Budurwa ta kona saurayinta a Kalaba
Wata daliba mai suna Odinke Sylbester, wadda ke karatu a Makarantar Koyon Aikin Jinya ta Jihar Kurosriba da ke garin Kalaba, ta kona shugaban kungiyar daliban makarantar mai suna Ethoti Uno da ruwan zafi, lokacin da ya je yi musu sulhu tsakaninta da abokan karatunta da ke karamar Hukumar Biase, inda suke samun horon sanin […]
Wata daliba mai suna Odinke Sylbester, wadda ke karatu a Makarantar Koyon Aikin Jinya ta Jihar Kurosriba da ke garin Kalaba, ta kona shugaban kungiyar daliban makarantar mai suna Ethoti Uno da ruwan zafi, lokacin da ya je yi musu sulhu tsakaninta da abokan karatunta da ke karamar Hukumar Biase, inda suke samun horon sanin makamar aiki.
Yadda lamarin ya faru kamar yadda shugaban makarantar Adat Adat Obona ya shaida wa Aminiya, “Shugaban daliban ya halarci inda ake ba su horo kan sanin makamar aiki domin ya dinke wata baraka tsakanin Odinke da wata mai suna Uno Obonno, da kuma sauran abokan aikinta kana kuma ya yi masu nasiha, domin su daina shaye-shaye a bainar jama’a tare da mutanen kauyen; ashe ta riga ta tafasa ruwa ta hada shi da gishiri da barkono ba tare da kowa ya sani ba. Sai ta je da dauko ruwan kamar abin arziki, kawai sai ta kwara wa shugaban daliban a jiki. A sakamakon haka, ya kone jikinsa, fatar ta sabule. Nan take aka garzaya da shi asibiti, ita kuma aka kama ta,” inji shi.
Wakilinmu ya ji ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kurosriba Irene Ugbo game da lamarin, ta ce wadda ma ake zargin na hannunsu, ana yi mata bincike.