Budaddiyar wasika zuwa ga Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato (2)
Shahararren marubuci BISHOP MATTHEW HASSAN KUKAH ya rubuta wata budaddiyar wasika ga marigayi Sardaunan Sakkwato, Alhaji Sa Ahmadu Bello a daidai lokacin da ya cika shekara 50 cur da barin duniyar nan, a sakamon kisan gilla da wasu karkatattun sojoji suka yi masa a ranar 15 ga Janairun 1966. Muhimmancin wasikar ne ya sanya shi […]
Shahararren marubuci BISHOP MATTHEW HASSAN KUKAH ya rubuta wata budaddiyar wasika ga marigayi Sardaunan Sakkwato, Alhaji Sa Ahmadu Bello a daidai lokacin da ya cika shekara 50 cur da barin duniyar nan, a sakamon kisan gilla da wasu karkatattun sojoji suka yi masa a ranar 15 ga Janairun 1966. Muhimmancin wasikar ne ya sanya shi ma shahararren marubuci, AUWAL G. DANBARNO (08064595353) da Shamsiyya Idris Kaduna suka fassara ta zuwa Hausa, mu kuma muka kawo muku ita, kamar haka:
A lokacin da babu kimiyya da fasaha, babu ayyuka a kasa, ka dasa ayyuka tun daga tushe. Ka gina manyan makarantu, irin su Jami’ar Ahmadu Bello, Makarantar Koyar da Tsarin Gudanarwa, Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Kaduna, kwalejojin ilimi, makarantun sakandare da sauransu. Ka kafa Cibiyar Ci Gaban Arewacin Najeriya, Kamfanin Zuba Jari na Arewacin Najeriya, filin wasa na Ahmadu Bello, Ma’aikatar Watsa Labarai ta Najeriya, Kamfanin jaridun New Nigeria. Masaku irin su Masakar Kaduna, Masakar Zamfara, Masana’antar Siminti ta Arewacin Najeriya, Masana’antar Mai ta Arewa, masaukin baki na Hamdala, Dalar Gyada ta Kano, masaukin baki na Central Kano, Bankin Arewa, da sauransu da dama.
Shin da wadannan ayyuka abin alfahari, a ce duk da ko ’yar Arewacin Najeriya ba za su yi tinkaho kamar ’ya’yan sarakuna ba? Sai dai kash! A yau magadanku sun kashe sun kuma binne duk wadannan ma’aikatu ta hanyar rashin dabarun tafiyar da tattalin ma’akatun. Ganinsu kawai ake a matsayin guraben gado kuma a yau maimakon tafiyar da su, magadan naku ne suka yi tsayuwar daka don yin jana’izarsu. Abin da ya yi saura a yanzu kawai gawarwakinsu ne.
A yau, muna waiwayen akidun da suka shiryar da kai ne. Duk da dan gazawa, ka yi iyakar kokarinka don ganin ba a bar Arewa a baya ba. A kokarin yin hakan, ka daura damarar daura wahalallen ginshiki mai matukar wuya. Ka yi kokarin hade kan jama’a masu bambancin tarihi, al’adu da akidu. Amma abin bakin ciki, mutanen ba su rike wani makami kamar kimiyya da ilimi ba don gina birane. Duk da haka shirinka na yaki da jahilci ya taimaki talakawa manoma da dama wajen samun ilmi da wayewa.
Bisa dalilai da dama, Arewa na cikin hargitsi a yau. Hargitsin, sakamako ne na cutar da ta kama kasar, bayan an yi maku kisan gilla kai da sauran ’yan kasa nagari. A hankali muka fada komar Yakin Basasa. A yau muna da jihohi talatin da shida kuma tsohuwar Jihar Arewa na da jihohi sha tara. Za ka yi farin cikin sanin kusan dukkan gwamnonin Arewar an haife su ne kusan lokacin da aka kashe ka. Ka ga ke nan matasa ne masu jini a jika. Don Allah ka yi masu addu’ar samun tsira daga munanan kura-kuran iyayensu, su kuma gina garin da kowa zai ji dadin kasancewa a ciki. Sabanin iyaye da kawunnansu, sun samu ilimin jami’a kuma sun yi aiki a wuraren da ke da al’ummu masu tarin yawa. Gwamnanmu na Sakkwato, an haife shi ne kwanaki kadan gabanin mutuwarka, kuma da taimako da goyon bayan ’yan Kudu ya rike matsayin Shugaban Majalisar Dattijai ta Tarayya. Wannan kuwa ya sha bamban da lokacinku da dangantaka take da tsaurin gaske. Za ka yi mamakin jin cewa, wadanda ka yi wa lakabi da Scallywags a garin Legas, wadannan da suka yi maka tawaye a kan takaddamar bayar da mulkin kai a shekarar 1956, su ne suka mara wa Janar Buhari baya, dan Asalin garin Daura, wanda a yau shi ne Shugaban kasarmu. Don Allah ka yi mana addu’ar samun al’umma ta gari.
Hankalinka zai yi matukar tashi, idan ka ga yadda Arewa ta zama a yau. Boko Haram, wani gungun bata gari, makasa, sun karbi ragamar Arewa, sun mayar da ita yanki mara amfani. A yau an rasa dubunnan rayuka, miliyoyin jama’a na rabe a sansanonin gudun hijira. An yi hasarar rayukan dubannin mata da kananan yara ba tare da sun yi laifi ba. Babbar alamar Arewa shi ne sansanin gudun hijira mai cike da radadi. An halaka dubunnan ’yan matanmu, wasu an keta haddinsu ta hanyar fyade da auren dole. An yi garkuwa da ’yan matan wani kauye, Chibok sama da dari biyu, har ila yau ba a san makomarsu ba, fiye da kwana dari shida ke nan, ba amo ba labari. Al’ummar Arewa sun zuba ido ga Gwamnatin Tarayya ne kadai, sun ki daukar hakkin abin da yake a bayyane, ya rataya a kansu ne, ko sakamakon sakacinmu da rarrabuwar kawunanmu.
An rika tafka rashin gaskiya a gidan da ka gina tun farko. Tun daga wannan lokacin rashin gaskiya ya ci gaba da yawaita a zukatan mutanen, kuma rarrabuwar kawuna ya kara yawaita. Mun zubar da jini mai yawa a Arewa, za ka yi mamakin yawan kaburburan da ke Arewa a yanzu.
Zan bar ka ka huta amma a karshe, ga wani dan tsegumi: Jikanka Hassan, shi ne Magajin Garin Sakkwato na yanzu. Ba na tsammanin zai iya wasan kwallon Fibes Kamar yadda ka yi, saboda yana da girman jiki fiye da kai. Za ka yi alfahari da shi. Haka zalika wannan karamin hazikin yaron, wanda ya samu takardar shedar kammala makarantar Kabba, wanda ka dauki nauyin karatunsa, bai zama wani abu a Gwannatin Arewa ba, sai dai ya zama gawurtaccen Malamin Coci. Za ka yi alfahari jin cewa a yanzu shi ne shugaban malamai na Cocin Katolika, zai kuma iya zama Shugaban Kiristocin Duniya baki daya! Don Allah ka fada wa Firaminista ya yi hakuri, ta shi wasikar sai mako mai zuwa. A yanzu dai muna kara barar addu’arka, Ubangiji Ya kara kare mu, Ya shiryar da mu, Ya yi mana gam da katar da irin halinku, kai da sauran takwarorinka mazan kwarai. Ka mika sakon gaisuwata ga Kanal Pam, shi da mai dakinsa mamana Elizabeth, tare da sauran maza da matan kwarai da suka rasa rayukansu tare da kai. Ka fada mata, don Allah ta nemi Jostis Oputa.