Bude makarantu: Malamai na koyon matakan kariya a Kebbi
Malaman makarantu guda 2,212 sun fara koyon hanyoyin karaiyda ga cutar COVID-19 bayan bude ajin karshe na makarantu a jihar Kebbi. Babbar Sakatariyar Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kebbi (SUBEB), Fatima Abubakar Udulu, ta bayyana haka yayin bude shirin horaswan a ranar Asabar. “Domin tabbatar da kariyar lafiyar dalibai da malamai daga COVID-19, SUBEB […]
Malaman makarantu guda 2,212 sun fara koyon hanyoyin karaiyda ga cutar COVID-19 bayan bude ajin karshe na makarantu a jihar Kebbi.
Babbar Sakatariyar Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kebbi (SUBEB), Fatima Abubakar Udulu, ta bayyana haka yayin bude shirin horaswan a ranar Asabar.
“Domin tabbatar da kariyar lafiyar dalibai da malamai daga COVID-19, SUBEB tare da kwamitin yaki da cutar na ba da horo ga shugabannnin makarantun firamare guda 1,901, shugabannin kananan sakandare 112, na manyan sakandare 115 da kuma masu lura da makarantun (supervisors) guda 84”, inji ta.
Ta ce ana ba su horon ne da hadin gwiwar kwamitin yaki da COVID-19 na Jihar, kuma shirin na kwana bakwai ya kunshi ba wa wasu manyan masu horaswa guda 15 da za su koyar da na kasa.
A jawabinsa, shugaban kwamitin yaki da cutar a Jihar Kebbi, Jafar Mohammed, ya ce manuar shirin shi ne tabbatar da bin matakan kariyar COVID-19 a tsakanin dalibai da malamai a dukkan makarantu.