Budurwa ta mutu tana kokarin kashe kwarkwatar kanta
Wata budurwa mai yin hidimar kasa NYSC a jihar Osun ta rasa ranta a lokacin da take kokarin kashe kwarkwar kanta inda tayi amfani da maganin nan na kashe kwari mai suna sniper. Mai yi wa kasar hidima mai suna Ayomikun Ademorayo na shirye shiryen bikin zagayowar ranar haihuwar ta a daidai lokacin ya rage […]
Wata budurwa mai yin hidimar kasa NYSC a jihar Osun ta rasa ranta a lokacin da take kokarin kashe kwarkwar kanta inda tayi amfani da maganin nan na kashe kwari mai suna sniper.
Mai yi wa kasar hidima mai suna Ayomikun Ademorayo na shirye shiryen bikin zagayowar ranar haihuwar ta a daidai lokacin ya rage kwanaki 10 sai ta tsefe kanta domin tayi gyaran kan da zata gwangwaje a lokacin bikin, ko da ta tsefe kan sai ta lura tana da kwarkwata nan ta nemi maganin kwarin sniper ta wanke kanta da shi.
A cewar makwabtanta bayan da ta gama wanke kan sai ta fita daga hayyacin ta bayan ta daure kan da dan kwali nan da nan aka garzaya da ita asibiti inda ta mutu kafin a kai ga isa asibitin lamarin wanda ya faru a ranar Lahadi ya firgita abokan karatun budurwar da makwabtan ta, suka ce a watan jiya mahaifiyarta ta rasu bayan mahaifinta ya rasu da dadewa lamarin da ya sanya ta zamo marainiya mai kula da kannanta da suke makarantar Sakandare tuni dai Hukumar NYSC a jihar Ogun ta dauki nauyin dawainiyar binne Ayomikun.