Budaddiyar Wasika Ga Shugaban Jam’iyyar PDP
A yau kuma, Malama A’isha Usman Liman [email protected] ta karkata alkalaminta ne zuwa ga Shuagaban Jam’iyyar PDP na kasa, Alhaji Ahmad Adamu Mu’azu, inda ta ja hankalinsa zuwa ga wani kuskure da suke shirin tafkawa. Me malamar take cewa ne? Mu karanta a tsanake: Ya mai girma Shugaban jam’iyar PDP na kasa (Alhaji Ahmad Adamu […]
A yau kuma, Malama A’isha Usman Liman [email protected] ta karkata alkalaminta ne zuwa ga Shuagaban Jam’iyyar PDP na kasa, Alhaji Ahmad Adamu Mu’azu, inda ta ja hankalinsa zuwa ga wani kuskure da suke shirin tafkawa. Me malamar take cewa ne? Mu karanta a tsanake:
Ya mai girma Shugaban jam’iyar PDP na kasa (Alhaji Ahmad Adamu Mu’azu), na rubuto wannan wasika ne musamman zuwa gare ka; domin in ba ka tawa gudunmowar shawara a kan yadda kake gudanar da ayyukan ofishinka, kai da sauran shugabanni da mambobin jam’iyar PDP. Kodayake ni ba ’yar siyasa ba ce amma kuma ni ’yar Najeriya ce mai kishin ganin ta ci gaba.
Ya mai girma shugaban jam’iyya, mun yi murna kwarai da gaske a lokacin da jam’iyarka ta zabo ka, ta ba ka ragamar shugabancinta saboda mun san ta yi zabe nagari na cancanta, tun da ta zabo mutumin da ya kware a fagen siyasa da kishin kasa da sanin ya kamata. Ba wai zuga ba, a gaskiya samun kamarka a fagen siyasar kasar nan da hali nagari, tun lokacin su Firimiya. Kuma a dalilin haka ne ma jam’iyyarka ta ga kai kadai ne za ka iya kai ta ga gaci, a lokacin da ruwa ya so ya cinye ta.
Lallai ka samu aiki mai yawa kuma cikin yardar Allah, sannu a hankali cikin lokaci kankane ka samo bakin zaren al’amarin kuma ka kwance dukkan wani zarge da ya zarge jam’iyyar. Muka yi murna kuma muka yaba maka.
Amma matsala daya da muka lura da ita, wadda ba mu sani ba ko kai ba ka lura da ita ba ko kuma ka lura da ita amma kana nan kana kokarin ganin ka warware ta cikin hikima da wayau da zurfin tunani irin naka. Matsalar kuwa ita ce maganar tsaida dan takarar Shugaban kasa da jam’iyya take ciki a halin yanzu. Abin da ya bayyana a gare mu shi ne, dukkan gwamnonin jam’iyyarku sun amince wa mai girma Shugaban kasa ya dauki takara ba hamayya kuma dukkan mambobin jam’iyya su ma suna ta kokarin ganin sun tsayar da shi ba hamayya.
To, a gaskiya shugaban jam’iya, yin hakan babbar matsala ce a gare mu. Abin lura a nan shi ne, yana da kyau a ba mutum aiki daidai da abin da zai iya yi, wanda ba zai iya ba a yi masa hakuri ko uziri. Shi mutum ajizi ne, kowa da kwazonsa kuma kowa da lurarsa da hikimarsa daidai da shi. Bai kamata a tilasta wa mutum a kan abin da aka san ba zai iya ba, ko a zuga shi a kan abin da aka san ba zai iya kai labari ba; don ana ganin yin hakan kara ce ko karamci ko girmamawa a gare shi. Abin nufinmu a nan shi ne, magana ta gaskiya a halin da kasar nan take ciki a yanzu ta fi karfin Shugaba Jonathan ya ci gaba da mulkinta, domin duk wata dama da ya kamata a ce ya samu kuma ya yi aiki da ita, kun ba shi kuma ya yi ta daidai da kwazonsa kuma daidai da iyawarsa. Sai dai shi kwazon da iyawar nasa ne ba su isa ba kuma ba su gamsar da kasar ba. Tilasta masa ko zuga shi ya ci gaba a hakan babbar nakasu ce ga babbar jam’iyya irin PDP, mai ikirarin ganin ta zama giwar jam’iyyun nahiyar Afirika.
