Budurwa ta kai harin kunar bakin wake a Kwantagora

Ana zargin cewa wata budurwa ce ta kai harin kunar bakin wake dauke da bam a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kwantagora a Jihar Neja a safiyar shekaranjiya Laraba lokacin da hankulan dalibai suka karkata wurin daukar darasi a ajujuwansu. Fashewar bam din ke da wuya sai rudane ya mamaye makarantar inda akasarin dalibai suka […]

Budurwa ta kai harin kunar bakin wake a Kwantagora
Budurwa ta kai harin kunar bakin wake a Kwantagora

Ana zargin cewa wata budurwa ce ta kai harin kunar bakin wake dauke da bam a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kwantagora a Jihar Neja a safiyar shekaranjiya Laraba lokacin da hankulan dalibai suka karkata wurin daukar darasi a ajujuwansu.

Fashewar bam din ke da wuya sai rudane ya mamaye makarantar inda akasarin dalibai suka yi ta guje-gujen neman tsira.
Budurwar ta tayar da bam din ne a kusa da zauren daukan darussa inda bam din ya yi gunduwa-gunduwa da namanta kuma ya hada da wasu mutum biyu, wani dalibi da almajiri da ke bara.
Wani dalibi da al’amarin ya auku a gabansa ya shaidawa wakilinmu cewa, “Fashewar bam din ke da wuya sai dalibai suka yi ta gudu ba tare da sun san inda suka nufa ba, wadanda suka kamata su yi gabas, sai suka yi yamma, jiki na rawa kuma sun kasa furta ko kalma.”
dalibin ya ce, wasu daga cikin daliban sun ce sun yi ban-kwana da karatun boko ke nan, wasu kuma suka ce ba abin da zai hana su neman ilimi, domin Musulunci ya kwadaita wa mabiyansa neman kowane irinn ilimi.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa aukuwar lamarin ke da wuya sai Shugaban Kwalejin ya yi wa jami’an tsaron waya domin kai dauki, kuma nan take suka isa kwalejin domin tabbatar da komai ya lafa kuma an hana aukuwar irin wannan lamari.
Gwamnan Jihar Neja Dokta Mu’azu Babangida Aliyu ya yi Allah wadai da harin bam din da ya kwatanta da abin takaici ganin cewa jama’an da ba su ji ba, ba su gani ba sun shiga cikin rudanin da ya kai ga rasa rayukan wasu da kuma samun raunuka.
Dokta Babangida Aliyu ya bayar da umarnin a yi wa wadanda suka samu raunuka magani kyauta, tare da samun kulawar likitoci yadda ya kamata.
Kuma nan take ya kira taron majalisar tsaro ta jihar, domin nemo hanyoyin kare rayukan jama’a.
Gwamnan ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu, da kuma yi wa wadanda suka samu raunuka jaje.Ya ce za su yi duk abin da ya kamata don kula da wadanda suka samu rauni.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Neja, Ibrahim Abiodun Gambari ya shaida wa wakilinmu cewa bincikesnsu ya gano cewa budurwar ta yi niyyar tayar da bam din ne a dakin karatun kwalejin, kuma tana hanyar zuwa ne ta taba kunamar bam din ya hallaka ta da mutum biyu da misalin karfe 12:45 na rana.
Ya ce likitoci na kula da mutanen da suka samu raunuka inda aka sallami wadanda raunukansu ba su yi tsanani ba.
Ibrahim Gambari, ya ce a shirye rundunar take don cigaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, kuma ya yi kira ga jama’a su rika da mutanen da ke shigowa cikinsu, musamman bakin fuskoki da ba su da tabbas.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi