Budurwa ta fada rijiya a Kano

An mika gawarta ga mahaifinta, bayan tabbatar da rasuwarta a asibiti.

Budurwa ta fada rijiya a Kano

Rijiyar Bajimba: Wadda ake dibar ruwa daga karfe 12 na dare zuwa 6 na safe Hoto daga Magaji Isah

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wata budurwa mai shekaru 16 da ta fada a rijiya.

Budurwar mai suna Aisha Mohammed ta fada a rijiya ne a unguwar Ja’en a ranar Asabar.

“Mun samu kiran agajin gaggawa daga wata Aisha Ibrahim, da misalin karfe 8:45 na dare.

“Nan take muka aike da jami’anmu zuwa wajen da misalin karfe 8:55 na dare, inda aka ciro budurewar aka kai ta asibitin Kwararru na Murtala Mohammed.

“Bayan tabbatar da rasuwarta a asibitin, an mika gawarta ga mahaifinta, Aliyu Mohammed,” cewar Abdullahi.

Wannan na dauke ne cikin wani jawabi da kakakin hukumar, Saminu Abdullahi, ya raba wa manema labarai.

Abdullahi ya kara da cewa har yanzu ba su da masaniya kan dalilin rasuwarta, amma ’yan sanda na ci gaba da bincike kan lamarin.