Budurwa ta mutu tana tsaka da saduwa da ‘Dan Yahoo’

Kotu ta tisa keyar wani mai damfara ta intanet dan shekara 19 zuwa kurkuku kan zargin lalata da wata budurwa har sai da ta mutu a Jihar Kwara.

Budurwa ta mutu tana tsaka da saduwa da ‘Dan Yahoo’

Ankwa

Kotu ta tisa keyar wani mai damfara ta intanet dan shekara 19 zuwa kurkuku kan zargin lalata da wata budurwa har ta mutu a Jihar Kwara.

’Yan sanda sun shaida wa kotu cewa matashin da ake zargin ya yaudari budurwar mai shekara 17 ne zuwa wani otel a garin Ilori, ya yi mata fyade har ta mutu.

Dan sanda mai gabatar da kara, Abdullah Sanni, ya shaida wa kotun cewa matashin ya yi kokarin tsere daga otle din, amma manajan otel din ya tsare shi, saboda bai biya kudin dakin da ya kama ba.

“Daga bisani manajan otel din ya bi shi zuwa dakin inda aka ga budurwar kwance a cikin jini ba ta motsi.

“Matashin ya shaida wa ’yan sanda masu bincike cewa shi dan damfara ta intanet ne kuma, ya sadu da budurwar, wanda a dalilin haka ne ta fara fitar da jini har ta mutu.”

Daga nan ne alkali Muhammad Dasuki ya ba da umarnin a tsare matashin a gidan yari, ya kuma dage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan nan na Disamba.