Budaddiyar wasika ga Shugaban Hukumar Kwastam Kanar Hamid Ali (Ritaya)

A yau kuma MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN (09093467171) ta rubuta budaddiyar wasika ce ga Shugaban Hukumar Kwastam ta kasa, Kanar Hamid Ali (ritaya), inda ta bijiro masa da wasu shawarwari tare da jan hankali, wadanda babu shakka abin dubawa ne; muddin dai ana son a fitar da jaki daga duma. Wadanne shawarwari ne  da wannan […]

Budaddiyar wasika ga Shugaban Hukumar Kwastam Kanar Hamid Ali (Ritaya)
Budaddiyar wasika ga Shugaban Hukumar Kwastam Kanar Hamid Ali (Ritaya)

A yau kuma MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN (09093467171) ta rubuta budaddiyar wasika ce ga Shugaban Hukumar Kwastam ta kasa, Kanar Hamid Ali (ritaya), inda ta bijiro masa da wasu shawarwari tare da jan hankali, wadanda babu shakka abin dubawa ne; muddin dai ana son a fitar da jaki daga duma. Wadanne shawarwari ne  da wannan hazikar mai sharhi ta rattabo? Mu karanta mu gani:

Ya kai Shugaban Hukumar Kwastam, mu ’yan kasa, mun yi murna, mun yi farin ciki da wannan mukami da Allah Ya ba ka. Lallai nadin da aka yi ma na shugabancin wannan muhimmiyar hukuma, in sha Allahu yana cikin addu’ar da muka yi wa wannan kasa ta neman canji kuma Allah Ya amsa, tun da Ya nada ka shugaban wannan katafariyar hukuma, mai muhimmanci a kasa.
Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, ya kamata ka san cewa wani abu da ya jima yana yawo a cikin zukatan ’yan Najeriya shi ne, Hukumar Kwastam ta yi kaurin suna wajen cin hanci da rashawa, tare da kwacen kayan mutane ba bisa hakki na shari’a ba, da dai sauransu. A zahirance, wasu sun yi amanna da hakan, sabanin wasu da suke ganin ba dai duka aka taru aka zama daya ba. Sai dai koma me aka ce, ko za a ce dangane da hukumar da ke sa idanu a kan fasa-kwauri da shigowar kaya cikin kasa, tana daya daga cikin hukumomin da ke samar wa kasa kudin shiga a kan lokaci. Domin takan kawo adadin harajin da aka dora mata, wani lokacin ma tun kafin cikar wa’adin da aka sanya mata.
To, sai dai kuma bayan hawan Shugaba Buhari, tun kafin a je ko’ina, tsohon jagoran hukumar, Dikko Inde ya yi murabus kuma ya jaddada cewa a duk lokacin da ake bukatar karin haske ko bayani a kan komai na jagorancin da ya yi, zai gurfana don yin karin haske. Jin hakan ya sa mutane suka shiga kalaman jinjina da yabawa a gare shi.
Bagatatan, sai Shugaba Buhari ya dauko ka, ya damka maka wannan katuwar hukuma, ina nufin kai kanka, Kanar Hamid Ali (mai ritaya). Tun daga lokacin ne aka fara kalamai masu cin karo da juna, na dacewar hakan ko akasin hakan. Amma dai a zahiri, kundin tsarin mulki ya aminta tsohon soja ya jagoranci hukumar ta Kwastam. Kuma har ma a cikin bayaninka na kama aiki, ka bayyana cewar gyara ka zo yi da sabunta hukumar, ba tare da nuna sani ko sabo ba.
Lallai mu talakawa mun ji dadi, mun yi murna da jin wadannan kalamai naka masu nuna bayyanar canji karara kuma mun san za ka iya.
Tun daga wannan lokaci aka daina jin duriyar hukumar, sai a wancan satin da ya shude aka ji mataimakanka su biyar sun rubuta takardar ritaya ta ganin dama – abin da ya dagula lissafin mutane da yawa a kasar nan. Ko mu ce abin da ya daure wa kowa kai a kasa.
Kwana guda da hakan, hukumar ta fitar da takardar sallamar aiki mai dauke da sunaye kusan mutane talatin da wani abu. Aka ce wai in dai suna cikin hukumar, ba za a samu gyaran da ake bukata ba.
A baya-bayan nan ma, an ce akwai wasu jami’an hukumar ku san su 400 da za a watso su waje, wai duk a cikin kawo canji da aikin gyaran da aka fara.
Madallah! A gaskiya kam in don batun gyara ne, babu shakka Hukumar Kwastam na bukatar gyaran fuska, har da saisaye. Sai dai mu muna da wasu korafe-korafen da namu hangen da namu shawarwari da muke son mu kai su gaban shugaba. Wadannan kuwa su ne kamar haka:
A gaskiya idan dai aka fara ta haka, to akwai ’yar matsala. Ba wai muna goyon bayan a yi sata muke nufi ba ko a kyale almundahana ta ci gaba da gudana ba. A’a, mu sai muna ganin kamar an yi gaggawar daukar mataki irin wannan. Ai duk shugaba yana son hadin kan ma’aikatansa kuma ai masu hikima sun ce da tsohuwar zuma ake magani. Kuma kamar yadda ka rigaya ka sani ne, da zarar an jefa wa ma’aikaci fargaba da rashin walwala a cikin aikinsa, ta yadda zai rika ganin tamkar tarko aka kafa masa don ya kama shi ya afka, to kishin aiki da rike amanar aiki za su raunana a zuciyarsa.
Haka nan aiki da tsohon hannu yana da ma’ana sosai. Mu dai shawararmu a nan ita ce, kawai a yi masu gargadi da tunatarwar cewa, wannan gwanmatin ba ta rashawa da sata ba ce kuma dama sun san da hakan. A hankali a duba wadanda suka cika adadin lokacin da ya kamata a yi masu ritaya, sai a yi masu; a ba su hakkokinsu a mutunce, su tafi suna murna. Kana iya sabunta wa ma’aikatanka bitar kundin tsarin mulkin hukumar, don kowa ya tuna kuma ya san da cewa kowane kuskure da laifi ga hukuncinsa.
Abin da ake tsoro, ya mai girma Shugaban Kwastam shi ne, idan hakan ya ci gaba, wato ana korar ma’aikata, to hukumar za ta zama abar barazana ga ma’aikatanta kuma kai ma kanka aikin zai kasance mai wahala a gare ka. Kuma a gaskiya daga karshe hakan matsala zai haifar, komai ya dagule, domin samun bakin zaren matsalolin da aka hango zai yi wuya. Ga shi kuma ba a samu sauyi ko ci gaban da ake muradi ba. Shi kansa shugaba mai mulki, an maida ma shi hannun agogo baya, domin an kara masa adadin marasa aikin yi da yake ta fatutukar ya rage adadinsu.
Allah Ya sa Shugaban Kwastam ya sadu da wannan wasika tawa kuma ya amfana da shawarwari da hangen da take dauke da su, amin.