Budurwa da bindige saurayi don ya ki sumbatar ta
Ta dirka wa saurayin harsashi a kirji, nan take ya ce ga garinku nan.
Wata budurwa a Jihar Illinois ta kasar Amurka ta harbe wani saurayi har lahira saboda ya ki ya sumbace ta kamar yadda ta bukata daga gare shi.
Wannan al’amarin ya auku ne lokacin da budurwar da saurayin tare da budurwarsa ke tsaka da shan giya a gidansa kamar yadda jaridar Chicago Sun-Times ta ruwaito.
Buduwar mai suna Claudia Resendiz-Florez mai shekara 28, ta harbe saurayin ne bayan ta roke shi da ya sumbace ta amma ya ki, maimakon haka sai ya juya ya sumbaci buduwarsa tana gani.
Hakan ya sa ta nuna masa fushinta, sannan ta ce dole sai ya sumbace ta, a karo na biyu.
Da ya ki sumbatar ta a karo na biyun, sai ta yi wuf ta dauko bindigarsa da ke aje ta auna shi, kafin kiftawa da bismilla har ta dirka mishi harsashi a kirji, nan take ya ce ga garinku nan.
A halin yanzu ’yan sanda na ci gaba da bincike a kan alamarin, ita kuma za a ci gaba da tsare ta har zuwa lokacin da alkali zai yan ke hukunci, kamar yadda dan sandan da ke kula da shari’ar ya tabbatar.