Budaddiyar wasika zuwa ga Ministan Tsaro
Zuwa ga Ministan Tsaro. Assalamu alaikum Mai girma Minista, bayan gaisuwa, ina fata kana cikin koshin lafiya. Ina da yakinin wannan rubutu nawa zai isa gare ka. Don haka ina fata za ka yi masa karatun ta-natsu. Da farko kafin kai an yi Ministan Tsaro dan Jihar Zamfara a baya-bayan nan wato Janar Aliyu Muhammad […]
Zuwa ga Ministan Tsaro.
Assalamu alaikum Mai girma Minista, bayan gaisuwa, ina fata kana cikin koshin lafiya.
Ina da yakinin wannan rubutu nawa zai isa gare ka. Don haka ina fata za ka yi masa karatun ta-natsu.
Da farko kafin kai an yi Ministan Tsaro dan Jihar Zamfara a baya-bayan nan wato Janar Aliyu Muhammad Gusau, inda ake zargin cewa Janar Ali Gusau bai yi wani abin kirki ga al’ummar Jihar Zamfara a zahirance kamar yadda kai ka yi ta wata fuskar ba. Kuma ko bayan ba ka za mu ga wani abu da za mu tuna da kai. Domin baya ga makarantun sakandare na soji da ka kawo Jihar Zamfara da barikin soja na dindindin biyu da a lokacinka suka samu matsuguni a garin Gusau. Wadannan kurum abin a yaba ne, na ayyukan da ka yi kokari a lokacinka suka shigo Zamfara.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba a tarihin Jihar Zamfara ba a taba lokacin da aka wulakanta rayuwar dan Adam aka yi kisan kiyashi, kamar lokacin da kake Ministan Tsaro ba, hasali ma a yanzu da nake wannan rubutu a Jihar Zamfara ba inda ake mummunan kisan mutane kamar yankin da ka fito da ke dauke da kananan hukumomin Birnin Magaji (karamar hukumarka) da Kauran Namoda da Shinkafi da kuma Zurmi. Wadannan kananan hukumomin babu wani gari daya da mazauna cikinsa suke kwana da idonsu rufe. Hatta karamar hukumar da ka fito a cikin garin da gobe kana iya zama Sarkin garin wato Birnin Magaji, zaman lafiyar al’ummar garin shi ne kullum ’yan sa-kai su kewaye shi da bindigogi kirar gida, su kwana suna ruwan wuta. In ba haka ba wallahi sai ’yan ta’adda sun wargaza garin kamar yadda na gani da idona lokacin da na yi aikin zaben bana. Kasa da kilomita daya da Birnin Magaji yanzu haka mutum bai iya zuwa in dai yana son ya rayu tare daiyalansa, in dare ya yi. Yau da nake wannan rubutu wato 12-4-2019 a Karamar Hukumar Birnin Magaji duniya ta ji yadda wani mazaunin karamar hukumar yake shaida wa sashin Hausa na BBC a shirinsu na safe cewa, an kashe mutum 32, inda ya tabbatar da cewa, a kauyukansu kwata-kwata babu jami’in tsaro, kuma duk masifar da suke ciki ba a taba kawo masu jami’an tsaro ba. Tare da bayyana cewa, yau (ranar da yake magana) da take Juma’a ba za su yi Sallar Juma’a a masallacin garin ba.
Hakan na nuna irin masifar da al’ummar suke ciki, wanda mu al’ummar Jihar Zamfara mun dade muna mamaki duk da tsatsonmu ne Ministan Tsaron Najeriya baki daya. Muna cikin masifa, ba wani takamaiman matakin tsaro da gwamnatocinmu tun daga ta jiha da ta tarayya suke dauka don dakatar da kisan kiyashin da ake yi mana.
Kwatsam! Sai muka ji ka fito karara kana zargin da hannun wadansu sarakuna a hura wutar kai hare-hare da kisan jama’a da kuma satar mutane domin karbar kudin fansa da suka zama ruwan dare a Jihar Zamfara.
Hakika mun dade muna mamakin wannan maganar daga gare ka. Domin tun shekarun baya mu mazauna Jihar Zamfara mun dade muna zargin cewa, akwai hannun wadansu sarakunan gargajiyar jihar, kuma ita kanta gwamnantin Jihar Zamfara, duk da ba ta taba daya daga cikin manyan sarakunan jihar ba, amma ta taba uwayen kasa da aka samu da hannu dumu-dumu a cikin wannan matsalar duk su kansu har yanzu ba a yanke masu hukunci a kan aika-aikar da ake zargin sun aikata ba.
Ya mai girma Minista! Babban abin da ya ba mu mamaki da kai shi ne; matsayinka na gogaggen jami’in tsaron da ya yi aikin samar da tsaro har ya kai matsayi Janar a soja kafin ya yi ritaya, wanda saboda gogewarka ce a harkar tsaro, ya sa Shugaba Buhari ya damka maka mukamin Ministan Tsaro, mukami mai girma da daukaka ta fuskar tsaro a kasarmu, amma abin mamaki a wayi gari wai kai ne ke fitowa ka fada wa duniya kana zargin wadansu da hannu wajen ta-da-zaune-tsaye. Ya mai girma Minista! Na tabbatar kana da dalilin da ya sa ka fadi waccan maganar, domin duk wani tsaro da asirin kasar nan yana hannunku. In kuwa haka ne ba Sarki daya ko mai sarautar gargajiya da yake da rigar kariya, kamar ta Gwamna ko Mataimakinsa ko Shugaban Kasa ko Mataimakinsa. Idan kuwa haka ne tmene ne ranar dukkan hukumomin tsaron Najeriya da ba za su yi aiki kan wadanda ake zargin suna da hannu wajen sanyawa ana yi wa al’ummar da ba su ji ba su gani ba kisan kiyashi?
A ranar Alhamis 11-4-2019 Majalisar Sarakunan Jihar ta fito ta barrranta kanta kan wannan zargi da kake yi wa mambobinta, inda ta nemi ka fito ka bayyana sunayen wadanda ke da hannu a kisan da ake yi a Jihar Zamfara. Don haka muna kira da babbar murya ku dauki mataki kwakkwara ga wadanda ake zargi da hannu a wannan aika-aikar. Muddin ba ku yi haka ba, to hakan zai nuna cewa ku kanku kuna da hannun a kisan da ake yi mana. Kasancewar ku ne masu hurumi na karshe a Najeriya na daukar mataki a kan masu ta da kayar baya, amma a wayi gari kun san masu ta-da-zaunen-tsaye a ce kun zura idanu.
Mai girma Minista! Yau da na ke wannan rubutun saura kwana 47 zangon mulkinku na farko da kake cikin Majalisar Ministoci ya kare. Ba ka da tabbaci za ka koma a matsayin Minista duk da gwamnatinku ce za ta koma in har an sake komawa da kai ba ka da tabbacin za ka koma Ministan Tsaron da kake da damar taimakon jiharka, a kan wannan masifa da ta riske mu.
Don haka muna fatan za ka yi amfani da wannan damar ta karfin fada-a-jin da kake da shi wajen tabbatar da an hukunta sarakunan da ka ce suna da hannu da ma sauran duk wani mai hannu a cikin wannan muguwar aika-aikar. Ruwa ba ya tsami banza dole akwai masu amfana da wannan kisan kiyashin da ake yi mana, kuma dole akwai masu daukar nauyinsu.
Don haka mun zura ido mu ga matakin da kuke dauka, a kan wadannan sarakuna da kuke zargin suna da laifi.
Daga karshe muna rokon Allah Ya sa kukanmu ya kai ga kunnuwan wanda muka yi dominsa, Ya kuma ba shi ikon share mana hawayenmu.
Ya Allah muna rokonKa kada Ka kama mu da laifin da wadansu wawaye daga cikinmu suka yi maKa. Allah Ka ji tausayinmu Ka kawo mana zaman lafiya mai dorewa a Jihar Zamfara da kasarmu Najeriya baki daya. Allah Ya kare jami’an tsaronmu duk inda suke ka ba su nasara wajen murkushe ’yan ta’addan da suke ci gaba da cin karensu babu babbaka.
Daga Abdulmalik Sa’idu Mai Burodi Tashar Bagu Gusau.
Jami’in Hulda da Jama’a na Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa Reshen Jihar Zamfara.
Za a iya samunsa ta tarho: 08069807496.