Budurwa mai shekara 14 da ke kiwon manyan macizai

Bidiyon wata budurwa mai suna Chalwa Ismah Kamal mai shekara 14 ’yar kasar Indonesiya ya dauki hankalin jama’a da dama a kafafen sada zumunta bayan an nuna ta tana wasa da manyan macizai shida da take kiwo a gidansu. Hakan ya sa wadansu ke ta jinjina mata kan bajintar da ta nuna. Wadansu da yawa […]

Budurwa mai shekara 14 da ke kiwon manyan macizai

Chalwa Ismah Kamal, budurwa mai shekara 14 da ke kiwon manyan macizai

Bidiyon wata budurwa mai suna Chalwa Ismah Kamal mai shekara 14 ’yar kasar Indonesiya ya dauki hankalin jama’a da dama a kafafen sada zumunta bayan an nuna ta tana wasa da manyan macizai shida da take kiwo a gidansu.

Hakan ya sa wadansu ke ta jinjina mata kan bajintar da ta nuna.

Wadansu da yawa idan suka ga macizan suna tserewa ne saboda razanar da suke yi, musamman a cikin maza akwai wanda yake kamar zai iya hadiye matashin mutum cikin sauki.

Amma Chalwa Ismah cikin sauki take hulda da su abin da ba kasafai da yawan jama’a za su iya yi ba.

Chalwa Ismah ’yar asalin garin Purworejo da ke tsakiyar birnin Java, ta wallafa hotunan yadda take rayuwa da macizan shida a cikin gida ba tare da ta nuna wata fargaba ko tsoro ba, idan tana tare da su.

An yi ta yada hotuna da bidiyon Chalwa Ismah Kamal tana wasa da macizan wanda hakan ya yi matukar daukar hankalin jama’a a shafukan sada zumunta na TikTok da Instagram, kuma ya sa wadansu masu bibiyan shafukan ke barin bakinsu a bude.

Ba kowa ba ne ya san tarihin Chalwa har ta kai ga mallakar wadannan manyan macizai, sai dai ta bayyana wa kafar labarai ta Intanet Lampung77 cewa, ta fara kiwon macizan ne a gida tun tana da shekara hudu kuma ba ta jin tsoronsu idan sun kewaye ta ko sun yi mata zobe.

Sai dai damuwar mutane ita ce rayuwar Chalwa na cikin hadari, kamar yadda dubban masu sharhi ke ta wallafawa a bidiyon da aka watsa a shafukan sada zumuntar.

Chalwa ta yi kokarin bayyana cewa macizan ba su da guba ko kadan, amma ba kasafai ake samun macizan da ba su da dafi ba.

A cikin gidansu Chalwa ba ita kadai ba ce ke hulda da macizan, kamar yadda wani bidiyon da aka wallafa ya nuna cewa wani dan uwan Chalwa bai tsoron macizan.

Chalwa Ismah ta dai fara wallafa bidiyon macizan ne a shafin sada zumunta na Instagram a karshen watan jiya na wani karamin lokaci, amma daga bisani aka gano ta dade tana hulda da macizan na tsawon lokaci.