Budurwa ta rataye kanta a Kano
Wata buduwar mai kimanin shekaru 15 da aka bayyana sunanta da Bahijja Gombe, ta kashe kanta a gidan da take aiki a Kano. Ana zargin ta kashe kanta ne ta hanyar ratayewa kuma babu wani rubutu da ta bari da ke bayyana dalilinta na kashe kanta. Rikici: ’Yan sanda sun kashe matasa 2 a Kano […]
Wata buduwar mai kimanin shekaru 15 da aka bayyana sunanta da Bahijja Gombe, ta kashe kanta a gidan da take aiki a Kano.
Ana zargin ta kashe kanta ne ta hanyar ratayewa kuma babu wani rubutu da ta bari da ke bayyana dalilinta na kashe kanta.
Kakakin ’Yan Sandan Jihar, Abdullahi Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin, da cewa an tsinci gawar budurwar ce a rataye a cikin gidan.
Ya ce an dauke gawarta zuwa dakin ajiye gawarwaki na asibiti kuma rundunar ta fara gudanar da bincike a kan lamarin don gano musabbabin mutuwar ta.
Mun samu rahoton ne da misalin karfe 10 na daren ranar Asabar cewa Bahijja, yar shekara 15 an same ta rataye a cikin wani gida inda take aiki in ji shi.