Budaddiyar Wasika ga Shugaba Buhari

Hakika mai girma Shugaban Kasa ya halarci taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 73 har ya yi jawabi wanda ya kunshi yadda ake takura wa Musulmin kasar Myammar ya ba da shawara a kan yadda ya kamata kasashen Falasdinu da Isra’ila su ci gashin kasashensu ba wai kasar Isra’ila ta zama ita ce babbar kasa […]

Budaddiyar Wasika ga Shugaba Buhari
Budaddiyar Wasika ga Shugaba Buhari

Hakika mai girma Shugaban Kasa ya halarci taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 73 har ya yi jawabi wanda ya kunshi yadda ake takura wa Musulmin kasar Myammar ya ba da shawara a kan yadda ya kamata kasashen Falasdinu da Isra’ila su ci gashin kasashensu ba wai kasar Isra’ila ta zama ita ce babbar kasa kuma Falasdinu tana karkashinta ba. Hakan zai zamo an sare maciji ba a sare kansa ba ke nan. Duk da cewar ana ganin bai tabo matsalolin da suke damun kasashen Afirka sosai ba musamman Najeriya, amma ya yi maganar yadda za a inganta dangantaka a tsakanin Najeriya da wasu kasashe makwabta, har a ci gajiyar Tafkin Chadi wanda zai inganta harkar noma da kiwon kifi a kasar nan, har ya tabo batun nan na a dawo wa kasar nan makudan kudaden da wadansu marasa kishin kasa suka jibge a manyan kasashe, domin a inganta rayuwar ’yan kasar nan.

Wani abu da za a lura da shi, taron Majalisar Dinkin Duniya da ake gudanarwa duk shekara har ya rika gayyatar kasashe masu karfi da kasashe matalauta, wani lokacin yana kama da ihunka banza, domin tun daga aka halicci kasar nan ake wannan taro, amma har yau mafi yawan matalauta kasashe ba a samu ci gaban da ake so ba, musamman abin da ya shafi zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki, wanda samar da wadannan abubuwa guda biyu zai haifar da ilimi da abinci zai kuma kawar da tsadar rayuwa da samar da zaman lafiya a irin kasashenmu nan da nan. Amma har yanzu sai ka ga ba a magance wadannan matsaloli ba, babu dadi a ce manyan kasashen nan suna inganta kasashensu da abubuwan more rayuwa da inganta tattalin arzikin kasashensu, amma kasashen Afirka an zamar da su dandalin kashe-kashe da yake-yake da talauci da jahilci da cin hanci da rashawa da ma uwa uba tatsar da manyan kasashe ke yi wa kananan kasashe wanda har yanzu ba a daina ba, duk da ana cewa an ba su ’yancin kai, domin ko lokacin da ake mulkin mallaka ba a wahala kamar yanzu. Waje daya toshewar basirar shugabanni kasashen Afirka ta sa sun ki samar da kiwon lafiya a kasashensu, sai dai masu hali da masu mulki su tafi neman magani kasashen waje, an bar talakawa na fama da zazzabin cizon sauro da amai da gudawa da sauransu.

Ba za ka ga ’ya’yan shugabanni da iyalansu na kai kansu asibitin talakawa ba, ba za a gansu a makarantar ’ya’yan talakawa ba, sai dai su kai ’ya’yansu kasashen waje. Ta ina za a magance rashin lafiya da jahilci a kasashen? Ana ware makudan kudade, amma kafin abin ya zo ga talakan da ake yi dominsa, sai dai a bada masa kura, sai a wawushe kudin a je a biya bukatar kai sai dai ka ji shiru.

Yanzu ga kasafin 2018 babu wanda zai ce ya gani a kasa kamar yadda ake zato, kasafin 2017 kansa ba a san yaya aka yi ba, na san ana biyan albashi da wasu ’yan ayyuka nan da can, amma talaka ya gani a kasa har yanzu ana sa ido.

Wani abin takaici, duk ranar da aka ce saura wata shida zabe, to sai ka ga abubuwa sun tsaya cak mutane na ta wahala, sai dai ka ga ana kashe kudade ba bisa ka’ida ba, kuma bukatun kashe kudi a harkar siyasa sai dada karuwa suke, mutane na fama da wahala.

Lallai a nan ya kamata a yi dokar da duk wanda zai tsaya takara musamman gwamnoni su sauka a nada kantomomi a kyale su su je yi kamfen domin gudun kada ayyuka su tsaya mutane su shiga wahala.

Yanzu in ka je ofishin gwamnoni sai ka ga tarin takardu ya taru babu kulawar Gwamna, wasu na rashin lafiya ne watakila ma har lallurar ta ci, ta cinye har an mutu, wasu kuma na taimakon karatu ne watakila an kore mai nema, domin akwai wanda zai yi shekara yana ajiye ba a kula ba, to ga kuma siyasa tana kadawa kuma lallai na yarda babu tashin hankali da halin shiga tsaka mai wahala ga ’yan siyasa a irin wannan lokaci musamman ga gwamnoni, ka ga in akwai wakilin da za a sakar masa ayyuka da suka shafi rayuyar al’umma, sai abin ya zo da sauki (a lokacin Gwamna Abubarkar Rimi ya bai wa mataimakinsa rikon kwarya shi kuma ya tafi hada-hadar yakin neman zabe) ka ga ina ma a ce za a yi koyi da irin wannan tsari a kasa baki daya.

