani da dukkan abin da ambata a wannan wasikar idan lokacin aurensu ya zo.
Ku huta lafiya.
Nasir Abbas Babi ya rubuto daga Jihar Sakkwato.
Za a iya samunsa a wadannan lambobin: 08033186727 da 080095653401