Budaddiyar wasika ga zababben Gwamnan Kano, Abba Gida-Gida

A zaben bana ma Sanata Kwankwaso ya sake dibarku kuka sake canja sheka.

Budaddiyar wasika ga zababben Gwamnan Kano, Abba Gida-Gida

Abba Gida-Gida

Kafin in ce komai a kan wannan wasika ina rokon Allah (SWT) Ya ba ka abokan aiki nagari Ya kuma yi riko da hannayenku ta yadda za ku samu damar sauke dimbin nauyin tafiyar da mulkin al’umma da Ya dora maku, amin summa amin.

Ya Mai girma Gwamna mai jiran gado, Injiniya Abba Kabir Yusuf da ake yi wa lakabi da Abba Gida-Gida, ka dai san irin gwagwarmayar da ka sha kafin Allah Ya kai ka ga wannan matsayi da ka fara nema a zaben shekarar 2019, a inuwar tsohuwar jam’iyyarku ta PDP.

Kai da jagora kuma ubangidan siyasarka Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma dan takarar Shugaban Kasa a sabuwar jam’iyyarku ta NNPP a zaben da ya gabata.

Ya kamata in tunatar da kai cewa tunda aka fara wannan mulkin dimokuradiyya a 1999, inuwar jam’iyya daya kuke da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, kuma a karkashin jagoranci jagoranku Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, in ban da a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019, da aka karya kara a tsakanin Sanata Kwankwaso da Gwamna Ganduje.

Wannan raba gari da aka yi tsakanin Gwamna Ganduje da Sanata Kwankwaso, ita ta ba da dama Sanata Kwankwaso da ku magoya bayansa kuka bar Jam’iyyar APC kuka koma zuwa tsohuwar jam’iyyarku ta PDP, kuma ya tsayar da kai takarar Gwamnan Jihar Kano a zaben shekarar 2019, inda kuka fafata da Gwamna Ganduje na Jam’iyyar APC, Allah cikin ikonSa Gwamna Ganduje ya yi nasara.

A zaben bana ma Sanata Kwankwaso ya sake dibarku kuka sake canja sheka daga jam’iyyarku ta PDP kuka koma Jam’iyyar NNPP, inda ya sake tsayar da kai dan takarar Gwamnan Jihar.

Zaben da a wannan karo ka yi nasarar lashe shi, baya ga sanatoci biyu daga cikin uku da ’yan Majalisar Wakilai 19 daga cikin 24 da kuma gagarumin rinjaye a ’yan Majalisar Dokokin Jihar da jam’iyyarku ta samu.

Alhamdulillah! Yanzu ka yi nasara, kuma mutanen ciki da wajen Kano sun san cewa gwamnatinka gyauron gwamnatin Kwankwaso ce.

Ma’ana za ka zartar da manufofi da aikace-aikace irin wadanda gwamnatinku ta Kwankwasiyya ta aiwatar, kamar yadda ka sha nanatawa a lokacin kamfen, shi ya sa mata da matasa’yan dangwale suka shige gaba wajen tabbatar da nasararka.

Samun wannan nasara da ka yi ta sa har ka fara ba da shawarwari a kan wasu ayyuka ko batutuwa da gwamnatin da za ka gada take kai.

Alal misali ta hannun Sakataren Yada Labaranka, Sanusi Bature Dawakin Tofa zuwa yanzu ka fitar da wasu bayanai guda biyu.

Na farko ka shawarci duka mutanen da gwamnati mai ci yanzu ta raba ko ta sayar wa fila a cikin ko jikin gine-ginen gwamnati irin su makarantu da asibitoci da masallatai da makamantansu, lallai su dakatar da yin gine-gine, don kuwa gwamnatinka za ta binciki yadda aka yi rabon.

Na biyu, ka shawarci bankunan kasuwanci su dakatar da ba gwamnatin jihar rance ko lamunin koda sisin kwabo ne.

Sanarwar da ka kira shawara, amma kuma ka ce wanda bai ji bari ba zai ji hoho!

Masana harkokin siyasa da na shari’a, duk suna ganin ka yi azarbabi, kasancewar wa’adin wannan gwamnati ba zai kare ba sai ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.

Da wannan ke nan daga nan zuwa wancan lokaci duk abin da gwamnatin Ganduje ta yi halal ne, don haka kamata ya yi ka kara hakuri sai ka karbi ragamar mulkin jihar.