Jam’iyyar PDP babbar jam’iyya ce da ta kunshi mutane manya da kanana a cikin kowane sako na kasar nan. Don haka muke ganin cewa ba ya cancanta ko kamata ga shugaban jam’iyya ya yi zugum yana kallon ana caccanza tsare-tsarenta ko manufofinta ko ka’idojin jam’iyyar haka kawai, don a dadada wa mutun daya ko wasu mutane; alhalin jam’iyya ce take da ikon sa wa ko hanawa. Har wayau, jam’iyya tana da karfafan mambobi wadanda kwazonsu da hikimarsu za su iya daukaka darajarta kuma su kara mata kauna da kima ga al’ummar kasa.
Ku duba fa ku gani halin da kasar nan take ciki a halin yanzu – ba tsaro, ba bin dokokin kasa, cin hanci da rashawa sun yi yawa, ga bambance-bambancen yanki da na kabilanci da ma na addinai ko’ina a kasa. Kuma kun san wannan duk gazawa ce ta Shugaban kasa, ba ta jam’iyya ba, domin kuwa ai ba shi ne ya fara shugabancin kasa nan a karkashin jam’iyyar PDP ba. Kuma in tsantsar kauna ce ta sa kuke son ku kara tsaida shi, ni ina ganin ai ba ku fi tsohon Shugaban kasa Obasanjo so da kaunar shi ba. Shi fa ne ya hada ku da shi amma kuka ga ya fito fili ya koma gefe, ya zayyano gazawarsa da nakasunsa. To shi ne mu za ku ci gaba da kakaba mana shi, alhali duk ta bayyana a fili ba zai iya ba? Ba ma shi kadai ba, duk wani dan majalisa ko gwamna da kuke son ku ba tikitin sake taka takara ba hamayya, to an saba ka’idar siyasa ta gaskiya kuma an koma turbar son kai. To sauran ’yan siyasa (’yan jam’iyya) fa da suke da burin ganin su ma sun hau sun ba da tasu gudunmowar, yaya za ku yi da su?
Gaskiya shugaban jam’iyya, ya kamata ku sa madubin hangen nesa ku hango kuma ku kara dora Shugaba Jonathan a kan sikeli ku gani. In sha Allahu za ku ga nauyinsa ba zai kai ya iya sake jan ragamar shugabancin kasar nan ba.
Ya mai girma shugaban jam’iyya, muna sane da cewa duk wanda mutum ke so ba ya ganin laifinsa. Shi ya sa muka ce bari mu dan haska muku don ku gane irin halin dimaucewar da kasa take ciki, a kan wannan shawarar da kuke son dauka a jam’iyya. Kuma ku gane irin kuskuren da kuke dab da tabkawa a kan wannan shawara taku. Kuskure mana! Don gaskiya yin hakan zai iya ja muku faduwar zubargada a babban zabe na gaba. Kun ga kuma ke nan alwashin da kuka sha na ganin kun shekara takwas sau goma jam’iyyar PDP na mulkin Najeriya ya hadu da kalubale tun daga cikin gida. Ni wallahi da ma za a nemi shawarata, da na ce kai shugaban jam’iyyar ne ma ka fi cancanta da taka takarar wannan kujerar ta shugabancin kasar nan a jam’iyyarku ta PDP.
Daga karshe, ina rokon ’yan jam’iyya da suka ga wannan shawara ba ta yi masu dadi ba, to su yi hakuri amma kuma ina rokon su da su dora shawarar a kan sikili na gaskiya, su auna su gani kuma su koma baya su tuna su ga yadda suka ji a lokacin da aka dora musu tsohon shugaban jam’iyya (Alhaji Bamanga Tukur) da suka gane bai da kwazon da zai iya jan ragamar shugabancin jam’iyya, ba haka suka rika kokowa ba da korafi da bore, har ta kai ga wasu suka yi tawaye, suka balle daga jam’iyar ba? Wanda har ya kai ta ga mummunar hasarar da ta rasa gwamnoni har biyar, mambobi ko ba adadi. Gaskiya in ba ku yi hattara ba, abin da zai sake faruwa ke nan a babban zabe mai zuwa.
Allah Ya sa shugaba da sauran mambobin jam’iyyar PDP su duba wannan shawarar da idon basira, amin. Wassalam.