Budaddiyar Wasika zuwa ga Gwamnan Zamfara
Tare da fatan kana cikin koshin lafiya. Zan so yin amfani da wannan damar in isar da sakon da nake da tabbacin zai zo gunka. Sai dai ina son duk wani mai taimaka maka ta fannin tsaro da sha’anin matasa da ma cigaban al’umma, ka mika masa ko umurtarsa ya yi wa wannan wasika tawa […]
Tare da fatan kana cikin koshin lafiya. Zan so yin amfani da wannan damar in isar da sakon da nake da tabbacin zai zo gunka. Sai dai ina son duk wani mai taimaka maka ta fannin tsaro da sha’anin matasa da ma cigaban al’umma, ka mika masa ko umurtarsa ya yi wa wannan wasika tawa karatun ta natsu.
Ya Mai girma gwamnan jiha tun daga lokacin da Jihar Zamfara ta fada cikin matsalar tsaron da har an wayi gari mafiya yawan ‘Yan Najeriya suna kamanta ta da Jihar Borno da ‘Yan Boko Haram sunka daidaita.
Da farko ka dauki sha’anin da wasan yara har kake kallon abin da karamar matsalar makiyaya da manoma da ta zama ruwan dare game duniya. Sai dai daga baya ina ganin zuwa yanzu ka tabbatar da matsalar ta fi karfin tsirarun manoma da makiyayan Jihar Zamfara, wanda tun farko ya Mai girma gwamna ina ganin sakaci da ko-in-kula ne ya sa wannan matsalar ta cigaba da ruruwa. Saboda Rashin zama a cikin jihar, ko ma in ce wallahi wannan babbar illa ce. Duk da na ji da kunne na a BBC-HAUSA, mai taimaka maka ta fuskar watsa labarai Malam Ibrahim Dosara ya na shaida wa duniya cewa; “Kai ne gwamnan da ka fi kowane gwamna a fadin Najeriya kula da sha’anin tsaro.” Tabbas duk Bazamfaren da ya ji haka sai dai ya ce; “ta zo mu ji ta.” Kuma ba ya rasa nasaba da yadda muke ganin kullum sha’anin tsaron yana kara tabarbarewa ne. Dole ne a yi wadannan tambayoyi:
Shin hanyoyin samar da tsaron ne ka fi takwarorinka kwarewa a kansu?
Ko dai kudi ne zunzurutunsu ka fi warewa sha’anin tsaro?
Amsar da na ka sa samun mai ba ni amsarta ke nan. Kwatsam sai na tsinci dame a kala. Wani ke shaida mini cewa; zunzurutu kake ware wa matsalar tsaro duk watan Allah ta’ala. Amma sai dai kash! Sai a rasa inda kudin ya yi.
Don haka tun a ranar nake dokin feke alkalamina, domin rubuto maka shawarata, a kan wannan matsalar.
Ya Mai girma gwamna, ni dai a nawa ganin matsalar tsaron Jihar Zamfara ta farko ta samo asali ne daga sakacinka. Kuma duk wannan ya faru ne saboda rashin zamanka a cikin jihar. Shi ya sa a ke kashe mutun biyar ko sama da haka ba wani wanda zai sanar da kai. Sai ko in mu muka sunsuno, har munka sanar da duniya. Kuma hakan bai sa ka katse abin da kake yi ka dawo gida ba, ta yadda za ka binciki musababbin aukuwar lamarin. Don haka tun ana kashe ‘yan kalilan an tabbatar an fasa, an ga jini sai aka koma kan daruruwa.
Mai girma gwamna ka dauki matakai iri-iri don magance matsalar a mazahabar taka, kana ganin kana daidai. To, amma sai dai a gaskiya ina ganin da sake. Domin idan muka fara da matakinka na farko da ka fara dauka a farko-farkon shekarar nan, na hana yawo da babura daga karfe takwas na dare zuwa shida na safe, wanda kake ganin cewa tabbas zai kawo sauki.
Maganar gaskiya wannan matakin ko da dai bai kara rurura wutar wannan rikicin ba, to, wallahi ya durkusar da Jihar Zamfara, musamman manyan garuruwan jihar. Domin kasuwnaci kwata-kwata ya tabarbare, inda can ainihin ake aika-aikar dokar ba ta aiki kwata-kwata. Ke nan an bata goma biyar ba ta gyaru ba.
Sai kuma maganar dakatar da ‘yan-sa-kai. Tabbas ‘yan-sa-kai su kansu suna da ta su babbar matsalar. Domin yanzu na ji har su kansu sun fara garkuwa da mutane. To, tabbas kusan in ce kai ne sila. Domin a Jihar Zamfara ko in ce da dama daga cikin yankunan karkara a Najeriya ba su da jami’an tsaro kwata-kwata. Shi ya sa wasu ke sama wa kawunansu tsaro. Shekaru da dama ba mu ji haka ta faru ba. Sai yanzu. Wanda kamata ya yi lokacin da ‘yan ta’addar suka addabi jama’a, sai a kirawo ‘yan-sa-kai din domin su sun san ba masu laifi ba ne, gwamnati ta zauna da su ta dora su a kan babbar hanyar da za su taimaki jami’an tsaro a kawo karshen matsalar, sai gwamnati ta yi musu goma ta arziki a gode musu, tare da dora su kan hanyar noma da kiwo ta yadda za su amfani kansu da jiharsu. In kuma har akwai wadataccen fasahar samar da tsaro, tare da yawan jami’an tsaron, sai a kira su a gode musu tare da karfafa su a kan aikin da suka yi na kare rayukkan al’ummarsu tsawon shekaru da dama.
Sai dai kash a lokacin gwamnatin ba ta yi haka ba, sai dai ma hantararsu da ta yi, tare da dakatar da su. Kuma ba ta samar da tsaron a kowane lungu da sako ba. Kamar yadda al’ummar gundumar Kungurmi da ke a karamar Hukumar Bungudu sunka shaida mini cewa; “ mu wallahi ko lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani shiri mai taken operation mesa. ma mu ga an kawo mana ko jami’in tsaro daya ba,” wanda wannan ne ya harzukar ’yan-sa-kai, har suka ce to sai su ga wanda zai raba su da makamansu. Yau an wayi gari sun fara aika-aikar da suke yi yanzu.
A farko-farkon watan da ya shude matsalar tsaron ya dawo Danya shar.
Madadin yadda munka ga ka nuna da gaske kake yi hanyar ziyartar duk wani mai ruwa da tsaki ta fuskar tsaro, musamman babban hafsan sojan sama da Shugaba Muhammadu Buhari da ma zaman da kuka yi da duk wasu sanatoci da ‘yan majalisar tarayya, domin ganin cewa wannan matsalar ta kau, har kuka tura jami’an tsaro a dazukkan. kun yi kokarin dora al’ummar da matasansu ba su riga sun rike makamai ba, ta yadda ba za su yi sha’awar rike makaman ba.
Amma sai dai kash! Sai ka dauki matakin tarwatsa wadanda a can baya ba su tarwatse ba. Ma’ana tayar da tashoshin mota na duk wani gari da ke da tasha fiye da daya, musamman a garin Gusau da garin Mafara.
Anya kuwa mai girma gwamna, ka tauna kafin ka furzar?
Da haka nike rokon Allah ya sa wannan kira namu ya kai ga kunnuwan da muka yi domin su.
Ya Allah wannan matsalar da ta yi wa Jihar Zamfara katutu, Allah ka yi mana katangar karfe da ita. Ya Allah ka daukaki Jihar Zamfara da Najeriya kwata.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau, shi ne, Jami’in Hulda Da Jama’a na kungiyar Muryar Talaka Ta kasa reshen Jihar Zamfara) 08069807496 [email protected]