Budaddiyar wasika ga manyan Arewa
Ina mai matukar fari cikin da samun damar rubuta wannan wasikar ga manyan Arewa game da wani abu mai muhimmaci.Kamata ya yi da manyan Arewa, kamar tsofaffin shugabannin kasa Ibrahim Babangida, Shehu Shagari da kuma Abdulsalami Abubakar da su hada kansu wuri guda su mara wa tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari waje neman shugabancin […]
Ina mai matukar fari cikin da samun damar rubuta wannan wasikar ga manyan Arewa game da wani abu mai muhimmaci.
Kamata ya yi da manyan Arewa, kamar tsofaffin shugabannin kasa Ibrahim Babangida, Shehu Shagari da kuma Abdulsalami Abubakar da su hada kansu wuri guda su mara wa tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari waje neman shugabancin kasar nan a zabe mai zuwa na badi.
Kuma ina rokon sarakuna kamar mai matarba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da Sarkin Musulmi da sauran sarakuna na yankin Arewacin kasar nan da su yi wa talakawan taimako waje ganin Janar Muhammadu Buhari ya haye bisa kujeran mulkin Najeriya, don fitar da kasar nan daga kangin da ya dabaibaye kasar da kuma sama wa talakawan kasar mafita.
Don Allah ina rokon wadannan manyan Arewa da sarakuna da su dubi girma Allah su dubi wahalar da kasar nan ke ciki, musamman yankin Arewa inda rayuka ke ta salwanta, musamman a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.
Janar Muhammadu Buhari dai a sanin kowa, mutum ne mai adalci, mai kaunar talaka. Kuma a halin da kasar nan ke ciki, shi ne kadai wanda zai fitar da kasar da al’ummarta daga wahalolin da suka addabe ta.
Yanzu dai ba wai Arewa ce ke neman canji ba, har da kasar baki daya. Kuma idan ya samu mulkin zai tsaya sosai waje inngata rayuwar talakan kasar gaba daya.
Yana da manufofi masu kyau don ingata rayuwar talaka, don haka ya kamata a wannan lokacin manyan Arewa da sarakunanta su fito su goya wa Janar Muhammdu Buhari baya don ganin ya samu mulkin kasar nan a badi.
Janar zai ingata harkar noma don Najeriya na da albarkatun noma sosai kuma a matsayinsa na tsohon soja, zai ingata harkar tsaron kasa na sosai don a samu lafiya da walwala mai inganci. Harkar kasuwanci za ta bunkasa sosai, idan ya zama Shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Don Allah manyan Arewa da sarakunan kasar nan ku ba Janar Muhammadu Buhari goyon baya, ya samu ya hau karagar mulkin Najeriya.
Alhaji Ismaila, lamba 20, Kasuwar Shopping, Jimeta-Yola, Jihar Adamawa