Budaddiyar wasika ga sabon Shugaban kasa da sababbin Gwamnonin APC

Da farko ina taya ku murna bisa hukuncin Allah da ya sa jama`ar kasa suka amince maku suka zabe ku, har kuka kai ga gagarumar nasarorin da kuka samu a cikin zabubbukan kasa da aka gudanar a ranakun 28 ga watan Maris da ya gabata da kuma 11 ga wannan watan na Afrilu.Nasarar da ta […]

Budaddiyar wasika ga sabon Shugaban kasa da sababbin Gwamnonin APC
Budaddiyar wasika ga sabon Shugaban kasa da sababbin Gwamnonin APC

Da farko ina taya ku murna bisa hukuncin Allah da ya sa jama`ar kasa suka amince maku suka zabe ku, har kuka kai ga gagarumar nasarorin da kuka samu a cikin zabubbukan kasa da aka gudanar a ranakun 28 ga watan Maris da ya gabata da kuma 11 ga wannan watan na Afrilu.Nasarar da ta bai wa abokan hamayarku na jam`iyyar PDP da akasarin `yan kasa da ma na kasashen waje mamaki a kan ta zo bagatatan a inuwar sabuwar jam`iyyarku ta APC, idan aka yi la`akari da irin karfin ikon kasancewa kan karagar mulki da daularsa da sauran dama da babbar jam`iyyar PDP da ke mulkin kasar nan yau kusan shekaru 16, tun bayan da aka dawo mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, ta ke da su amma kuka yi mata kayin da za ta dade ba ta mike ba.

