Budurwa ta jefa kanta cikin teku a Legas

An samu sa-in-sa mai zafi tsakaninta da wanda za ta aura.

Budurwa ta jefa kanta cikin teku a Legas

Kogin Legas

A wani yunkuri na sawwake wa kanta rayuwar duniya, wata budurwa da ba a san ko wace ce ba ta daka tsalle daga kan doguwar gadar nan da ke Legas ta fada cikin teku.

Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), ta ce wannan al’amari ya auku ne ranar a Alhamis a Gadar Third Mainland.

Sakataren Hukumar, Dokta Femi Oke-Osanayintolu, ya ce bayan samun labarin faruwar lamarin sun tura jami’ansu inda suka fara bincike ko Allah Ya sa a gano matar.

Ya ce bayanan da suka tattara sun nuna an samu sa-in-sa mai zafi tsakaninta da wanda za ta aura, kafin daga bisani ta zo ta fada cikin tekun.

Bayanai sun ce tana isa kan gadar a tasi, sai aka ga tafito ba tare da bata lokaci ba ta yi tsalle ta fada.

A halin yanzu, tawagar ceto na ci gaba da bincike a cikin kogin domin gano ta.