Budurwa ta maka mahaifinta a kotun Bauchi

Wata budurwa mai suna Maryam Adamu ta maka mahaifinta a gaban kotun Shari’ar Musulunci da ke Tashar Babiye, tana rokon alkalin da ya raba aurenta da mijin da mahaifinta ya daura mata aure da shi, domin ba ta kaunarsa. Ta bayyana wa kotu cewa mahaifinta ya daura mata aure da Sani danjuma mai shekara 48 […]

Budurwa ta maka mahaifinta a kotun Bauchi
Budurwa ta maka mahaifinta a kotun Bauchi

Wata budurwa mai suna Maryam Adamu ta maka mahaifinta a gaban kotun Shari’ar Musulunci da ke Tashar Babiye, tana rokon alkalin da ya raba aurenta da mijin da mahaifinta ya daura mata aure da shi, domin ba ta kaunarsa.

Ta bayyana wa kotu cewa mahaifinta ya daura mata aure da Sani danjuma mai shekara 48 a duniya, ita kuma shekararta 14 kacal a duniya saboda haka ba za ta iya zama da shi ba, domin ya yi mata tsufa.
Maryam Adamu da mahaifinta suna da zama ne a kauyen manu da ke yankin karamar Hukumar Bauchi. Ta bayyana wa kotu cewa tun lokacin da aka daura auren ta gudu daga gidan mahaifinta, domin a cewarta, bai yi mata adalci ba.
Da take zantawa da Aminiya a harabar kotun, ta kara da cewa idan mahaifinta zai iya tunawa ya auri mahaifiyarta ce lokacin yana samari ita kuma mahaifiyarta tana budurwa, don haka yanzu an wuce lokacin da iyaye za su rika auren dole ga ’ya’yansu.
To, sai dai kuma da alkalin kotun ya tambaye ta tun lokacin da aka daura auren, ko ta tare a gidan Sani danjuma? Sai ta bayyana cewa tun lokacin da aka daura auren ta gudu daga kauyensu. Yanzu haka kuma tana zaune ne a gidan ’yar uwan mahaifiyarta da ke Unguwar Nasarawa Jahun, Bauchi.
Alkalin kotun mai shari’a Ishak Magaji ya dage sauraron karar har zuwa ranar 2-11-2015 domin yin nazari da yanke hukunci kuma ya bukaci mahaifin nata da ya je su tattauna da sauran ’yan uwansa game da lamarin.