Budaddiyar wasika ga Gwamna Ganduje

Ina fatan Editan Aminiya zai bani dama in mika koken manoman da aka cinye musu gonakin gado ga Gwamna mai adalci Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ta yadda idan ya sanya aka bincika gaskiyar lamarin zai yi kokarin bin Kadin hakkinmu. Kuma muna fatan Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu zai yi mana kokari […]

Budaddiyar wasika ga Gwamna Ganduje

Ina fatan Editan Aminiya zai bani dama in mika koken manoman da aka cinye musu gonakin gado ga Gwamna mai adalci Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ta yadda idan ya sanya aka bincika gaskiyar lamarin zai yi kokarin bin Kadin hakkinmu. Kuma muna fatan Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu zai yi mana kokari kamar yadda magabtansa suka yi, har Allah Ya sanya a bai wa mai hakki hakkinsa.

Tauye hakkin manoma ta hanyar kwace musu gonakinsu na gado, iyaye da kakanni ba karmin koma baya ba ne ga kasa, musamman adaidai wannan lokaci da manufar Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta himmatu wajen bunkasa tattalin arziki ta hanyar noma. Manomin duk daya samu kansa a irin wannan yanayi ko dai yaci gaba da noman a wani wuri ko kuma daga nan shike nan. Irin wannan ta sanya da aka kibiyanmu diyya agonakin gwaji na tsohon Gwmanan Kano, marigayi Kwamishinan ’yan sanda Audu Bako, wasunmu suka yi watsi da aikin gona, amma mu muna kokarin ganin an mayar mana gonakinmu,tunda mutum 17 kawai aka biya diyya daga cikin mjtum 131.

Da aka yi wa Janar Yakubu Gawon juyin mulki sai akadiana biyan diyyar wadannan gonaki, musamman namu da suke a yankin Tiga. Kuma mun bi duk daukacin hukumomin da abin ya shafa, amma lamarin ya ci tura. Kai akwai lokacin da muka tafi fadar Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, harya yi umarni aka rantsar da mu. Kuma dagacikin wadanda suka karbi wannan rantsuwa har yanzu suna nan. Wannan matsala tamu da ta ki ci, ta ki cinyewa shekara da shekaru tana barin fadar Kano sai hukumomisu yi watsi da ita. Yanzu ma mun sake kai wa Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II wannan koke namu.

Mai girma Gwmana na tabbatar da cewa Allah Ne shaidarmu,amma idan aka tuntubi Hadi Sarkin Shanu da Saminu Iliyasu, wadanda sanannun mutane a gfadin Tiga, kuma da su aka yi ta kokarin kwatar hakki,har zuwa lokacin da wani Hakimi Alhji Ibrahim Cigari ya ce mana idan kun je Rano mu ne, haka idan kuka ce kunci mu ne, kai ko Kanon ma kuka je mu ne. Don haka ku daina zuwa kusa da wadannan gonaki, har sai abin da hukuma ta bayar da umarni a kai.

Kan wannan hakki namu, ba za mu je kotu mu bata lokaci ba, domin hukuma na da iko da fadin kasarta, amma dai hakki ne na masu noma wuri, musamman wadanda suka ci gado na iyaye da kakanni. Kodayake wannan ba zai hana mu gurfana a gaban Hukumar korafi ta Jihar Kano, don ganin ta bi kadin wannan lamari. Muna yi mata fatan Allah Ya bai wa Alhaji Muhyi Rimin gado idon bin hakkin duk wanda aka zalunta a fadin jiharmu, kamar yadda Gwamna Ganduje ya nada shi a wannan mukami. Muna fatan kafafen yada labarai za su yi kokarin bankado masu fama da matsala irin tamu, domin suna da yawa sai wadanda Allah Ya sa lamarinsu ya kamari.

A karshe wannan koke namumuna mika shi ga Mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin yana kudurin ganin an bunkasa harkar noma a kasar nan. Sauuau uwa-uba mai gayya, mai aiki Gwamnanmu Alhaji Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Mai Martaba Sarkinmu, Muhammadu Sanusi II. Muna fatan wadannan shugabannin al’umma za su kwatar wa mai hakihakkinsa, tunda su Allah Ya dorajan ragamar al’umma a fadin kasar nan.

Usaman Bala Muhammad ya rubuto kokensa daga Tiga 08069769629/08094849538.