Budaddiyar Wasika ga Shugaban kasa Buhari

Godiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya tabbatar da kai a matsayin shugaban wannan kasa tamu Najeriya. Ba za mu iya fasalta farin cikinmu ba, musamman mu talakawa game da samunka a matsayin jagoranmu, sai dai mu yi ta addu’a kan Allah Ya jagorance ka, ka cika burin da muke fata; ta samun kyakkyawan jagoranci […]

Budaddiyar Wasika ga Shugaban kasa Buhari
Budaddiyar Wasika ga Shugaban kasa Buhari

Godiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya tabbatar da kai a matsayin shugaban wannan kasa tamu Najeriya. Ba za mu iya fasalta farin cikinmu ba, musamman mu talakawa game da samunka a matsayin jagoranmu, sai dai mu yi ta addu’a kan Allah Ya jagorance ka, ka cika burin da muke fata; ta samun kyakkyawan jagoranci daga gare ka bayan mun shafe shekaru muna shan wahalhalu a hannun shugabannin da suka gabata.

Hakika muna daukarka a matsayin jagoran ceton talakawa irin Malam Aminu Kano, sai dai muna sane guguwarka ta Buhariyya ta taho da wasu gwamnoni da sanatoci da ’yan Majalisar Tarayya, wadanda ba irin akida da halinka suke da su ba. Kuma ya kamata mu shaida musu cewa mu talakawa muna sanar da su yanzu fa ba irin tafiyar da suka saba za a yi ba. Don haka su tsaya kan gaskiya da amana su guji cin amanar wadanda suka zabe su. Idan sun yi haka a baya, yanzu fa lokaci ya canja, su tsaya su yi abin da zai amfani kasa da al’umarta domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali su dawo.
Bayan haka muna rokon Shugaban kasa da gwamnoni musamman na Arewa su dubi talakawa da ke kasa kaya a bakin hanya da idon basira, wadanan mutane da so samu ne za su so a ce su ne masu manyan shaguna da rumfuna a cikin kasuwanni da bakin tituna. Amma tunda ba su da karfin yin haka ne suka kasa kaya a gefen titi domin su samu abin da za su kare bukatunsu da na iyalansu. Sai sun kasa kayan nan suke samun na abinci da na biya kudin hayar gidajen da suke ciki da na ilimin ’ya’yansu, don haka bai kamata a rika bin su ana kwace musu kaya ana dada talautar da su ba. Idan har hukumomi da shugabannin ba za su tallafa musu ba, bai kamata su dada jefa su a cikin bala’i ba, kamata ya yi duk mai kokarin neman halalinsa a taimake shi ba a dada karya shi ba, yin haka zai jawo fushin Allah da karuwar masu aikata miyagun ayyuka, musamman a Abuja, inda nan ne aka fi tozarta masu talla ko dafa abinci a wuraren da idan ma aka tashi mutane suna iya zama mafakar barayi da miyagu.
Mene ne alfanun ka rushe wurin sana’a ko kasuwanci ka bar shi ya tara ciyawa da bola? Wannan shi ne galibin abin da ke faruwa a Abuja, inda in ka yi magana sai a ce ai ba a gina birnin don talakawa ba, shin mai dukiya da mai mulki zai rayu ba talaka ne?
Don haka muna fata Shugaban kasa da gwamnoni da mukarraban gwamnatin nan za su dubi yadda ake musguna wa masu kananan sana’o’i da kasuwanci a Abuja da sauran biranen kasar nan don kawo musu sauki ko samar musu mafita, maimakon karya su da hakan yana iya mayar da wasu daga cikinsu masu aikata miyagun ayyuka.
Allah Ya taimake mu, Ya tabbatar da zaman lafiya a kasar nan.
Alhaji Musa Muhammad Dukawa, P.O Bod 754, Kano (08133711801)

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna