Budurwa ta fada a rijiya ta mutu a Kwara

Hukumar kashe gobara ta Jihar ta tabbatar da faruwar lamarin.

Budurwa ta fada a rijiya ta mutu a Kwara

Rijiya

An tsinci gawar wata budurwa ’yar shekara 18 mai suna Waliyah a wata rijiya a Jihar Kwara.

Wannan dai na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan an gano gawar wani yaro dan shekara bakwai bayan ya zame ya fada cikin rijiya a yankin Akerebiata, Karamar Hukumar Ilọrin ta Gabas a Jihar Kwara.

Lamarin na baya-bayan nan ya faru ne da misalin karfe 6:46 na yammacin ranar Talata a Ile-Olodo, unguwar Ita Merin a Karamar Hukumar Ilorin ta Yamma.

Wakilinmu ya samu labarin cewa, faduwar matashiyar a cikin rijiyar ya firgita wasu mazauna unguwar.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Hassan Hakeem Adekunle ya ce an mika gawar matashiyar ga Magajin Ile-Olodo, Alhaji Adisa Akanbi.

A cewarsa, “Daraktan hukumar kashe gobara na Jihar Kwara, Prince Falade John, ya gargadi iyaye da su guji sa yaransu debo ruwa a rijiyoyi marasa murfi.”

Kazalika, ya ce sun dauko gawar wani mutum da ya mutu a rijiya bayan an sanar da hukumar game da faruwar lamarin da misalin karfe 5:08 na yammacin ranar Talata.

“Marigayin yana da kimanin shekara 43 kuma an mika gawarsa ga ’yan sanda a Ilọrin,” in ji shi.

’Yan Bindiga: An miƙa wa gwamnatin Kaduna mutum 58 da aka ceto

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna

Barikin Ladi: Asalin garin da yanayin rayuwar mazauna