Ya Mai girma Abba Gida-Gida ka fi ni sanin abin da batun fili yake ciki a yau har ma a gobe in Allah Ya so a jihar.

Kai ka sani cewa kasancewar mutanen jihar Musulmi ne, ya sa ba ka jin ana tashe-tashen hankula da kashe-kashen rayukan al’umma a kan rikicin fili a jihar kamar yadda ake yawan yi a jihohin Kudancin kasar nan.

Duk da ba a samun tashe-tashen hankula da kahe-kashe a kan rigingimun filaye, amma dai a bayyane take kotunan jihar makare suke da dimbin shari’u na shekaru aru-aru a kan rikicin fili, walau tsakanin mutum da mutum ko tsakanin gwamnatin jihar da jama’a ko tsakanin kamfanoni da gwamnati ko da jama’a, wasu shari’un ma tun zamanin gwamnatin mulkin soja ake ta bugawa.

Da wannan nake ganin in har ka ce gwamnatinka za ta waiwayi batun rabon filaye, to kuwa sai ka share shekara takwas a zangonka na daya da na biyu, ba ka gano batin zaren ba, kuma shari’un filaye da kotuna ke fama da su za su yi matukar karuwa.

Don kuwa hatta yadda gwamnatin jagoranku Kwankwaso ta raba ko ta soke izinin mallakar fili a Kano wasu na ganin an yi masu ba daidai ba, wadanda suka yi kara wurin Allah sun kai wadanda suke kotu suna kotu.

Ka ga ke nan allura na iya tono garma. Akwai kuma batun sababbin masarautun Bichi da Rano da Karaye da Gaya da gwamnatin Ganduje ta kirkiro.

Koda yake na ji a lokacin kamfen dinka a cikin amsa tambayar abokan aiki ka ce ba ka san yadda aka kirkire su ba, amma in ka zo gwamnati za ka duba yadda aka kirkire su ka kuma tsaya a nan.

A nan ina ga ya kamata ka bar wannan batu yadda aka kirkire su, da fatar ka yi kokarin ganin inganta garuruwan hedkwatocin masarautun da yankunan masarautun baki daya da dukkan ayyukan ci gaban da suka kamata.

Kasancewar yanzu wadannan masarautu hudu sun shiga cikin zukatan mutanensu a zaman wani abu na ci gaba ya fara samun yankunansu.

Na ji wasu da ban san yadda zan kira su ba a Kano, har sun kafa wata sabuwar kungiya wai ita Abba-Tsaya-da-Kafarka.

Tunda mulkin dimokuradiyya ake yi suna da ’yancin yin haka, amma ka yi hankali da su ba sai na buda ba. Mutanen jihar sun shaide ka a kan ba ka da hayaniyar siyasa irin ta jagora.

In ka iya hakuri da shi, karshe kai ne Yarimansa kamar yadda na ji yanzu wasu sun fara kiranka. Ka ga dai yadda suka kare da Gwamna Ganduje duk tsananin biyayyar da ya rika yi masa a tsawon shekarun da suka yi.

Ina fata cikin bincikar wannan gwamnatn da za ka gada, za ka rika cizawa kana hurawa, don kada daga karshe bukata ta taso ka yi amai ka lashe, kamar yadda Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya yi, bayan ya shafe shekara kusan takwas yana tuhumar tsohon Gwamnan Jihar Barista Ibrahim Shehu Shema da laifin yin sama-da-fadi da biliyoyin Naira na al’ummar jihar, amma bukatar ya taimaka masa a zaben da ya gabata tana kunno kai sai Kwamishinan Shari’a na Jihar ya ba da umarni a sanar da kotun ya janye dukkan laifuffukan da ake tuhumar tsohon Gwamnan, haka kuma aka yi.

Ita ma Gwamnatin Shugaba Buhari mai ikirarin yaki da cin hanci da rashawa bayan ta yi nasarar daure tsofaffin gwamnonin jihohin Filato Mista Joshua Dariye da Rabaran Joly Nyame na Taraba, wane-tudu wane-gangare kwatsam! Sai ta ce ta yi masu afuwa.

Ina sake jaddada addu’ar Allah Ya yi riko da hannayenku ta yadda za ka samu sauke nauyin dimbin matsalolin da za ka gada musamman biyan ma’aikata dimbin bashin kudaden sallama na yin ritaya.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos