Budaddiyar wasika ga Gwamnan Jihar Katsina
Tare da fatan maigirma gwamna na cigaba da kimtsa ’yan komatsansa, don barin sabon gidan Gwamnatin Jihar Katsina, gidan da aka kwashe makudan kudin al’ummar jiha aka narkar da su wajen ginawa tare da kawatashi, a daidai lokacin da a ke fama da matsalar ruwan sha da matasa masu gararamba akan tituna da majalissu, ba […]
Tare da fatan maigirma gwamna na cigaba da kimtsa ’yan komatsansa, don barin sabon gidan Gwamnatin Jihar Katsina, gidan da aka kwashe makudan kudin al’ummar jiha aka narkar da su wajen ginawa tare da kawatashi, a daidai lokacin da a ke fama da matsalar ruwan sha da matasa masu gararamba akan tituna da majalissu, ba aikin fari, balle na baki.
A daidai irin wannan lokacin al’ummar yankunan karkara ke fama da matsalolin sufuri na lalacewar hanyayoyi. Hakika misalan matsalolin da ke ciwa al’umma tuwo a kwarya na da tarin yawa! A daidai lokacin da alkalumman matan da ke rasuwa wajen haihuwa, sakamakon karancin jami’an lafiya da magani; ga shi Jihar Katsina ta ciwo lamba ta biyu a jerin jihohin da ke fama da fatara da talauci. Al’amura da dama sun yi mana dabaibayi, amma a haka gwamna ka kekashe kasa ka kauda kai daga kirayen-kirayen al’umma, ka kera wannan katafaren gida don biyar bukatar kanka, ba ta al’ummar Jihar Katsina ba. Ba gidan ba ne matsalarmu, nasan yanzu dai wajibi ne kayi bankwana da wannan gida kasa da kwanaki 100 masu zuwa!
Ya maigirma gwamna, kafin ka yi bankwana da wannan kujera da ka share shekaru takwas kana kamawa, kana karyawa yadda kakeso, zan so in san inda aka kwana akan maganar ma’aikatan nan sama da dubu uku da ka dakatar a daidai lokacin da muke kuka akan matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa. Ina matsayin wadannan bayin Allah ya maigirma gwamna? Wai ina asalin kudinmu na kananan hukumomi tsawon shekaru hudu, wanda ka bayyana wa duniya lokacin rantsar da shugabannin kananan hukumomin da ka yi a watannin baya, wanda ka bayyana akwai kimanin biliyan 36 a wannan asusu, muna bukatar karin bayani! Ina aka kwana akan karin kudin albashin malaman Firamare da aka yi a takarda, amma ba su gani a kasa ba? Kana gab da barin madafun iko! Yaushe za ka biya
fitattun ’yan kwangilar Jihar Katsina da har yanzu ba a biya su kudin wasu kwangilolin da suka yi ake yimana gori da su? Ina kudin asusun gwamnatin jiha da har ba za a biya wadannan bayin Allah hakkokinsu?
Kada in tsawaita maka da tarin tambayoyin da nake ganin amsarsu za ta yi wuyar gaske cikin kankanin lokaci, sai dai ina son maigirma gwamna, ka tuna cewa akwai ranar da za ka amsa wadannan tambayoyi da ma wasu makamantansu, ko ka shirya, ko ba ka shirya ba, wannan ita ce, ranar da ’yan kanzagi da masu fushi da fushinka ba za su amfane ka da daidai da kwayar zarra sai abin da ka shuka!
Kamar yadda ya zame maka wajibi barin wannan katafaren gida, haka wajibi ne barin wannan duniya da muke cikinta mai cike da rudani, tamkar yadda ka amshi ragamar a hannun wani , wanda ya koma ga Allah, to ka tuna kai da ni duka za mu amsa kira. Yanzu dai mun ga naka salon mulkin, da yadda ka rika keta yancin bil’adama da sunan siyasa! Mun ji yadda ka mayar da mu kyankyasai, don kawai mun saba maka ta fuskar jam’iyyar siyasa! Uwa uba mun ji yadda ka rika yi wa ayoyin Alkur’ani shishshigi da sunan tallata dan takararka! Sai yaushe za ka fito ka nemi afuwar ’yan adawa akan wannan cin mutunci? Yaushe za ka fito ka shelanta tubarka tun a duniya ko don ka kubuta daga laifin fassara ayoyi da son rai? Shawara dai ta rage wa mai shiga rijiya!
Kwamared Sagir Musbahu Daura Dole daga kungiyar Muryar Talaka, Jihar Katsina 08095597525.