Wannan nasara, ita ta kawo yanzu jam`iyyarku, bayan tana da Gwamnonin jihohi sama da ashirin (cikin ana jiran karkare zabubbukan Gwamnonin jihohin Taraba da Imo da Abia), da akasarin gagarumin rinjaye a Majalisun Dokokin jihohin (musamman irin na su Kano da Katsina da Sakkwato da Jigawa da makamantansu), inda jam`iyyarku ita za ta yi kidanta ta yi rawarta. Haka labarin yake, jam`iyyarku it ace take da mafi rinjayen `yan Majalisar Dattawa da Sanatoci sama da 60, koda yake tana bukatar karin Sanatoci 12, kafin a ce za ta iya yin kidantata ta kuma yi rawarta yadda take bukata cikin tafiyar da harkokin a Majalisar. A can zauren Majalisar Wakilai ta tarayya kuwa jam`iyyarku tana da Wakilai 209, wanda zai ba ku rinjayen a je a karasa, baya ga tashi da ta yi da kujerar uban gayya, wato lashe kujerar shugabancin kasa. Kun kuma sani cewa wannan shi ne karon farko a cikin tarihin mulkin dimokuradiyyar kasar nan na shekaru 16 jam`iyyar PDP ta fadi kasa warwas.
Dukkan wannan nasara da ku ka samu kun san cewa daga Allah take kamar yadda na fadi tun farkon bude wannan makala,kuma kamar yaddaAllah ya tabbatar cewa “Shi yake da mulki, shi kuma yake bayar da shi ga wanda ya so a lokacin da ya so”, haka ma batun karbe shi yake a gare shi. Kun dai ji yanzu irin cece-kucen da ake yi a cikin kasa cewa wai shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya nemi mukarrabansa irin su Ministoci da masu ba shi shawara na musamman da `yan kwamitin yakin neman zabensa, lallai su dawo da makudan kudaden da ya ba su su raba wa masu kada kuri`u cikin wancan zabe, tun da dai yanzu ta tabbata ba su zabe shi ba. Kudaden da ake zargin sun kai tiriliyan biyu, kwatankwacin rabin kasafin kudin gwamnatin tarayya na bana. Zargin da shugaban kasar ya karyata a kan ya kashe wadancan makudan kudade, bare kuma a yi batun ya ce a dawo da su. Koda yake ku ma din kun kashe irin abin da kuka iya kashewa. A takaice abin da nake son cewa a nan shi ne, kusan dai ba kudi ya sa kuka zo kan karagar mulki ba. Allah cikin ikonsa ne ya sa kuka shiga inuwar sabon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari, guguwar ta kada da ku.
Ku sani cewa a wasu jihohin da za ku karbi mulki nan da kwanaki 35, in Allah ya kai mu, Gwamnoninsu suna ta yin dagawa da alfaharin ba wani tasiri da za ku yi, bare ma ku karbi mulki daga hannunsu. Saboda giyar mulkin da ta rika rudinsu,amma sai ga shi da aka kada kuri`a ,kun yi masu nisa. Wannan kadai ya isa ku sani cewa Allah ne ya zabe ku ya ba ku wannan mulki, amma ba wai don karfinku ko kudadenku ko hikimarku ba, sai don kuma ya jarraba ku, ya ga ko kuma za ku butulce wa na`imarsa kamar yadda wadanda za ku gada suka yi, ya kuma nuna masu iyakarsu.
Dukkanku kun san irin mawuyacin halin da kasar nan da mutanenta suke ciki, na sukurkucewar matakan tsaro da rashin ayyukan yi da fatara da talauci da uwa-uba cin hanci da rashawa da suka yi katutu, musamman cikin tafiyar da ayyukan gwamnatoci.Akwai kuma matsaloli irin na tabarbarewar ilimi, samar da ruwan sha, inganta ayyukan kiwon lafiya da makamantan matsalolin rayuwa. Kuma a kan irin wadannan matsalolin kuka yi yakin neman zabenku, don haka akwai bukatar tun ba ku hau kan karagar mulki ba, ku san abin da ya kawo ku mulki, shi ne irin yadda za ku kyautata rayuwar al`umominku, ba tare da bambancin siyasa ba. Na san kun fi ni sanin mawuyacin halin da al`ummar kasar nan suke ciki, don haka ku kara kwana da sanin akwai aiki jajawur da yake bukatar ku tashi tsaye wurjanjan, ku yi kamar kuna yi, amma ba ku fara tunanin za ku mike kafa ku ji dadi ba.
Sanya haka a cikin zukatanku tun yanzu da kuma addu`ar Allah ya yi maku jagora da mutane suka ci gaba da yi maku zai maku jagora cikin fara tunanin zakulo mutanen kirki da za su taimaka maku ku sauke wannan babban nauyi. Duk da yake wasu suna cewa wai siyasa “Kasuwar bukata ce,” kar ku bari wannan rudin ya shiga cikin kunnuwanku, don muddin haka ta faru, to, kuwa ba za ku iya zakulo mutanen kirki ba, idanuwanku za su rufe a kan sai dan jam`iyyarku ko a `yan jam`iyyar sai ku ce sai wanda ya ba ku gudummuwa mai tsoka, kome rashin kirkinsa.Idan kuka fara da haka, to, kuwa kun fara saka da mugun zare ke nan. Allah ya kiyaye.
Duk da yake da zarar an rantsar da ku kamar yadda shugaba Jonathan mai barin gado ya ce, yanzu zai fita daga kejin da yake tsare yau shekaru 16, da suka gabata, kuma za ku samu kan ku cikin irin wancan keji daga jami`an tsaro. Ina fata za ku yi iyakacin kokarinku wajen samun hanyoyin saduwa da wadanda kuke tare kafin ku zo kan wannan kujera, ba su tsinke ba, don ko ba komai akwai `yan shan kai da za su nemi kutsa maku ta kowace hanya, koda kuwa ta kauce hanya ne don kawai su samu kanku, lalle ku ci gaba da neman tsari daga irin wadannan miyagun mutane. Kazalika, ku yi kokarin samar da kafofin da za ku rika ji daga mutane na kasa-kasa, a kan halin rayuwar da suke ciki da kokarin ganin kuna magance masu bukatunsu yadda za ku iya. Kada ku dauki girman kai ku korawa kanku, ku rika tunawa cewa wata rana za ku dawo cikin al`umma.
Duk wadannan abubuwa da na ambata da ma wadanda Allah bai sa na ambata ba, ba za su samu ba, har sai kun tafiyar da mulkinku cikin kamanta gaskiya da adalci, wanda shi ya sa har gobe ake ambato tare da yin addu`o`in alheri ga shugabannin farko da wadanda suka biyo bayansu na kasar nan. Ai yin abubuwan alherin ne ya sanya yau shekaru 30, da Janar Buhari ya bar mulki akai ta shaukin ya dawo. Ina rokon Allah (S.W.T) Ya yi maku jagora, amin suma amin.