Budurwa da mahaifinta sun gurfana a kotu kan aure
Wata budurwa ’yar kimanin shekaru 15 mai suna Hauwa Mohammed Wobi ta kai karar mahaifi ta mai suna Mohammed Wobi akan ya hanata auren wanda take so. Hauwa wacce bayanai suka nuna cewa mace ce mai yawan canza samari kamar riguna duk da karancin shekarunta, a karshe ta fitar da wani saurayi dan kimanin shekaru […]
Wata budurwa ’yar kimanin shekaru 15 mai suna Hauwa Mohammed Wobi ta kai karar mahaifi ta mai suna Mohammed Wobi akan ya hanata auren wanda take so.
Hauwa wacce bayanai suka nuna cewa mace ce mai yawan canza samari kamar riguna duk da karancin shekarunta, a karshe ta fitar da wani saurayi dan kimanin shekaru 27 mai suna Malam Abdullahi Pakistan wanda mahaifinta bai yi na’am da dabi’unsa ba kuma hakan ya sa ya ce ba zai iya aurar mata da shi ba.
Da wannan dalilin ne ya sa Hauwa ta yi karar mahaifin nata a wata kotu mai zaman kanta da ake kira Great 2 Area Court da ke kusa da fadar Mai Martaba Sarkin Keffi Cindo Yamusa II a karamar hukumar Keffi na Jihar Nasarawa. An fara sauraron shari’ar ce a ranar 20 ga wannan watan da muke ciki.
Budurwar dai ta bada hujjojin ta ne kamar haka: “Ba na yi karar mahaifina ne domin na tozarta ko wulakanta shi ba, a’a sai don na samu nasarar na auri wanda nake so, shi kuma Babana baya so, har ta kai yana zargin ina iskanci. Kullum sai ya yi mini duka, hakan ya sa na bar gidanmu zuwa wajen mahaifiyata a Marabar Gurku wanda daga bisani na yanke shawarar yin kararsa domin kotu ta sanya Babana ya amince na auri wanda nake so watau Malam Abdullahi.
A nasa bangaren mahaifin yarinyar Mohammed Wobi wanda dan asalin Jihar Barno ne kuma mazaunin garin Sabon Gida da ke karamar hukumar Kokona da yake amsa tambayar Alkali ya ce, “ tabbas na ji zantutakn Hauwa, Hauwa ’yata ce ta cikina kuma ban hana ta auren wanda take so ba sai dai ina son in gina mata rayuwa da tubali mai karfi da zai mata karko domin jin dadinta da danginta baki daya, domin na sanya ta a makarantar firamare ta gama kuma na yi farin ciki da sakamakon da ta kawo mini inda hakan ya sa na yanke shawarar sanya ta a makarantar sakandare don ta ci gaba karatu amma ta ce aure za ta yi. Ya ce duk da haka ban ki ba domin aure na gaba da komai musamman a wajen ’ya mace, don haka ya sa na amince ta fito da wanda take so. Wata rana wani saurayi mai suna Musa Suleiman da kansa ya zo ya nuna yana son ta da aure inda na bukaci ya turo. Har tsawon wata shida Musa bai turo kowa don batun auren Hauwa ba, kuma kullum yana zuwa hira, hakan ya sa na dakatar da shi, daga bisani ya dauke ta zuwa Maraban Gurku na wasu watanni bayan ta dawo gida ne sai wasu daga Maraba suka biyo ta har gida da cewa suna son ta da aure, su ma suka kauce ban sake jin duriyarsu ba. Daga nan Hauwa kullum sai canza samari take yi ni kuma ba na jin dadin haka. Wata rana na dawo daga aikin tuki dagaAbuja sai na samu Naira dubu 11 (N11,000) da shinkafa kimanin mudu biyar a wajen matata da cewa wani sabon saurayin ne ya kawo mana da cewa yana son Hauwa da aure, sai na ce ban amince ba tun da bai zo ya same ni mun yi magana baki da baki ba. Daga nan na dauki Hauwa da kudin, da shikafar zuwa gidan Sarkin Sabon Gida, Alhaji Bako Sallau Mai Keffi na ce a mayar wa saurayin kayansa.
Bayan wasu kwanaki kuma sai na ga wasu matasa sun same ni da cewa abokinsu yana son ’yata da aure, wato wannan saurayin da ya aiko min da kudi da shinkafa mai suna Malam Abdullahi Pakistan. Sai na ce masu ba zai yiyuwa ba, domin mutum ne da aka san shi da auri-saki to bayan ’yan kwanaki sai ta bar gida kuma ban san inda ta je ba. Daga nan ne sai na ga sammaci daga kotu cewa ’ya ta Hauwa ta kai karata. Kimanin kwanaki 14 ke nan ban sa Hauwa a ido ba sai yanzu da muka hadu a kotu.”
Sai dai Abdullahi Pakistan, wanda mahaifin Hauwa Mohammed Wobi ke zargin da hure wa ’yarsa kunne bai halarci zaman kotun ba.
Bayan alkali ya saurari jawabin mai kara da kuma wanda ake kara sai ya dage shari’ar zuwa 10 ga watan Nuwamban wannan shekara inda ya bukaci su je su sulhunta juna kafin zagayowar ranar shari’ar.
Amma a tattaunawar da wakilinmu ya yi da Hauwa tana nuna tana so ta auri Malam Abdullahi ne don ta janyo ra’ayin mahaifiyarta wajen dawowa cikin addinin Musulunci. Ta ce mahaifiyarta ta Musulunta ne a lokacin da ta auri mahaifinta Mohammed Wobi amma bayan sun rabu sai ta koma ruwa.