Budurwa ta kashe saurayinta kan Naira dubu 50

Takaddamar da ta kaure a tsakanin saurayi da budurwarsa wato Mista Duniya Philemon Tabat  da Uzoamaka Dorathy Nworie kan Naira dubu 50 ta jawo ajalin saurayin a Jihar Ebonyi.Kakakin ’yan sandan Ebonyi ASP Chris Anyawu ya shaida wa manema labarai a hedkwatarsu cewa mamacin ya fito ne daga kauyen Dutsen Makaranta a Jihar Nasarawa kuma […]

Budurwa ta kashe saurayinta kan Naira dubu 50

Takaddamar da ta kaure a tsakanin saurayi da budurwarsa wato Mista Duniya Philemon Tabat  da Uzoamaka Dorathy Nworie kan Naira dubu 50 ta jawo ajalin saurayin a Jihar Ebonyi.
Kakakin ’yan sandan Ebonyi ASP Chris Anyawu ya shaida wa manema labarai a hedkwatarsu cewa mamacin ya fito ne daga kauyen Dutsen Makaranta a Jihar Nasarawa kuma an gano gawarsa ce a juji a mararrabar Onuebonyi an yasar ranar 25 ga watan Disamban bara.
ASP Anyanwu ya ci gaba da cewa “Sarkin kauyen ne da mukarabansa suka sanar mana, mu kuma muka dauki mataki aka dauko gawar aka aje ta a dakin ajiye gawa na Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Ababkaliki. Daga nan muka gayyato budurwar tasa muka yi mata tambayoyi ta yi mana bayani inda ta tabbatar da cewa marigayin saurayinta ne kuma ya zo takanas ta Kano ya same ta har gida da mota kirar Sienna a ranar 23 ga watan Disamban bara. Motar mai lamba Db 815 AAA, a cewarta tun cikin watan Yulin 2012 ta sanya aak sayo mata motar kan Naira dubu 350, idan an kawo mata motar. Ta ce bayan da aka kawo motar sai saurayinta ya ce motar fa kudinta ya haura yadda aka yi cinikinta da farko, a yanzu Naira dubu 700 ne, don haka cikon Naira dubu 350  yake nema a wurinta.”
Jami’in ’yan sandan ya ce “Daga nan ita kuma ta ga mota ta yi mata tsada, sai ta ce ya sayar da motar ya zame sauran kudinsa ya kawo mata nata Naira dubu 350. Ana cikin haka ne sai ta kai shi wurin wani mutum mai suna Ituma Omokwu a ranar 24 ga Disamban 2013, shi kuma ya sayi motar a kan Naira dubu 750. Kuma nan take wanda ya saya ya ba da Naira dubu 700 tare da alkawarin bayar da ragowar Naira dubu 50 a karshen watan Disamban barar. A cewarta bayan da suka dawo gida sai ta bukaci ya ba ta kudinta Naira dubu 350, amma sai ya ba ta Naira dubu  300, saura Naira dubu 50 ya ce idan ya karbo cikon kudin motar zai ba ta.
Ya ce kasa cika alkawarin da Duniya ya yi ya sa fada ya kaure a tsakaninsu inda Uzoamaka ta buga masa wani abu mai nauyi a kai nan take ya fadi kasa warwas rai ya yi halinsa.
Ya ce wadda ake zargi a kokarinta na kada a same ta da laifi ne wajen yada gawar asirinta ya tonu.
’Yan sandan sun ce wadda ake zargin na hannu kuma za su mika ta kotu sannan suna kokarin gano dangin mamacin da ke Jihar Nassarawa domin su zo su karbi gawar dan uwansu.