Kuma a da can haka ake yi, sannan wani abu da yake faruwa a yanzu a ce Gwamna shi ne komai a harkar kudi, domin a da kasafi ake yi a ba ma’aikatu da hukumomi kasonsu a na sa ido, amma yanzu a ce Naira dubu 50 in za ta fita sai Gwamna ya sani, to  ya za a ce ba za a shiga wahala ba? (Lallai da sake).

Shi ya sa sai su yi ta cin karensu ba babbaka saboda sun rike makoshin jama’a, kwangila ta zama sai ’yan lele, rashin taimako ya yi yawa, an bar mutane sai roko da tumasanci.

Sannan wata shawara kai-tsaye zuwa wajen Shugaban Kasa da ya kara kaimi a kan yadda ake juya akalar jihohi, musamman gwamnoni da suka ci zabe a Jam’iyyar APC, domin wadansu gwamnonin kai ka ce su ne za su sa Jam’iyyar APC ta sha kaye, saboda halin ko in kula a wasu bangarori na al’umma.

Misali abin da ake fada a Jihar Osun a ce ma’aikata wata talatin babu albashi yanzu ya yi daidai? To da za a yi bincike akwai wasu jihohin da suke da irin wannan tabon. Alhamdulillahi Jihar Kano tana ba da albashi a kan lokaci, sai dai wata ’yar walwala ta ma’aikata ta tsaya musamman don bashin nan na abubuwan hawa da ake bayarwa. Sannan yana da kyau Shugaban Kasa lallai ya sa idanu a kan yadda gwamnoni ke tafiya da al’amuran jihohinsa.

Kuma abu na biyu, wasu abubuwa ganin yadda Shugaban Kasa yake da kwarjini da kima, lalle wasu abubuwa sai yana saka baki, ba wai ya yi shiru ba. Yanzu ga maganar karin albashi da ake nema a kai ruwa-rana, wanda kowa ya san irin wahala da fargaba da tashin hankali da tsadar rayuwa da take damun ma’aikatan kasar nan, ya kamata a ce an yi karin albashin nan tun shekara 3 da suka shige, amma rabon da a yi karin albashi ana maganar shekara 10 da suka wuce, wanda kamata ya yi duk bayan shekara 3 a rika duba albashin ma’aikata in an yi la’akari da tashin farashin kayan masarufi a yanzu. Kuma irin arzikin da kasar nan take ciki, ya ci a ce duk wani ma’aikaci ya mallaki fili har ya gina gida kafin ya bar aiki a cikin shekara 30 ko 35, amma in ba ma’aikaci yana da wurin da yake cuwa-cuwa ba, a halin yanzu babu wanda ya isa albashinsa ya gina masa gida a shekara 10 har ya sayi abin hawa kafin ya bar aiki.Sai dai ya ci bashi a yi ta zuba masa kudin ruwa, rayuwar ma ta ki albarka, hakan ya jefa ma’aikata musamman kanana da matsakaita cikin zullumi. Ka ga a nan babu yadda za a magance matsalar cin hanci da rashawa, domin gafiya ta tsira da na bakinta ake yi a halin yanzu. Lallai in har ana son a magance matsalar cin hanci da rashawa, to a dubi ma’aikata da idon basira, a daidaita albashinsu daidai da yanayin kasa. Wani abin takaici sai ka ga albashin ’yan siyasa mai kauri, amma sauran ma’aikata da suka yi shekaru masu yawa suna aiki ba su samu ko kusa da irin albashin ’yan siyasa ba, ko da ko kansila ne, kuma kasuwa daya suke shiga. Saboda haka lallai Shugaban Kasa ya yi iya yi a tabbatar da inganta rayuwar ma’aikata, domin rage radadin talauci da tsadar rayuwa da rage matsalar cin hanci da rashawa.

Waje daya ina ma a ce a rage kudin man fetur zuwa Naira 90, a kuma rage kudin wutar lantarki da kashe 40, ina tabbatar da cewa kasa za ta dawo cikin hayyacinta, arziki zai shiga hannun al’umma, ’yan kasuwa za su samu ciniki, domin kowa ya san ma’aikata su ne jijiyar kasa, in sun samu, kowa zai samu. Sai a samu zaman lafiya da karuwar arziki, hakan ya jawo farashin kaya ya dan yi dama-dama saboda rage kudin man fetur da na wutar lantarki. Kuma yana da kyau a kafa hukumar kula da farashin kaya.  A ba ta karfi, ta shiga kowane sako don hukunta masu kara farashin kaya ba kai, ba gindi.

Babu dadi ace ma’aikaci ya share shekara 30 ko 35 yana aiki amma ya kasa mallakar abin da dan siyasa zai mallaka a shekara 4 koda ko kansila ne. Lallai ya kamata a duba wannan domin a samu daidaito a tsakanin albashiun ma’aikata da na ’yan siyasa.

Sannan wata muhimmiyar magana daga bakin da ba ya karya ya nuna cewa albashin  dan Majalisar Wakilai ana hada masa komai da komai a wata yana tashi da Naira miliyan 26, haka Sanata duk wata ana hada masa komai da komai yana tashi da Naira miliyan 36. Wanda albashin darakta a matakin jiha ba ya wuce Naira dubu 150 a wata haka na Babban Sakatare ba ya wuce Naira dubu 290 a wata, ya ilahi ina zancen adalci a nan? Ya kamata a rage albashin ’yan majalisa ya dawo Naira miliyan 2 a wata, ragowar kudin kuma a samar wa ’ya’yan talakawa ayyukan yi da inganta ababen more rayuwa ga sauran al’umma.

Abdullahi Idris Yakasai

GSM 08054407095

Email Add: [email protected]