Bude makarantu: Sai an kara matakan kariya —Malamai
Malamai sun bukaci a dauki karin matakan kariya kafin a sake bude makarantu bayan an rufe su sakamakon bullar cutar coronavirus a Najeriya. Kungiyar Malamai ta Najeriya (NUT) reshen Jihar Neja ta yi kiran tana mai yaba wa gwamnati game da neman shawarwarin masu ruwa da tsaki kan hanyoyin da za a bi domin sake […]
Malamai sun bukaci a dauki karin matakan kariya kafin a sake bude makarantu bayan an rufe su sakamakon bullar cutar coronavirus a Najeriya.
Kungiyar Malamai ta Najeriya (NUT) reshen Jihar Neja ta yi kiran tana mai yaba wa gwamnati game da neman shawarwarin masu ruwa da tsaki kan hanyoyin da za a bi domin sake bude makarantun cikin aminci.
Babban Mataimakin Babban Sakataren NUT, Labaran Garba ya ce, “Ba za mu yi gaggawar sake bude makarantu ba domin kada mu jefa mutane da yawa cikin hadarin yaduwar coronavirus.
“Malamai sun fi hadarin kamuwa domin su ne ke cikin kowane matakin sake bude makarantun, da suka hada da karbar dalibai da kuma koyar da su.
- Gwamnati ta fitar ka’idoji shida na bude makarantu
- Bude Makarantu: Gwamnatin Tarayya ta yi wa jihohi gargadi
- An ba wasu makarantu izinin yin jarabawa a Najeriya
“Muna bukatar karin matakan kariya, sannan duk abin da gwamnati za ta yi ta fara la’akari da malamai kafin komai”, inji Garba.
Ya yi jawabin ne yayin kaddamar da sabuwar sakatariyar da kungiyar ta gina a garin Minna na jihar Neja.
Idan za a iya tunawa Gwamnatin Tarayya ta ce ba za ta sake bude makarantu a fadin Najeriya ba, sai ta tabbatar da an dauki dukkan matakan kariya da suka dace.
Gwamnatin ta ce hakan zai yiwu ne idan har aka kai sadda take da tabbacin cewa dalibai a dukkan matakan ilimi na iya zuwa makaranta su dawo ba tare da yiwuwar su kamu da cutar ba.
Da take sanar da matakan kariyar da ta shardanta kafin lokacin bude makarantun, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta kuma ta shawarci shugabannin dukkan makarantu da su yi amfani da lokacin da makarantun ke kulle domin samar da dukkan kayan kariyan da ake bukata.