Bude Makarantu: Gwamnatin Tarayya ta yi wa jihohi gargadi
Kwamitin Yaki da COVID-19 na Fadar Shugaban Kasa ya gargadi jihohi game da shirinsu na bude makarantu da gidajen kallo da wuraren motsa jiki da sauran wuraren taruwar jama’a. Hakan na zuwa ne yayin da kwamitin ke kokawa bisa yadda ya ce ake wa dokokin kare yaduwar cutar COVID-19 hawan kawara a jihohi. Shugaba kwamitin […]
Kwamitin Yaki da COVID-19 na Fadar Shugaban Kasa ya gargadi jihohi game da shirinsu na bude makarantu da gidajen kallo da wuraren motsa jiki da sauran wuraren taruwar jama’a.
Hakan na zuwa ne yayin da kwamitin ke kokawa bisa yadda ya ce ake wa dokokin kare yaduwar cutar COVID-19 hawan kawara a jihohi.
Boss Mustapah ya kara da cewa zuwa yanzu ba a bin matakan kariya a wuraren taruwar jama’a. “Matsalar ta fi kamari a kasuwanni, da tashoshin mota da wasu wuraren ibada.
- Gwamnati ta fitar ka’idoji shida na bude makarantu
- NCDC ta kora dalibai gida a Kuros Riba
- Bude makarantu: Muna duba yiwuwar karkasa azuzuwa — Gwamnati
“Gwamnatin Tarayya ta ayyana matakan kariya da ya kamata a kiyaye sannan ta bukaci gwamnatocin jihohi su tabbatar ana bin su. Don hakan ina yin tuni a kan wannan”, inji Boss Mustapha.
Ya ce akwai yiwuwar sake yin duba a kan daukacin matakan kariya da Gwamnatin Tarayya ta saukaka.
“Yadda ake karya dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi abu ne da ya kamata a mayar da hankali a kai, domin duk ka’idojin da aka ayyana an yi su ne domin kare lafiyar al’umma”, inji shi.