Budurwa ta tura wa saurayinta ’yan fashi a Kano

Ana zargin budurwar da yi wa saurayin turen ‘yan fashi saboda ya fasa auren ta.

Budurwa ta tura wa saurayinta ’yan fashi a Kano

Wata budurwa ta gurfana a gaban kotu bisa zargin yi wa tsohon saurayin da zai aure ta turen ’yan fashi da suka kwace masa kudade saboda ya fasa auren.

Ana zargin hannun budurwar da aka gurfanar a Kotun Majistare da ke zamanta a unguwar Gyadi-gyadi, Kano a fashin da aka kwace N800,000 daga tsohon saurayin da suka dade suna soyayya kafin ya janye.

Rahotanni sun nuna masoyan na tsaka da soyayya ne kwatsam saurayin ya fara kauce-kauce, daga baya ya ce su bar wa Allah Ya zaba musu mafi alheiri, a karshe dai ya ce ya hakura da auren ta.

Rashin jin dadin matakin da saurayin ya dauka ne ake zargin ya fusata tsohuwar masoyiyar tasa har ta yanke shawarar yi masa turen ’yan fashi gidansa.

A ci gaba da sauraron shari’ar da aka fara tun kwanakin baya, Mai Shari’a Auwal Yusuf ya ce kotun za ta yi nazari kan bukatun da lauyoyin bangarorin biyu suka gabatar, sannan ya sanya ranar 24 ga Disamba, 2020 domin ci gaba da shari’ar.

Tun da farko lauyan mutum ukun da ake zargi da fashin mai suna Anas Idris, ya ce tun a zaman kotun na baya sun bukaci ta ba da belin wadanda ake tuhumar amma lauyoyin gwamnati da ke cikin shari’ar suka ki cewa uffan.

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano