Budaddiyar wasika ga sabbin ‘yan Majalisar Tarayya
A gaskiyar magana ya kamata a wannan sabuwar majalisar karo ta 9, ta fito da wani tsari yadda kowane dan Majalisar Dattawa da ta wakilai da ma ’yan majalisar jihohi, su yi wani tsari yadda kowane wakili zai iya saduwa da al’ummar mazabarsa kai tsaye, domin tattaunawa a kan abin da ya kamata ya mika majalisa […]
A gaskiyar magana ya kamata a wannan sabuwar majalisar karo ta 9, ta fito da wani tsari yadda kowane dan Majalisar Dattawa da ta wakilai da ma ’yan majalisar jihohi, su yi wani tsari yadda kowane wakili zai iya saduwa da al’ummar mazabarsa kai tsaye, domin tattaunawa a kan abin da ya kamata ya mika majalisa a matsayin ra’ayin alummar mazabarsa.
Kuma lallai kudin nan da ake cewa na aikin mazabu, da ake ba ‘yan majalisa wanda miliyoyi ake magana, ya zama akalla ana kashe kaso biyu a cikin uku na wannan kudade a cikin al’ummar wannan mazaba, hakika hakan zai magance ko rage matsalolin ilmi da talauci da harkokin lafiya a kasarnan baki daya, domin ko ina zai jike da ayyukan alkairi kuma alumma zasu gamsu lallai akwai wani abu da ake kira roman demokradiyya, domin ’yan majalisar dattijai kadai ana bawa kowanne dan majalisa sama da miliyan 13 a matsayin kudin inganta mazabu, banda alawus da albashi. Haka dan majalisar wakilai ko wanne ana bashi sama da miliyan 10 su kuma ’yan majalisar jihohi na karbar miliyan 7 dukkan ninsu a kowanne watan duniya haka ake basu.
Kuma wani abin takaici inba ai hankali ba wannan majalisar karo ta 9 lallai in ba’ai da gaske ba, zata fita baya lalacewa, domin yanzu ga rigimar shugabanci a majalisa, wanda sabbi da sukaje har anfara basu toshiyar baki na kusan naira miliyan biyar, domin su yadda da shugabancin wani, kaga wannan zaisa afara koya musu sanin mahimmancin karbar na goro, in sunyi Magana ko sunki yarda ace to shikenan sai dai su zama ’yan kallo, baza a rikayi da suba, lallai shugaban kasa yasan hanyoyin da zaibi domin yakar wannan bakar al’ada a majalisun kasarnan.
Kuma ya kamata lallai asan yadda za’ayi a gyara kundin tsarin mulkin kasarnan ya zama duk wani zababbe kada ya huce zango 1, ma’ana ya zama da kayi shekara biyar to kauce ka bawa wasu dama, koda shugaban Kasa da gwamnoni da ’yan majalisa kaga wannan zai rage hadamar neman mulki da wasu ’yan tsirari ke hana wasu a dama dasu, kuma wannan zai rage siyasar kudi da siyasar uban gida, zai rage rikicin siyasa da banga, kuma hakan zai taimaka a samu ayyuka suna tafiya kamar yadda yakamata, domin kowa zai yi kokari yayi abin kirki kafin lokacinsa ya kare ba tare da barin kwantan aiki ba.
Kuma gaskiya al’umma sun gaji da tsarin mulkinnan na Amurka, mutane yanzu sunfi son akoma tsarin mulki irin na da na kasar Ingila, shine tsari da yake dai-dai da al’adun mutane, kuma akwai tattalin dukiyar kasa batare da al’mabazzaranci ba, munasa ran wannan majalisa ta 9 zata jajirce domin dawo da wancan tsarin da aka fara dashi tun farkon dawo da mulki kasarnan, babu laifi ayi masa tsari yadda zai biya bukatun ’yan kasa, amma lallai majalisa ta zama ana zamane na wucin gadi kamar da. Hakan zai taimaka talakawa su zama suna saduwa da wakilansu ba tare da wasan buya ba.
Hakanan wannan karan munasa ran majalisa ta 9 zata fito da tsarin aiki da dokoki kamar yadda ya kamata kuma dokoki masu tsauri tare da nuna ba sani ba sabo, wannan shine zai magance matsalar cin hanci da rashawa da zalunci ko daurewa karya gindi a kasarnan, kuma ya zama dole ayi wani gyaran fuska a bangaren shari’a da bangaren tsaro yadda kwalliya zata rika biyan kudin sabulu.
Haka nan dai muna sa ran a wannan majalisa ta 9 zatai kokari ta dawowa kananan hukumomi mar tabarsu a rika basu kudadansu kai tsaye mai makon yanzu da gwamnonin jihohi sukeyi musu karfa karfa, wannan zai taimakawa al’umma na can kasa susan ana demokradiyya ta hanyar samar da ayyukan yau da kullum kuma ana daukar masu aikin yi dama bunkasa ababan more rayuwa a tsakanin alumma musamman a kar-kara ,amma ya zama anasa ido sosai.
Sannan lallai shugaban kasa yayi kokari ya zabo abokan aiki jajirtattu banda la’akari da abokantaka ko ‘yan uwantaka ko surkantaka ko takama da asali a’a cancanta da nagarta da karancin buri da kishin kasa da kwazon aiki za’a lura dasu.
Kuma wannan karan shugaban kasa da ’yan majalisa da gwamnonin jihohi su ba da mahimmanci akan tsaro da ilmi da harkar lafiya da bunkasa tattalin arziki ka’in da na’in, kada kuma a rika sakaci da jan kafa wajen abin da ya shafi bukatun alummar kasa musamman kasafin kudi da abinda ya shafi ababan more rayuwa.
Akwai wani shiri da shugaban kasa ya bijiro dashi mai taken (sauyi ya fara daga kai na) wanda gwamnonin jihohi sukai masa rikon sakainar kashi, shugaban kasa kuma baya bibiya saidai talla a kafafan yada labarai musamman talabijin, lallai wannan karan abawa wannan shiri karfi sosai domin cusa tarbiyya da kishin kasa da gaskiya a zukatan’Yan kasa.
Kuma Shugaban Kasa a wannan zangon nasa na karshe, ya dubi Arewacin kasar nan da idon basira, ya ingantata ta fuskar hadin kai da zaman lafiya da bunkasa tattalin arziki da kasuwanci da kuma inganta harkokin ilmi duk na Arewacin kasar nan,domin wadannan su ne ajandar Arewacin kasar nan, hatta man fetur an tabbatar akwai shi a jihohi uku na Arewacin kasarnan,to a wadannan shekaru hudu da suka rage wa Shugaba Buhari ya tabbatar an fara cin gajiyarsu da batun jawo ruwan nan zuwa Arewacin kasar nan,domin wankin hula yana neman ya kai dare, sannan a bai wa jihohi da ma su samar da wutar lantarki kari akan wacce ake samu daga gwamnatin tarayya ta zama a araha,kuma ya kamata mu tambayi kawunanmu,wanne dalili ne ga arewa taja ragamar kasarnan karo na 9 amma har yanzu Arewacin kasar nan na fama da talauci da jahilci da tashe-tashen hankula da rashin hadin kai? lallai a wannan karon anabin shugaban kasa da duk wani dan siyasa zababbe na Arewacin kasar nan da sarakunan gargajiya da ’yan boko da masu fada a ji da malaman addinai bashi, ya zama kalubale, kodai azo a samarwa da Arewacin kasa rnan mafita ko mulki in ya koma Kudanci haka za a zuba wa Arewacin kasar nan ido suna ta kashe kawunansu a banza ayita samar da karin almajirai da sauran muggan laifuka, wanda lallai dole a rika haskawa shugabanni da masu ruwa da tsaki a arewacin kasarnan hanyoyin da za a bi a bunkasa arziki da zaman lafiya da dawo da harkar zamantakewa mai inganci, dole shirin ya tabo al’amuran shugabannin siyasa da sarakunan gargajiya da ’yan boko da masu hali da malaman addinai da masu fada aji yadda za’a gudu tare a tsira tare ko Arewacin kasar za ta dawo da martabar da aka santa da ita ta fuskar hadin kai da zaman lafiya da karuwar arziki da ilmi da tarbiyya. Sauran talakawa kuma suma wace irin gudun mawa zasu iya bayarwa a wannan sabuwar tafiya ta inganta arewacin kasarnan? A kasance da batutuwa irin wannan domin samarwa da arewacin kasarnan mafita a wannan karon na shekaru hudu na karshe na shugaba muhammadu buhari kuma zangon karshe na arewacin kasar nan , kudu kuma ta dauka, fata dai Allah ya kiyaye a samu mulkin a samu kudi da adaukaka amma gidanka da unguwarku ko garinku ya gagareka zuwa.
A karshe wannan yarinya Zainab Habibu Kila, da azal yaso ya fadowa Allah Ya ceto rayuwarta, kuma wannan ya nuna a fili al’umma ya kamata duk abu daya faru na zalunci a ciki da wajen Kasarnan a fito ayi zanga-zanga ta lumana kamar yadda wasu matasa suka fara akan wannan abu, nan da nan gwamnatin taryya tai kokari har aka sakko wannan yarinyar daga kasar saudiyya, saboda mutane kada su rika dangana ko ake shikenan akwai Allah (hakika akwai Allah) amma yin irin wannan gwagwarmaya zai taimaka hukumomi su dauki abu da mahimmanci, duk da dai dama shugaban kasa tuni ya ba da damar ayi bincike. Su kuma irin wannan azzalumai da sukewa matafiya cushe lallai ayi bincike watakila sunanan da yawa kuma wata kila sunanan da mutanensu a can kasar saudiyya dama wasu kasashen masu taimaka masu. Matafiya su kuma su kara lura da masu yimusu dakon jaka zuwa cikin jirgi.
Ka ga kasar Sudan da tai wannan zanga-zanga ta gwagwarmaya akan kara kudin biredi kawai sai gashi ta samu babbar mafita har akai awan gaba da shugaban kasar wanda ya zama sai tarihi, amma anan sai anyi a hankali da lura kada ayi kitso da kwarkwata.
Abdullahi Idris Yakasai
08054407095