Budaddiyar wasika ga Yakubu Soja

Gaisuwa mai yawa da fatan alheri zuwa ga mai girma mai taimaka wa gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai na musamman a kan harkar tsaro Kanal Yakubu Yusuf Soja mai ritaya. Na rubuto maka wannan budaddiyar wasikar ce ta hanyar wannan jarida mai farin jini wajen al’umma domin in tunatar da kai cewa mu […]

Budaddiyar wasika ga Yakubu Soja

Gaisuwa mai yawa da fatan alheri zuwa ga mai girma mai taimaka wa gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai na musamman a kan harkar tsaro Kanal Yakubu Yusuf Soja mai ritaya.

Na rubuto maka wannan budaddiyar wasikar ce ta hanyar wannan jarida mai farin jini wajen al’umma domin in tunatar da kai cewa mu Jarumai da Gora na Hayin Banki muna bukatar mota.

Ina wannan rubutu ne a matsayina na wakilin Jarumai da Gora, Hayin Banki Kaduna. Sanin ka ne cewa wannan kungiya ita ce mai fafutukar kare lafiya da samar da zaman lafiya a unguwar Hayin Banki da kewaye. Sanin kowa ne cewa mun samar da zaman lafiya a Hayin Banki, har ma muna kai dauki ga makwabtanmu. Kuma cikin ikon Allah, duk inda muka kai dauki, ana samun sauki da nasara. Allah Ya dafa mana matuka, kuma mutane suna sambarka. Kuma na ce ina tunadar da kai ne saboda na san cewa ka san duk ayyukanmu, kai namu ne, mu naka ne, kuma mun san cewa ka na yi, domin a lokacin da ka zo wajenmu a wancan lokacin, har kudi ka ba mu domin mu kama ofis. Kuma kana yawan yabo da ambaton ayyukan a matsayin misali, saboda kana jin dadin yadda muke samun nasara.

Daga cikin nasarorin da muka samu tun lokacin da muka fara aiki, mun samu nasarar dakile ta’addanci a kewayen, ta hanyar magance ’yan sara-suka da ake kira da ’yan shara. Sannan mun magance matsalar sace-sace da kwace da suka yi wa kewayen katutu. Sannan mun mun dakile matsalar rashin tarbiya a tsakanin matasan garin da kewaye.

Mai girma, ina mai farin cikin sanar da kai cewa ayyukanmu ba su tsaya a Hayin Banki ba. Mun wuce nan, domin muna kai dauki a unguwannin da suke makwabtaka da mu. Duk inda aka samu matsala musamman harkar ta’addanci da sara-suka, akan kira mu mu je mu kai dauki. Kuma cikin ikon Allah, duk idan mun je ana samun nasara. 

Mai girma Yakubu Soja, sai dai duk irin kokarin da muke yi, kullum muna samun matsalar harkar sufuri. A duk lokacin da aka bukaci taimako a wasu unguwanni, ko kuma a nan cikin unguwar, sai mun nemi motar haya, mun biya kudi kafin a kaimu, wanda a sanadiyar hakan, wani lokacin kafin mu kai unguwar, sai ka ga har ’yan ta’addan sun gudu. Wannan lamarin yana ci mana tuwo a kwarya. Wani lokaci kuma sai dai mu nemi aron mota, sannan mu sha mai da za mu yi amfani da shi.

daukacin wannan ayyukan da muke yi, muna yi domin Allah ne, sannan don taimakon mutane. Ina da yakinin cewa da kai da sauran shugabannin Jihar Kaduna kuna gani, kuma kuna jin dadin kokarin da muke yi duk da cewa ba a ba mu ko kwabo. Rashin ba mu kudi, ba shi ba ne matsalar, babbar matsalar ita ce rashin kayan aiki, musamman rashin motar da za mu rika zirga-zirga.

Wannan ne ya sa na rubuta maka wannan wasika domin na san cewa za ka iya, kuma kana yi, domin mun samu labarin unguwannin da ka taimaka musu kamar haka.

Babban burinmu shi ne mu samar da zaman lafiya, kuma mun sadaukar da lokutanmu da rayukanmu ne domin kawai a samu zaman lafiya mai dorewa. Don haka muna a taimaka mana domin mu samu saukin aiki.

Da fata wannan wasika za ta kai wajen Yakubu Soja, ko kuma wadanda za su isar masa da sakon. 

Suleman Khalid, Komanda na Jarumai Da Gora, Hayin Banki Kaduna. 07036600999