Budaddiyar wasika zuwa ga Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato
Shahararren marubuci BISHOP MATTHEW HASSAN KUKAH ya rubuta wata budaddiyar wasika ga marigayi Sardaunan Sakkwato, Alhaji Sa Ahmadu Bello a daidai lokacin da ya cika shekara 50 cur da barin duniyar nan, a sakamon kisan gilla da wasu karkatattun sojoji suka yi masa a ranar 15 ga Janairun 1966. Muhimmancin wasikar ne ya sanya shi […]
Shahararren marubuci BISHOP MATTHEW HASSAN KUKAH ya rubuta wata budaddiyar wasika ga marigayi Sardaunan Sakkwato, Alhaji Sa Ahmadu Bello a daidai lokacin da ya cika shekara 50 cur da barin duniyar nan, a sakamon kisan gilla da wasu karkatattun sojoji suka yi masa a ranar 15 ga Janairun 1966. Muhimmancin wasikar ne ya sanya shi ma shahararren marubuci, AUWAL G. dANBARNO (08064595353) da Shamsiyya Idris Kaduna suka fassara ta zuwa Hausa, mu kuma muka kawo muku ita, kamar haka:
Ban san irin lakabin da ya kamata na kira ka da shi ba, musamman a yanzu da lakabin “Ranka ya dade” bai da amfani a gare ka, tun da ka riga mu gidan gaskiya. Duk da haka, kasantuwar wannan muhimmiyar shekara ce, na yanke shawarar rubuta wasiku biyu; daya zuwa gare ka, dayar kuma ga Sa Abubakar Tafawa balewa. Amma zan fara da kai saboda wasu dalilai. Wadannan wasiku su ne hanya mafi dacewa na hasashen tattaunawa da ku. A bangare guda, zan ba ku sakamakon abin da kuka bari bayanku. Abin da magadanku suka yi da jarin da kuka zuba, sannan da yadda suka kasafta gadonmu ga zuri’arsu.
A wani bangaren, ina ji na kamar jika ne da ke kai karar kawunsa ga kakansa, saboda haka ka yi hakuri da ni. Ina tunanin ya zama dole ne, don in muka ci gaba a haka, ina da tabbacin labarinku zai zama shafa labari a kunnen jikokin jikokinku. Abin ban takaici ma, a yanzu da yawa sun mayar da sunayenku wani tikitin samun na abinci. Ina kuma jin tsoron wasu daga cikin dabi’un da ka rayu, ka kuma mutu a kai suna neman gushewa. Wani Malami Bature kuma masoyin Arewacin Najeriya; Farfesa John Paden ne kadai ya rubuta cikakken tarihinka. Wani zai yi tunanin ya zuwa yau, wadanda ke da’awar sunanka sun samar da wata kujera mai taken ilimin sardauna, a daya daga cikin Jami’o’in Arewa. Amma ina, ga dukkan alamu wasu abubuwa mafi muhimmanci a gare su sun dauke hankulansu.
Dalilin wanna wasika na biyu shi ne, kasancewata mazaunin garinka na haihuwa a yanzu (Sakkwato). Wajen da nake matsayin Bishof na al’ummar Cocin Katolika. Za ka yi farin ciki da jin cewa, har yanzu Sakkwato gari ne mai matukar zaman lafiya. A bangaren ci gaba kuwa, ba na tsammanin ba za ka iya bata ba, a mafi yawancin unguwannin.
Na ziyarci kauyen Rabah, wajen da aka haife ka, na kuma ga gidanka a nan Sakkwato. Na gaza yarda, sai dai hakan ya tuna min da yanayin rayuwar daya daga cikin gwarazana, takwaranka na wancan zamanin, Julius Nyerere na kasar Tanzaniya, wanda gidansa ke da matsuguni a titin Dares Salaam. Tun da kowa halittar Allah ne, ina da tabbacin kun hadu da juna.
Gare mu masu tasowa, a matsayin ’ya’ya a karamin kauyenmu, garin Sakkwato ya samu matsuguni a zukatanmu ne kawai saboda sadaukantakarka da jajircewarka da ya kusanta mu da garin. Duk da haka idan na waiwayi baya, ina kallon ba ziyartar Sakkwato kadai na yi ba, na kasance ne halastaccen dan wannan jihar. Ina sane na tsaya a kauyen Rabah, don kawai in shaki iskar mahaifarka wajen da ka taso, wajen da kuma mahaifinka ya rike sarautar dagacin kauyen.
Shekaru hamsin ke nan da aka yi maku kisan gilla, kai da jarumar matarka. Lallai da a ce ta ba da hakuri ko ta boye, ta yiwu makisan naku su sauya tunani. Duk da haka, a cikin kauna ta gaskiya, so da kuma sadaukarwa, ta ba da kanta domin kare abin da ta fi so a lokaci mafi muhimmanci. A cikin wannan runguma da kuka dawwama, wanda ta zama garkuwa, aka aika da ku barzahu. Ina fatan dukkanku kuna Aljannah cikin farin ciki.
Na yi girman da ya kamata a ce na san ka, amma ban taba samun damar ganinka ba, kamar sauran miliyoyin kananan yaran Arewacin Najeriya. Mun samu labaranka, kuma hotunanka kadai muke da su a zukatanmu. Hakika mun sha almara kala-kala a kan kai da Malam Aminu Kano. A dan karamin hangen mu, sunanka ya fi tsorata mu, amma na Aminu Kano ya fi faranta mana. Mun fi kaunar sunan Aminu kano. Tun farko mun taso cikin fargaba da tsoron Sarakunan Gargajiya, muna kallon su a matsayin azzalumai, masu karbar haraji. Muna tuna irin bakin cikin da ziyararsu ke haifarwa, musamman a gidajen talakawan kawunnanmu na kauyuka, idan sun zo karbar harajinsu. Amma da muka samu labarin Aminu bai goyi bayan haraji ba, mun so shi saboda haraji barazana ne ga kudin makarantunmu.
Matsayinka a tarihi tabbatacce ne, amma har yanzu akwai abubuwa masu rikitarwa game da abin da ka bari. Mun ji kuma mun karanta cewa kai masoyin Arewa da mutanenta ne, ba tare da kallon bambacin addinansu ba. Amma mawakan fasaha sun bar mana alamun yabo da labaran girma da dattakunka. Wannan ba waje ne na jayayya a kan ayyukanka ba. Ka gina harsashi don ganin mu ’ya’yanka ba mu fuskanci kila-wa-kalan rayuwa ba a gaba. Amma a yau, da yawa daga cikin ’ya’yan naka sun zama marayu saboda yankin ya zama wani gawurtaccen gidan marayu.
’Ya’yanmu sun cika gari da barace-barace, wasu da suka dan samu karatun ba aikin yi, kuma babu makoma, iyayensu ba su da abin yi kuma wadanda suka yi aikin sai mutuwa suke ba fansho. Noma ya zama sana’ar rashin aikin yi. Za ka zub da hawaye in ka ga inda muke a yanzu. Son zuciya ya cinye mu, sojojinmu sun baro filin daga saboda ba mai yi musu jagora. Babu hanyar bi balle wurin zuwa, haka zalika mafi yawan mutane sun rasa kuzarin tunkarar kowanne irin kalubale.