Bude Masallacin Jumu’a: Yadda mata suka tsere wa maza

Ranar Lahadin da ta gabata ce aka bude Masallacin Juma’a na farko da kismud Da’awa na Makaratar Nurul Huda da ke Abuja ya gina a kauyen Giri a Gwagwalada da ke Birnin Tarayya, Abuja. Wanda ya shugabanci taron Alhaji Musa Wakili, Wakilin Agomari na Giri, a jawabinsa ya tunatar da mahalarta taron bude masallacin muhimmancin […]

Bude Masallacin Jumu’a: Yadda mata suka tsere wa maza
Bude Masallacin Jumu’a: Yadda mata suka tsere wa maza

Ranar Lahadin da ta gabata ce aka bude Masallacin Juma’a na farko da kismud Da’awa na Makaratar Nurul Huda da ke Abuja ya gina a kauyen Giri a Gwagwalada da ke Birnin Tarayya, Abuja.
Wanda ya shugabanci taron Alhaji Musa Wakili, Wakilin Agomari na Giri, a jawabinsa ya tunatar da mahalarta taron bude masallacin muhimmancin neman ilimin addini, ya ce Manzon Allah (SAW) ya ce, “Wanda Allah Ya nufe shi da alheri sai Ya sanar da shi addini.” Daga nan sai ya yaba wa jagorar kismudu Da’awar kan kokari da jajircewarta wajen yada Musulunci da iliminsa a yankin.
A jawabin Shugabar Malama Halima Sa’eed ta yi bayanin yadda ta faro harkar ilimantarwa da da’awa a yankin inda ta ce: “Lokacin da na zo rukunin gidajen malaman Jami’ar Abuja da ke kusa da Giri a matsayin matar aure a 1992, na iske babu masallaci balle makarantar addini, don haka sai na yanke shawarar fara karantarwa a dakina da mata 11, daga nan aka fadada karantarwar zuwa masallacin Giri.”
Malama Halima Sa’eed ta  ce daga nan ne suka yanke shawarar kafa makarantar Nurul Huda wadda a yanzu haka ta samu nasarar gina makarantu biyar, yayin da ake ginin karin wasu biyu.
Ta ce bayan kafa Nurul Huda a 1993, ba su tsaya ga karantarwa kadai ba suna gudanar da ayyukan da suka hada da kira zuwa ga addini da bayar da tallafi inda a yanzu haka suke daukar nauyin marayu 106. Sauran sun hada da ciyarwar Ramadan da daukar nauyin wani shiri na addini a gidan rediyon bision FM da koyar da sana’o’i. Ta ce daga baya suni kafa bangare na musamman domin aikin da’awa da aka sanya wa suna kismud Da’awa a karkashin Nurul Huda din. Hajiya Halima Sa’eed ta ce sun yunkuro domin kara samar da masallatai a yankin, amma sai suka lura cewa, mutane sun mayar da makabartar Musulmi hanya wasu ma da gayya suke shiga saboda ba ta da katanga, inda a shekarar 2010 suka sayi fili a Sabuwar Unguwa da niyyar gina masallaci a wurin da ake bude masallacin na ranar.
Ta ce bayan sayen filin ba su ci gaba da aikin gininsa ba. Ta ce wata rana mai unguwar da filin yake wanda duk da ba Musulmi ba ne, shi ya jagoranci Musulmin unguwar 10 wadanda suka kai masa kukan suna son filin da za su gina masallaci, inda ya shaida musu cewa ta sayi wannan fili don haka suka same ta suka shaida musu bukatarsu, kuma bayan ta amince ne limamin unguwar na yanzu ya jagoranci wasu Musulmi suka haka ramin ginin masallacin.
Hajiya Halima Sa’eed ta ce, daga nan ne Hajiya Hauwa Abdullahi, matar tsohon Ministan Ayyuka da Sufuri Alhaji Abdullahi Idris ta fara aikin ginin masallacin. “Kuma a lokacin azumin bara an yi taro, inda malamai da daliban makarantar Nurul Huda suka tattaunawa a karshe suka tara gudunmawa don kara aikin ginin masallacin,” inji ta.  
A laccar da ya gabatar wajen bude masallacin wani malamin addinin M usulunci Ustaz Tameem Yusuf, ya bayyana masallaci da cewa shi ne daki na farko a bayan kasa, kuma saboda girman masallaci a wurin Allah ne ya sanya Ya kira shi da dakinSa.
Sheikh Tameem Yusuf ya ce, yayin da gina masallaci yake da muhimmanci kuma yake da lada mai yawa, babban abin bukata a wurin al’ummar Musulmi shi ne su raya masallacin ta wajen tsayar da Sallah a cikinsa da yin zikirori da karantarwa a cikinsa.
Ya kuma shawarci Musulmin unguwar su kula da tsabtar masallacin domin yin haka wani yanki ne na raya masallacin.
Daga nan sai ya shawarci mazaje su sake salon tafiyarsu a wajen neman ilimin addini, ganin yadda a yanzu mata ke kokarin tsere musu a wannan fanni. Sheikh Tameem ya ce, ya halarci wajen wani saukar karatu a wata makaranta inda dalibai mata suka ninnka dalibai maza, lamarin da ya ce kalubale ga mazan.
A jawabin Shugaban Hukumar Alhazai ta Birnin Tarayya, Alhaji Bashir Abba Salanken Nasarawa ya yaba wa kismud Da’awa ne kan kokarinta na yada addinin Musulunci a tsakanin al’umma.
Ya bukaci Musulmi musamman masu hannu da shuni su rika tallafa wa kungiyoyin da suke kokarin tallafa wa mabukata a cikin al’umma.
Sai dai a karshen taron lokacin da aka bukaci a tallafa don ci gaba da aikin samar dab shimfidu da fankoki a masallancin, matan sun sake tsere wa mazan da suka halarci bude masallacin inda Hajiya Maryam Larai Adamu Aleiro ta yi alkawarin sayen darduma biyu daga cikin 14 da masallacin ke bukata a ranar Litinin da ta gabata, yayin da ta ce a bi ta gida a karbo fankoki uku nan take.
Matan sun ci gaba da bayar da gudunmawar kudi, yayin da a gefen ’yan uwansu maza Aminiya ta lura gudunmawar da suka bayar ba ta taka kara ta karya ba. Sai dai Salanken Nasarawa ya ce wadansu daidaikun Musulmi sun yi alkawarin bayar da nasu taimakon ta hannunsa, kuma za su tuntubi kismud Da’awa domin ganin irin tallafin da za su bayar.