Budurwa mai yin barcin awa 20 kullum
Emily Rowland wacce ake yi wa lakabi da Sarauniyar Barci, tana fama da cutar barci inda take shafe sa’o’i 20 tana barci mai nauyi kullum. Hakan yana sa ta cikin wani yanayi da ke shafar kwakwalwarta. Yanayin da Emily ke ciki ya sa ba za ta iya shiga cikin sahun masu gasar kyau da ake […]
Emily Rowland wacce ake yi wa lakabi da Sarauniyar Barci, tana fama da cutar barci inda take shafe sa’o’i 20 tana barci mai nauyi kullum. Hakan yana sa ta cikin wani yanayi da ke shafar kwakwalwarta.
Yanayin da Emily ke ciki ya sa ba za ta iya shiga cikin sahun masu gasar kyau da ake yi ba kuma ba ta je makaranta ba, na tsawon shekara biyu da rabi saboda yawan barci.
An dade ana yi wa Emily jinya a asibiti, kuma har yanzu ta kasa yin barcin ita kadai kimanin shekara takwas da suka gabata, kamar yadda iyayenta suka bayyana cewa ’yarsu za ta iya mutuwa lokacin da take yin barci.
Mahaifiyarta Brandi, a koyaushe tana lura da ’yarta inda ta ce, ba za ta iya cewa komai ba game da yanayin fargaba da ke a kan halin da Emily ke ciki.
Emily ’mai shekara 16 da take tare da iyayenta a Georgia ta fara ciwon barci neda yawan ciwon kai tun tana karama.
Sakamakon gwajin lafiyar da aka yi wa Emily shekara takwas da suka gabata ta nuna cutar na da alaka da kwakwalwarta ce don haka take fama da yawan barci.
Brandi mai shekara 42 ta ce, yanayin da Emily ke ciki ya sa ta rasa abokai saboda rashin fita daga gida da ba ta yi kamar sauran yara.
Emily ta ce, “Ina fuskantar kalubale musamman na gudanar da harkokin yau da kullum kamar yadda sauran ’yan mata ke gudanarwa a cikin sauki.” Wasu abubuwa mahaifiyata ce ke yi min saboda yawan barcin da nake yi. Wani lokaci in sanya tufafi ma yana zama min abu mai wahala, akwai lokutan da barci yake kwashe ni a gidan abinci da makaranta ko ina tare da saurayina. Mahaifiyata ita ce ke rike min takardun karatuna idan zan je makaranta.
Emily ta ce, “Ina fargabar yadda rayuwata za ta kasance nan gaba saboda duk tunanina ci gaba da karatu don neman ilimi ya sauya ba kamar sauran ’yan uwana dalibai ba, amma duk da haka ba zan mika wuya ba zan ci gaba da kokari kamar sauran dalibai,” inji ta.
Brandi ta ce da farkon fara makarantar Emily dai ta kasance mai hazaka amma yanzu zamanta a makarantar ya zama matsala, har sai da aka yi mata gwajin cutar da ke damunta aka gano abin da ke damunta.