Budaddiyar wasika ga mai martaba Sarkin Musulmi

A wannan makon, mun samu sako ne daga Malama A’ishatu Usaman Liman [email protected] a wasikar musamman da ta aika wa mai martaba Sarkin Musulmi. Ga sakon nata:  Ya Amirul Mu’uminina (Mai Alfarma Sarkin Musulmi), sunana Aishat Usman Liman, ni talakace daga cikin talakawanka, amma ina neman izini a wurinka da in gabatar da wata ’yar […]

Budaddiyar wasika ga mai martaba Sarkin Musulmi

Budaddiyar wasika ga mai martaba Sarkin MusulmiA wannan makon, mun samu sako ne daga Malama A’ishatu Usaman Liman [email protected] a wasikar musamman da ta aika wa mai martaba Sarkin Musulmi. Ga sakon nata: 

Ya Amirul Mu’uminina (Mai Alfarma Sarkin Musulmi), sunana Aishat Usman Liman, ni talakace daga cikin talakawanka, amma ina neman izini a wurinka da in gabatar da wata ’yar shawarata a gare ku game da halin da yankinmu na Arewacin Najeriya yake ciki a yanzu.
Kamar yadda kuka riga kuka sani, yanzu Arewa tana cikin wani irin hali na rashin tsaro da tattalin arziki, wanda ya yi musabbabin jefa ta cikin mugun talauci da kunci da tsadar rayuwa da dai sauran matsaloli da ke karuwa a kullum.
To, shi ne nake ganin Ya Amirul Mu’uminina, a matsayink ka na uban kasa, uban al’umma, gatan addini, a har kullum ku ne kuke da hanyoyi na magance matsalolin da suka addabi al’ummarku, addininku, kasashenku, kai har ma da kasashen makwabtanku; domin kuwa ku aka samu da kayanku (kasarku, addininku, al’ummarku, zamantakewarku, al’adunku, dabi’unku da tarbiyyarku).
To, shi ne nake ganin kullum idan wata matsala ta taso a tsakanin al’umma, lallai a wurinku za a samu maganinta, domin ku kadai kuke da ma’aunin auna ta da kuma rariyar tace ta da kuma kofar samun mafita daga gare ta.
Kodayake a gaskiya lokaci ya zo da wani irin canji, wanda ya samo asali a sanadiyar zuwan Turawan mulkin mallaka amma muna sane da irin rawar da manyanmu (sarakuna) na wancan lokacin suka taka, na ganin sun hana Turawa karbar martabar masarautunmu, al’adunmu, addininmu da kuma dabi’unmu (Allah Ya saka masu da alheri, amin). Amma sai suka canza sabon salo (Turawan) da yin wasu shuwagabanni a tare da ku wadanda kamar wakilai ne a gare su. Amma a kullum wadannan wakilan nasu talakawa ne a gare ku kuma dukkansu sun san ku iyaye ne a gare su kuma sun san cewa da bazarku suke taka rawa kuma ba wanda zai iya zama abin da ya zama ba tare da albarkarku a gare shi ba.
Ya mai martaba, shi ne nake ganin lokaci ya yi da za ku yi babbar tsawa da mashahurin jan kunne ga wadannan ’ya’yan naku (shugabannin Arewa), domin kuwa sun fara wuce makadi da rawa da kuma rikon sakainar kashi wa ’yan yankin da kama karya da a-fasa-kowa-ya-rasa ga al’amuransu na tafiyar da mulkin Arewa, wanda a sanadiyyar haka ya janyo wadannan matsaloli da yankin ke fuskanta, na rashin tsaro da rikice-rikicen addini da na kabilanci da uwa-uba tabarbarewar tattalin arzikin yankin,da rashin aikin yi; wanda har ake wa yankin lakabi da ‘cima-zaune’ ga kuma barazanar turbar rushewar da take ciki.
Ya mai martaba, ina ganin ba zai cancanta a yi zugum, a tsura masu ido cikin wannan turbar da suka kama, wadda ba mafita kuma ba gaskiya a cikinta, alhali ’yan uwa talakawa suna cikin mummunan halin matsin rayuwa kuma su ma talakawanku ne, masu son ku, masu biyayya a gare ku. Kodayake ba wai mun ce ba a tsawata masu ba ne samsam. A’a, ana yi amma yanzu ya kamata a yi masu kashedi da a kul, cikin babbar murya tare da gintaya masu wasu sharudda da dokoki da razana su tare da nuna masu an haife su, su ma fa suna da shugabanni; ba su ne shugabannin kansu ba, domin kuwa ko ya kunne ya bunkasa ba zai wuce kai ba.
