Budaddiyar wasika zuwa ga Muhammadu Buhari

Gaisuwa da fatan Alkhairi, Girmamawa, Jinjinawa da fatan Allah ya ida nufi. Ya mai girma Janaral Muhammadu  Buhari. Masu girma shugabannin jam’iyyar Adawa, da yawan al’ummar Najeriya sun kasance cikin  farin cikin lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC  da Buhari  yayi. Hakan tasa da dama muke ganin kamar Buharin ya  lashe babban zabe […]

Budaddiyar wasika zuwa ga Muhammadu Buhari
Budaddiyar wasika zuwa ga Muhammadu Buhari

Gaisuwa da fatan Alkhairi, Girmamawa, Jinjinawa da fatan Allah ya ida nufi. Ya mai girma Janaral Muhammadu  Buhari. Masu girma shugabannin jam’iyyar Adawa, da yawan al’ummar Najeriya sun kasance cikin  farin cikin lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC  da Buhari  yayi. Hakan tasa da dama muke ganin kamar Buharin ya  lashe babban zabe na kasa ne, har ta kai ga mun fara yima junan mu murnar samun canjin da muke ta addu’ar Allah ya kawo mana.
Wasu ma har sun fara kasafta irin tsarin da kasarmu za ta koma na tsaftaceta daga  manyan matsalolin da suka dabaibaye kasar mu, da suka hada da matsalar tsaro da fatara da talauci da cututtuka da rashin wadatattun likitoci a asibitoci da kwararrun malaman Asibiti, jahilci  da nakasa ilimi, zaman banza da gurbata tarbiyyar matasa,  rashin aikin yi ga matasa, da tada hankalin al’umma da kashe al’umma ba tare da daukar matakin hanawa haka ba, da asarar dukiyoyi. Sannan ga rashin iya tafiyar da mulki ta hanyar nuna bambancin addini da kabilanci.
‘Yan Najeriya mun kasance cikin farin ciki, ganin dukkan waddancan matsalolin karshen su ya zo a dalilin ganin wanda muke yi wa kyakkyawan tunanin kwararre ne a fagen kawar da matsalolin da suka addabi Najeriya zai hau kan mulki a 2015.
Amma kash! Tun kafin tafiya ta yi nisa sai aka jiyo  Janaral Buhari na fadin wai ba za a yi masa adalci a zaben 2015 ba, ya ce za a yi masa magudi. Haba maigida! Maganar ba za a yi maka adalci ko za a yi maka
magudi duk ba ta taso ba. Nasara kai ke da ita, abin da kawai ya rage, ka ci gaba da kara wa dimbin magoya baya kwarin gwuiwa, ka rika tabbatar mana da samun nasara a zaben 2015, kamar yadda alkiblar siyasar bana ta nuna.
Lokaci ya yi da kai da shugabannin jam’iyyar APC da ma masu kishin ci gaban kasar mu, su tashi tsaye wajen wayar da kan al’umma, kan yadda za akai ga samun nasara. Ya kamata al’umma su kare kuri’un su. Ta yaya za a tabbatar da an bai wa al’umma abin da suka zaba, ba tare da an canza masu kamar yadda aka saba yi a baya ba. Ya kamata Janar Buhari  ya san cewa dukkan hakkokin waddanda za su fita don zaben shi a babban zabbe  alhakin kare musu mutuncin su ya rataya ne a wuyan Buharin  da shugabannin jam’iyyar APC, dole a kare musu mutuncin su da kuri’un su da lafiyar su da rayukan su. Ke nan zama guri daya bai dace da Janar Buhari da Shugabannin jam’iyyar APC ba.
Lokaci ne wanda za a tashi a shiga lungu da sako don fadakar da al’umma. Dole a yi amfani da kafafen yada labarai na gida da na waje, don wayar da kan al’umma. Ba karamin aiki ba ne karbar mulki a hannu wanda bai son bayarwa, kullun hana idanuwan su barci suke yi, tunanin su ta yaya za su ci gaba da mulki
(duk kuwa da sun san al’umma ba su bukatar ci gaba da mulkin su), amma hakan bai hana su hana idanuwan su barci ba, ba su rabuwa da tarurruka da farfaganda da yada manufofin su a manya da kananan kafafen yada labarai.
Amma jam’iyyar APC gani take kwace goriba hannun kuturu ba wani aiki ba ne, hakan yasa ta yi kwanciyar ta, ta kama barci har da munshari. Ta kyale wadanda al’umma ba su san su na ta yakin neman a zabe su, ta hanyar amfani da talaucin da aka kakaba wa al’ummar kasar mu, ana ba su dan abin da bai taka kara ya karya ba, ana sayen kuri’un su.
A karshe ina kira da babbar murya ga Buhari da shugabannin jam’iyya da masu kishin ci gaban kasar mu, da mu farka daga nannauyan barcin da muke yi, mu san aiki ne babba a gare mu, Allah ya ba mu shugaba mai adalci, wanda zai magance mana matsalolin kasar mu amin.
Kabir Sakaina Layin ‘Yangoro Malumfashi. 08095968366

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi