Bude iyaka: Ba mu gani a kasa ba —Mazauna Seme

Al’amura sun ci gaba da kasancewa a daddafe tamkar ba a bude iyakar ba

Bude iyaka: Ba mu gani a kasa ba —Mazauna Seme

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin a bude wasu daga cikin iyakokin kasar nan ciki har da iyakar Najeriya da Jamhuriyyar Benin da ke Seme a Jihar Legas.

Sai dai da Aminiya ta ziyarci iyakar ta Seme don ganin yadda al’amura ke gudana ta iske cincirindon mutane ana hada-hada a iyakar, amma har zuwa lokacin babu alamar ana shiga ko fita da kayayyaki ta kan iyakar.

Wadansu daga cikin mazauna iyakar, sun shaida wa Aminiya cewa zuwa yanzu ba su gani a kasa ba, domin al’amura sun ci gaba da kasancewa a daddafe tamkar ba a bude iyakar ba.

Sun ce zuwa yanzu babu wani sauyi saboda rashin kankamar al’amura.

Malam Sa’id Abubakar wani direba da ke jigilar fasinjoji daga iyakar Seme zuwa Legas ya shaida wa Aminiya cewa har yanzu ba ta sauya zane ba, domin mutanen da ke shigowa Najeriya ta iyakar Seme na ci gaba da shigowa ne ta barauniyar hanya.

“Kuma jami’an tsaro na sane da wannan, babban takaicinmu mun kasa gane bambanci tsakanin aikin dan sanda da na jami’in shigida-fici, domin shinge ’yan sanda ya karu sosai

“Idan ka dauko fasinja sai su tsare ku, suna tambayar daga ina suke, ta ina suka shigo, sai su fake da cutar Kwarona su bata maka lokaci

“In fasinjojin sun ba su cin hanci sai su bari ku tafi, dama abin da suke nema ke nan, suna karbar daga Naira 5,000 zuwa sama,” inji shi.

Ya ce shingen ’yan sanda ya karu sosai kuma babu abin da suke sai karbar kudi daga matafiya, “Ko gero ko masara muka dauka wa ’yan kasuwa daga Najeriya a Alaba zuwa kan iyakar Seme sai mun ba Kwastam Naira 200 kowane buhu, daga baya ne suke kawar da kai

“Amma idan muka dauko kayan lantarki irin su talabijin komai takardunka sai ka ba su cin hanci,” inji shi.

Shin murna ya koma ciki?

Wata mai suna Ngozi da ke zaune iyakar Seme, ta bayyana farin cikinta game da yunkurin bude iyakar.

Ta ce fatarsu ita ce al’amura su daidaita a yankin kamar yadda suke a baya, sai dai ta ce har yanzu al’amura ba su fara daidaita ba, domin babu shigi-da-ficin kayayyaki.

Alhaji Zubairu Mele Abba Gana, mai lasisin fiton kayayyaki da ke zaune iyakar Seme, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan kasuwa masu fiton kaya suna cike da murna da farin cikin bude iyakar, domin wannan hanya ta fi musu saukin shigo da kaya.

“A baya da muka koma yin fito ta ruwa mun kasance cikin kunci da wahalhalu marasa misaltuwa.

“Kafin motarka ta kai gabar ruwa domin dauko kaya ba karamin jidali ba ne, haka nan idan ka je za ka dauki kayan a ce ba network, in kayanka suka kwana biyu a kasa a ci tararka, ka biya miliyoyin Naira babu sabo babu sassauci.

“Amma yanzu da aka bude iyakar mu halatattun ’yan kasuwa da gwamnati ta san da zamanmu za mu samu sauki, mu ci gaba da yin fito muna biyan haraji kasarmu ta samu ci gaba mu ma mu samu sa’ida,” inji shi.

Ya ce zuwa yanzu jami’an kula da shigi-da-fici a kan iyakar suna binciken masu ketarowa ko fita su tantance su, sai dai shigi-da-ficin kayayyaki bai kankama ba.

 “Fatarmu al’amura su kankama, masu fasakwauri kuma mahukunta su sanya ido a kansu, domin a dalilinsu ne ake daukar matakin da ke shafar mu ’yan kasuwa da gwamnati ta bai wa izinin shiga ko fita da kayayyaki,” inji shi.