Budaddiyar wasika zuwa ga matasa
Hakika matasa su ne kashin bayan ci gaban kowace al’umma, amma abin takaici shi ne, yadda tarin matsaloli suka yi wa rayuwar matasan katutu, wanda hakan ke haifar da mummmunan sakamako ga rayuwarsu da ci gaban al’umma baki daya. Tabbas matasa nagari na da gaggarumar gudunmuwar da ya kamata su ba da wurin ci gaban […]
Hakika matasa su ne kashin bayan ci gaban kowace al’umma, amma abin takaici shi ne, yadda tarin matsaloli suka yi wa rayuwar matasan katutu, wanda hakan ke haifar da mummmunan sakamako ga rayuwarsu da ci gaban al’umma baki daya. Tabbas matasa nagari na da gaggarumar gudunmuwar da ya kamata su ba da wurin ci gaban al’umma da ma ci gaban kasa baki daya, amma abin takaici, shi ne, yadda wasu ’yan uwana matasa ke canja yadda ya kamata su tafiyar da rayuwarsu cikin tsari, ta hanyar daukar wasu halaye da ba su dace da rayuwarmu ba, ba su dace da al’adarmu ba, kazalika ba su dace da addininmu ba. Ga kadan daga cikin halayen da wasu ’yan uwana matasa ke dauka;
1. Jahilci: Hakika matsalar jahilci cikin al’umma babbar matsala ce da ke hana kowane irin ci gaba a cikin al’umma ba wai ga matasa ba kadai, amma ta fi yin illa ga matasa saboda su ne kashin bayan ci gaban kowace al’umma kuma matasan su ne shugabanin gobe, amma yanzu ba kowane matashi ke kokarin neman ilimin addini ba, balle na zamani. Haka zalika gwammati na ba da gudunmuwa wurin wannan matsalar, ta fuskar kasa sauke nauyin da ke kanta na al’ummar da take jagoranta.
2. Shaye-shaye: Matsalar shaye-shaye matsala ce da ta dade tana ci wa al’umma tuwo a kwarya saboda tana haifar da mummunan sakamako ga rayuwar matasa da ma al’umma baki daya. Hakika matsalar shaye-shaye matsala ce da ke bukatar taimakon gaugawa wurin magance ta saboda ta saba wa rayuwarmu, lafiyarmu, mutuncinmu, al’adarmu da ma addininmu. Haka zalika gwamnati na da gudunmawar da za ta ba da wurin magance wannan matsala ta fuskar hana shigowa da duk wani abin da yake gurbatacce ko mai sa maye da kuma kamawa tare da hukunta masu fasa kwaurin miyagun kwayoyi.
3. Bangar siyasa: Siyasa wata muhimmiyar aba ce a rayuwar al’umma wadda ta hanyarta ne al’umma ke zaben shugabannin da suke so su jagorance su, to amma a halin yanzu siyasar kasarmu na dauke da tarin matsalolin da suka yi mata katutu, kuma suka hana ta ci gaba. Tabbas lokutan baya ’yan siyasa na amfani da matasa, tare da ba su kayan maye don su yi musu bangar siyasa da magudin zabe da sauransu. Kuma abin takaici ’yan siyasar kan watsar da matasan a lokacin da suka biya bukatarsu, ba tare da matasan sun amfana da komai ba.
4. Rashin aikin yi: Matsalar rashin aikin yi babbar matsala ce da ta zama gagarabadau ga mahukuntan Najeriya, kuma aka dade ana fama da ita kuma ake neman maganinta amma abin ya faskara, musamman gwamnatocin baya sun sha alwashin kawar da wannan matsala amma abin ya zama fada ce ba cikawa. A nasu bangaren ’yan uwana matasa na zaman kashe wando ba tare da yunkurin sama wa kansu aikin yi ko sana’ar yi ba sai dogaro ga gwamnati ta ba su aikin yi.
A karshe, ina kira ga ’yan uwana matasa su farka daga dogon barcin da suke yi, su gane akwai tarin matsaloli da suka yi wa rayuwarsu tarnaki, kuma suka hana su ci gaba. Don haka dole su tashi tsaye, su yaki duk wani mummunan hali, domin ci gaban rayuwarsu. Haka zalika ina kira ga gwamnati ta tashe tsaye don tallafa wa matasa. Su kuma ’yan siyasa masu mummunan dabi’ar lalata tarbiyyar matasa, ta hanyar ba su kayan maye da saka su cikin bangar siyasa su ji tsoron Allah su daina haka. Allah Ya sa wannan kira ya kai inda ya dace, amin.
Adamu Aliyu Amo, Katsina.
Sakataren kungiyar Muryar Jama’a Reshen Jihar Katsina. 0909 730 0909 [email protected]
A hukunta awakin da suka cinye mana doya
Daga Khaleel Nasir
Ba na manta wata rana, lokacin ina firamare. Bayan an tashe mu daga makaranta, maimakon mu nufi gida sai muka dunguma zuwa wani rafi yin wanka. Ban dawo gida ba sai wajen karfe biyar na yamma. Ga yunwa, ga gajiya ga fargabar rashin dawowata da wuri. Duk wannan ma da dan sauki idan ba a gane kurme muka je rafi ba, musamman ma babana!
kanena na fara cin karo tare da tambayata ina ka je ake ta nemanka?
Yau za ka sha duka wajen Baba! Ya kyalkyace da dariya, ya ce kuma akuya ta cinye abincinka! Na harare shi na wuce.
Lokacin da Baba ya titsiye ni da tambayoyi, ya tabbatar da rashin gaskiyata, sai ya yi min wata mazga a keya, na yi taga-taga, ashe akuyar da ta cinye min abinci na gidan, ta yi zaton kama ta zan yi ta mike a guje, ni ma sai na bi ta kofar gida da duka. Abin ya ba kowa dariya.
Don haka na fi kowa sanin rashin mutuncin akuya idan ta samu abincinka.Saboda haka nake kira da a yi saurin hukunta duk awakin da suka cinye mana doya. Khaleel Nasir Kiru, 07069191677,
imel: [email protected]