Budaddiyar wasika ga Shugaba Muhammadu Buhari

Ana yin mulki ne (shugabanci) a kan tsare rayuka da lafiya da dukiya da mutunci da addini na kowanne dan kasa da mazauna cikinta har da baki masu shigi da fici (don kasuwanci, sana’a da sauransu). Idan aka samu gazawar kowane dayansu, sai mutanen kasar su gwammace suna da masaniya domin kada su dogara da […]

Budaddiyar wasika ga Shugaba Muhammadu Buhari

Ana yin mulki ne (shugabanci) a kan tsare rayuka da lafiya da dukiya da mutunci da addini na kowanne dan kasa da mazauna cikinta har da baki masu shigi da fici (don kasuwanci, sana’a da sauransu). Idan aka samu gazawar kowane dayansu, sai mutanen kasar su gwammace suna da masaniya domin kada su dogara da babu, su yi tanadin wani tsari na tsare kansu da junansu.

Allah Ya wajabta yin kotuna da alkalai da kurkuku da jami’an tsaro a karkashin shugaba adali domin su rika bibiyar zamantakewar kowane dan kasa da mazauna cikinta da masu shigi da fici domin tabbatar da zaman lafiya da walwala da mu’amala wacce babu cuta babu cutarwa. Duk wanda aka samu ya aikata kowane irin laifi, Allah Ya tanadi hukuncin da za a yi masa kowane ne, ba bambanci kamar yadda dokokin duniya ma suka tanadi haka.

Tsakanin mai mulki da wanda ake mulka, mace ko namiji, yaro ko babba, da ko bawa, mai shi da mara shi kowa na da hakki. Yanayin da muka tsinci kanmu a Najeriya tunda aka kashe su Sa Abubakar Tafawa balewa da Sa Ahmadu Bello da Akintola, aka rusa Jamhuriyya ta Farko aka tasar wa rusa kasar baki daya, ake ta kashe bayin Allah da sace dukiyar kasar abin takaici ne.

Halin da muke ciki yanzu, arzikin kasar nan tamu kacokan yana hannun tsirarin barayin shugabanni, fajirai, ’yan kungiyar asiri da suka daddasa yaransu a ko’ina, tun daga Kamfanin NNPC da Bankin CBN. Bankuna da kowace ma’aikatar gwamnati da duk kamfanoni da masana’antu masu rai nasu ne, musamman na gine-ginen hanyoyi da gidajen gwamnati da ofisoshi. Sun rusa kamfanin mulmula karafa na Ajaokuta, sun ki yashe kogin Neja, sun rusa Bankin Arewa (BON) da sauran masana’antu sun mallake gidajen gwamnati da manyan filaye a Abuja.

A sa ido a kan tsofaffin shugabanni kafin a je ga kama su da kwace duk dukiyar da suka sace mana.  Duk kadarorin da aka kwato kada a sayar don babu masu kudin saye sai dai su. Gara a bai wa bankuna jingina a karbi kudin a yi wa talakawa aiki da su, har sai an kwato duk kudin da barayin suka sace baki daya, sannan a hukunta su.

Duk sun rabe komai a tsakanin junansu, sun tsiyata kowa. karin kudin mai da rusa darajar Naira, barayin shugabannin kadai ne suke amfana. Yayin da mu talakawan da aka yi wa sata, jarinmu yake rushewa. Ma’aikata albashinsu yake gaza biya musu bukatar mako guda, masu sana’o’in hannu: jima, rini, kira, dukanci, noma da kiwo ba sa samun abin da za su rike kansu saboda an kashe sana’o’in.

Rikicin Boko Haram ya hada da su, kowa ta kansa yake yi ba ta sana’a ba, saboda satar mutane da kashe mutane.

Tsaron rayuka da lafiya da dukiya yana bukatar garambawul mai karfin gaske, haka tattalin arziki da siyasa. Idan aka yi musu cikakken garambawul suka yi saiti babu wani barawo ko fajiri ko dan kungiyar asiri da zai taba zama mai mulki a Najeriya. Kunun zaki bai isa ya bai wa koko tsoro ba, sai dai in kokon ne ya zama tsararo, ba sukari.

Duk wanda bai goyi bayan wadannan shawarwari ba, shi ma yaron barayin ne, dan leken asiri, mai fuska biyu, a bincike shi, gida da waje.

Duk wanda yake son Shugaba Muhammadu Buhari ya gama lafiya ya sadu da Allah salin alin, wajibi ne ya ba da tasa gudunmawar a hukunta duk wadanda suka jefa Najeriya a cikin halin da muke ciki.  Duk wadanda suke kaunar talakawa da adalci wajibi ne su bad a hadin kai a kwato duk dukiyar Najeriya da aka sace daga duk inda aka kai aka boye.

Duk kasar da ba ta taimaka an dawo mana da dukiyar Najeriya da barayi suka boye ba, ta tabbata kasar barayi, ta fi kaunar barayi, maimakon mu, masu dukiyar. Tilas a yanke huldar jakadanci da ita, kada ta ci gaba da yi mana illa. Wannan aikin ya fi karfin ’yan sanda ko Hukumar EFCC sai kwamiti na musamman.

Sun rusa titunan jiragen kasa domin su bai wa kamfanoninsu gina titunan manyan motoci, marasa inganci (tarkon mutuwa). Duk shekara sai an yi face-facen hanya,  baicin asarar rayuka,.

Sun rusa kamfanin jiragen sama na Najeriya (Airways)  mai jirage kusan hamsin ko fiye domin kafa nasu kamfanonin jiragen sama masu cike da hadari da rashin tabbas da leken asiri. Sun rusa Kamfanin Sadarwa (NITEL) domin su kafa nasu kamfanonin sadarwar na leken asiri, sun rusa kamfanin wutar lantarki (NEPA) domin su kashe duk manyan masana’antu su rika shigo da janaretoci, suna shigo da kayan da muke sana’antawa a Najeriya don su tsauwala farashi, ga asarar ayyukan yi. Sun rusa matatun mai domin su rika shigo da tatacce da dangoginsa suna nunnunka farashi. Da ma, idan maimakon a tace a Najeriya aka ce sai an fita da gurbataccen an tace a wata kasa mai tsadar kudin aiki da kudin dako na fitarwa da kawowa da ma jiragen ruwan nasu ne, duk wannan ya sa dole farashin mai ya yi tsada, sannan a shigo da shi, a tace ba tare da sauran dangoginsa ba, ai tilas ya yi mugun tsada, ga rasa aikin yi na ma’aikatan matatun namu, uwa-uba duk sun rabe rijiyoyin man a junansu.

Wadannan su ne matsalolin da suke gaban Muhammadu Buhari a matsayinsa na Shugaban kasa mai cikakken iko, wanda jami’an tsaro da kotuna da alkalai da dukiyar kasa da baitul mali suke a karkashin ikonsa. Wadanda Allah Zai turke shi ya yi bayani a kan yadda ya gudanar da su.

Allah (SWT) Ya tsara, duk kasar da Ya halitta, komai girmanta, komai yawan mutanenta Ya tanadar musu duk abin da suke bukata na rayuwa, sai dai idan an samu rashin iya mulki ko zalunci.

Alhaji Abdulkarim daiyabu, shi ne Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN), kuma tsohon Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Harkokin Ma’adanai da Ayyukan Gona ta Jihar Kano,  kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar Alliance for Democracy (AD) ta kasa, za a iya samunsa ta: 08023106666, 08060116666