Bude kasuwar shanun Borno ya fara inganta rayuwar ‘yan kasuwa

A karshen makon da ya gabata ne Hukumomi a Jihar Borno suka ayyana bude katafaren Kasuwar Shanun dake yankin karamar Hukumar Jere, wanda kuma ya kwashe sama da shekaru biyu da rufe ta sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram, wanda ya addabi Kasuwar da ma jihar baki daya. Kasuwar wacce ta shahara a Nahiyar Afirka saboda […]

Bude kasuwar shanun Borno ya fara inganta rayuwar ‘yan kasuwa

A karshen makon da ya gabata ne Hukumomi a Jihar Borno suka ayyana bude katafaren Kasuwar Shanun dake yankin karamar Hukumar Jere, wanda kuma ya kwashe sama da shekaru biyu da rufe ta sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram, wanda ya addabi Kasuwar da ma jihar baki daya.

Kasuwar wacce ta shahara a Nahiyar Afirka saboda hada-hadan kasuwancin Shanu a gida da wajen Najeriya, da suka hada da kasashen dake makwafta da Najeriya Nijar, Kamaru da  Chadi gami da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, in da kuma yake samar da kudaden shiga ga gwmnatin Jihar Borno da ma Tarayyar Najeriya.

Haka kuma kasuwar ta na da mambobi sama da mutane dubu 15, gabanin rufe kasuwar, amma a halin yanzu an yi rajistan mutane dubu 914. Malam Bunu Kachallah, yana daya daga cikin ‘yan kasuwar shanun kuma, inda ya nuna farin cikinsa dangane da yadda aka bude masu Kasuwar bayan rufe ta na tawon lokaci.

“A gakiya mu na murna da farin cikin bude wannan kasuwa, ba don komaiba sai don irin yadda rayuwarmu za ta farfado, domin kuwa a baya, bayan rufe kasuwar mun fuskanci matsanancin yanayin rayuwa kasancewar duk wasu abubuwan da muka mallaka sun kare, hatta shanun da muke da su sun kare har muka zo abinci yana gagararmu, alhalin kuma bayan ada da muke da shanu da dama muna kuma da jarin kudi sama da Naira Miliyan 50, amma sai muka koma ba mu da komai duk da yake dai Allah Ne Ya aiko mana da shi, duk da cewar ada din wannan kasuwa tamu cike ta ke makil da Boko Haram, mu na tare da su, amma ba zamu iya cewa komai ba, saboda mu na tsoron rayukanmu saboda akwai munafukai a cikinmu, to amma kaga da a aka rufe kasuwar sai kowa ya shiga taitayinsa aka tantance na kwarai da na banza,” in ji shi.

Sannan ya kara da cewa, “Domin a lokacin da aka rufe kasuwar ba wanda bai durkushe ba, kuma kowa a yanzu ya dandana kudarsa, kuma wadanda ba na kwarai ba an tankade su, to yanzu kasuwar ta dauki hanyar ci gaba, domin zamu ci gaba da ketarawa zuwa kasashen ketare don sayar da shanun, mukan kuma yi musayan ababen bukatun yau da kullum a tsakaninmu da kasashen da muke makwaftaka ko kuma da bangaren kudancin kasar nan, don haka yanzu harkoki za su koma mana kamar da, musamman idan muka samu goyon bayan jami’an tsaro da hukumomin da abin ya shafa, to kuma mu mun sha alwashin ba su hadin kai da goyon baya wajen ganin an yi waje rod da bata garin cikinmu tun da a yanzu bin akidar Boko Haram ya zama kauyenci.”

Shi ma Malam Hussaini Grema, ya nuna farin cikinsa da bude kasuwar domin ci gaban rayuwarsu da iyalansu, ya kara da cewar, ai wallahi muna godewa hukumomi saboda bude mana wannan kasuwa yanzu rayuwarmu za ta koma daidai, duk da cewar kasuwar za ta rika hada-hadan shi ne a cikin gida wato daga nan Arewa maso Gabashi har ya zuwa bangaren Kudanci, amma babu batun bude hanyar Dikwa zuwa Gamborun Ngala zuwa kuma kasashen Kamaru da Chadi saboda kasuwancin shanu sai nan gaba, amma duk da haka mu a nan zamu ci gaba da kasuwancinmu a cikin gida don muna daukan shanu daga nan ya zuwa Kudu, kuma muna daukan sama da Tireloli 20, to yanzu ko da tireloli uku zuwa biyar muka dauka ai kaga yana da kyau zai taimaka mana wajen bunkasa harkar rayuwarmu da na iyalanmu gami da wasu ‘yan uwanmu koma bayan da, da harkoki suka tsaya cak, amma yanzu mun sami daman gudanar da hada-hada kenan, muna godewa hukumomin da abin ya shafa da na gwamnti da jami’an tsaro, saboda tsayawa da suka yi na rufewa da bude wannan kasuwar mun gode Allah Ya saka da alkhari amin,” a cewarsa.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50