Budaddiyar wasika zuwa ga amaryata (2)

Ki yi mini alkawarin cewa ba zan kai ruwa rana da ke ba a cikin abin da ya shafi ibadar Allah. Idan lokacin Sallah ya yi, in ga kin sa kaimi wajen yin ta. Ki lizimci karatun Alkur’ani Mai girma a cikin gidana, kuma ki mayar da hankali a kan karatun da zan ci gaba […]

Budaddiyar wasika zuwa ga amaryata (2)

Amarya

Ki yi mini alkawarin cewa ba zan kai ruwa rana da ke ba a cikin abin da ya shafi ibadar Allah. Idan lokacin Sallah ya yi, in ga kin sa kaimi wajen yin ta. Ki lizimci karatun Alkur’ani Mai girma a cikin gidana, kuma ki mayar da hankali a kan karatun da zan ci gaba da  koyar da ke na littattafan addinin Musulunci.

’Yan uwana dukansu ’yan uwanki ne. Mahaifiyata kuma mahaifiyarki ce. Kamar yadda Allah Ya san a haka nake daukar mahaifanki da ’yan uwanki! To ba dominsu ba, da ba ki samu tarbiyyar da ta ja hankalina zuwa ga aurenki ba! Ba domin wadannan mahaifan naki masu albarka sun haifa ba, da ni ban samu ba. Da ba su ba ni ke ba, da ba a yi maganar aurena da ke ba.

Saboda wannan dalilin ma, na samu zama da mahaifiyata wadda take matukar sonki da kaunarki, muka tattauna a kan yadda zamanku zai kasance idan Allah Ya nufe ki da zuwa gidana. Mahifiyata tana da hakuri, kuma na tabbatar za ta ba ki uzuri a duk inda kika samu kuskure a cikin hakkinta. Kuma za ta taimaka miki a duk inda bukatar haka ta taso. To ke ma ina neman ki daukar mata uzuri a duk inda ta shiga naki hakkin.

Ni kuma na yi miki alkawarin duk abin da kike so a wajena, zan yi miki shi ba tare da bata lokaci ba, in dai bai fi karfina ko ya saba wa shari’a ba. To idan ban yi miki ba wa zan yi mawa? Ke din nan fa, ke ce Allah Ya dauke nauyinki daga kan kowa ya dora a kaina. Kuma wajibin kowane Musulmi ne sauke nauyin da Allah Ya dora masa.

Ya ke amaryata! Zan kasance kusa da ke a duk lokacin da kike bukatar haka, zan share hawayenki in haskaka zuciyarki! Ba zan bari komai ya cutar da ke ba wallahi, muddin ina da iko a kan hakan. A shirye nake in kare mutuncinki da martabarki. Rayuwata fansa ce ga rayuwarki.

Daga karshe ina son ki isar mini da godiyata ga mahaifanmu masu albarka. Ki gaya musu ina godiya a kan karimcinsu a gare ni. Kuma ba zan manta da su ba har abada. Har ila yau, ki gaya wa kawayenki, ina musu godiya da fatar alheri. Allah Ya ba su maza nagari. Kuma ki hore su da amfani da dukkan abin da na gaya miki a cikin wannan takarda idan lokacin aurensu ya zo.

Har zan rufe, na manta ban gaya miki sakon gaisuwar abokaina ba, wadanda a gabansu nake rubuta miki wannan wasika, wadanda tuni suka dauki alkawarin bin wannan hanyar da na bi, domin samun zaman lafiya da nasu matan.

Gaisuwar ban girma da jinjina a gare ki ya ke sarauniyar ’yan mata, ’yar autar IYAYEN GIJI (mata), ma’abuciyar hankali da tattausan lafazi da tsoron Allah! Ki huta lafiya.

Nasir Abbas Babi

08033186727