Budurawa ta hada kai da saurayinta ya yi garkuwa da ita
Dubun wata yarinya mai shekaru 20 mai suna Tohibat ya cika bayan ta hada baki da saurayinta ya yi garkuwa da ita domin su karbi kudin fansa a wajen iyayenta. Lamarin ya auku ne a ranar 27 ga watan da ya gabata bayan da iyayen yarinyar suka shigar da kara a ofishin ‘yan sanda da […]

Dubun wata yarinya mai shekaru 20 mai suna Tohibat ya cika bayan ta hada baki da saurayinta ya yi garkuwa da ita domin su karbi kudin fansa a wajen iyayenta.
Lamarin ya auku ne a ranar 27 ga watan da ya gabata bayan da iyayen yarinyar suka shigar da kara a ofishin ‘yan sanda da ke Lafenwa a Abekuta, inda suka yi korafin cewa, ‘sun tura ‘yarsu kasuwar Lefenwa da ke daura da unguwar Sabo Abekuta ba su kuma sake jin duriyarta ba, sai daga bisani wani mutum ya kira su a wayar salula ya shaida musu cewa an yi garkuwa da ‘yarsu kana ana bukatar su biya kudin fansa Naira dubu 200. Kakakin ‘yan sanda jihar Ogun ASP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa DPO na Lafenwa CSP kayode Ayilara ya jagoranci jami’an ‘yan sandan sashen bincike har suka gano inda aka boye yarinyar a wani kango. Nan take suka kame mai gadin kangon mai suna Adebayo, wanda ya shaida cewa shi saurayin yarinyar ne, kuma ta hada baki da shi ne ya yi garkuwa da ita domin su samu damar karbar kudi a hannun iyayen ta su yi amfani da su a bikin ranar haihuwarta.
Kwaminshinan ‘yan sandan Jihar Ogun Ahmad Iliyasu ya sanya a tasa keyar saurayi da budurwar zuwa sashen rundunar da ke kula da manyan laifuka da suka hadar da yin garkuwa da mutane, Ahmad Iliyasu ya gargadi iyaye da su lura da tarbiyyar ‘yayansu, domin guje wa janyo masu abin kunya.