Ya shugabana kuma ubana, na san idan wannan takardar tawa ta shiga hannunku kuma wannan koken nawa ya isa gabanku, ina fatan in Allah Ya so, kuna da dubban matakan da za ku iya dauka a game da wadannan talakawan naku (shugabannin Arewa), kai harma da mu na kasa da su, domin dawo da Arewa a kan turbar gaskiya da martabarta da aka santa da su.
To amma duk da haka ya ubana, don Allah a yi mani izini in dan furta wata ’yar karamar shawarata a gare ku, ba don na isa ba sai dan ina ganin kamar wata gudumawa ce a gare ku, a matsayina na diya a gare ku kuma mai fatan ci gaban Arewa. Shawarar tawa ita ce kamar haka:
1-Ni a nawa ganin ya babana, za ka iya kiran taron manyan sarakunan Arewa, ku taru ku tattauna a kan matsalolin da yankin yake ciki na rashin tsaro da fadace-fadacen addini da na kabilanci da kuma tarkon karayar tattalin arzikin da ya kama yankin da warware wasu ’yan matsaloli da kuke ganin ku ma sun sha gabanku.
2-A cikin wannan taron ne nake ganin za ku iya yanke shawarar kiran shugabannin addinin nan guda biyu, Musulunci da Kiristanci na Arewa da su zo su zauna a gabanku, kowanne ya fayyace maku matsalar da ta addabe shi (a cikin addinin da kuma mabiyansa), sannan da matsalar da ke damunsa da makwabcinsa (daya addinin da ba nasa ba) da kuma hanyar magance matsalar.
3-Daga nan sai ku kira taron gwamnonin Arewa su ma su zo su fayyace matsalolin da ke addabar jihohinsu da kuma tasu shawarar yadda suke ganin za a magance wadannan matsalolin da yankin yake ciki.
4-Daga nan sai ku kira ’yan-majalisu na Tarayya da na dattijai, masu wakiltar yankin Arewa. Tare da tambayar su shawara a kan yadda za a yi a ceto Arewa daga wannan kangi da take ciki.
5-Sa’annan sai ku yi zama na musamman tare da kungiyar dattawan Arewa da ta samarin Arewa da wakilan wadancan shugabannin (na addinai da na gwamnoni) da kuka yi zama da su daga farko, domin tattaunawa ta musanman; tun da kun samu bakin zaren warware wadannan matsalolin tare da fitar da tsare-tsaren mafita ta musamman mai inganci, tabbatacciya kuma ta gaggawa ga wannan yanki na Arewa da bai san inda ya sa wa gaba ba sai Allah.
Amma na san watakila za ku yi zaton muna nufin taron kasa ne, a’a, ni dai ina nufin ‘Taron Majalisar Sarakunan Arewa Don Ceto Yankin Daga Halin Durkushewa.’
Ya shugabana, lallai ina ganin wannan taron ba karamin tasiri zai yi ba a wajen dawo da martaba da so da kauna da ke tsakanin ’yan Arewa kuma zai jaddada hadin kai da kawar da tunanin kowa-tashi-ta-fisshe-shi da ke zukatan ’yan Arewa a yanzu kuma zai farkar da manya da kananan ’yan yankin da tunanin suna cewa sun girma, sun fi karfin manyansu.
Ya mai martaba, muna sane da cewa sau da yawa kukan so ku yi irin wannan taro na fadakarwa amma sau da yawa kukan samu ’yan matsaloli wadanda suke hana tabbatuwar hakan amma in Allah Ya yarda yanzu kuna cikin addu’o’in talakawanku na neman mafita, insha Allahu. Allah zai muku gajora, domin ku sama mana mafita da muke nema ruwa a jallo kuma muna da yakinin cewa ku kadai muke da su wadanda za mu iya kai wa kokenmu kuma ku share mana hawayenmu, domin ku ne iyayenmu, shugabanninmu na kusa da mu kuma ku ne masu gani da lura da halayyar da muke ciki a kullum.
Ya Allah Ya ba ku iko da kwarin gwiwar ceto mu da yankin Arewa daga wannan hali da muke ciki. Amin.
Na gode, Allah Ya kara wa mai Martaba Sarkin Musulmi, uban kowa lafiya da basira da hikima da tausayi. Amin!

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50 a Kaduna

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54