Budurwa ta yi garkuwa da saurayinta don ta samu kudin biki
Daure shi suka yi sannan suka bi ta kansa da mota
Wata budurwa ta hada baki da ’yan bindiga suka sace saurayin da ya nemi aurenta don samun kudin yin shagalin bikinta da wani.
Matashin na cikin shirye-shiryen auren ta ne aka samu sabani a tsakaninsu suka raba jiha, sai dai Aminiya ba ta san musabbabin sabanin ba.
- Yadda mutanen Jingir suka yi wa ’yan bindiga kofar rago
- Mahara sun bindige mutum 40 a Nijar
- Mai jego da jaririyarta sun tare ofishin gwamna kan rashin biyan albashi
- ’Yan taratsi sun umarci kamfanonin mai su fice daga Akwa Ibom
Amma duk da cewa sun rabun, tsoffin masoyan ba su yanke hulda a tsakaninsu ba, har zuwa ranar da aka yi garkuwa da shi.
Ranar Alhamis da dare ne aka kame matashin mai shekara 50, ba a sake ganin sa ba, sai gawarsa aka tsinta a hanyar Durbawa da ke Karamar Hukumar Kware a Jihar Sakkwato.
Yadda aka sace shi
Majiyarmu ta ’yan sanda ta ce budurwar ta hada baki ne da sabon saurayin da zai aure ta aka sace tsohon saurayin don su samu kudin da za su yi amfani da shi a bikinsu da ke matsowa.
“Da suka gano cewa babu kudi a asusunsa na bakin sai suka kashe shi.”
Wata majiyar kuma ta ce buduwar ta kira tsohon saurayin ne cewa ya same ta a babban shagon kasuwanci na AGG.
Da ya je wurin, sai ya same ta tare da saboda saurayin nata, amma ta ce masa dan uwanta ne.
“A nan ne ta roke shi cewa ya kai su wani wuri, shi kuma ya amince, ya dauke su, ya kai su.
“Bayan ya ajiye su, yana kokarin yin ribas da motarsa sai wata karamar mota kirara Volkswagen Golf ta zo ta tare shi ta baya,” inji ta.
Majiyar ta ce sai mutanen da ke cikin karamar motar suka fito dauke da bindiga kirar AK-47 suka shiga motar mamacin suka wuce da shi.
Ita kuma budurwar da sabon saurayin nata da suke shirin angwancewa suka shiga motar masu garkuwar suka bi bayansu.
Majiyar ta ce masu garkuwar sun kwace wayar mamacin suka duba abin da ke cikin asusun bankinsa, amma sai suka iske babu kudi a ciki a lokacin.
“Sai shugaban masu garkuwar ya zo inda budurwar da saurayinta suka yi fakin, ya ce musu shi fa zai kashe shi tunda ba abin da za a samu a wurinshi.
“Da ya koma sai sauka daure shi, sannan suka bi ta kansa da mota,” inji majiyar.
Wasu majiyoiy na cewa ’yan sanda na tsare da mutum bakwai a halin yanzu, ciki har da budurwar da sabon saurayinta.
Sai dai kakakin ’an sandan a Jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar ya ce budurwar da wani mutum daya ne ke hannun Rundunar.
Ya ce an kwace bindiga kirar AK47 daya a hannun wadanda ake zargin, sannan ana ci gaba da gudanar da bincike.
Saurayin da tsautsayin ya fada a kansa, Abba Abbey Gidan Haki tsohon hadimi ne ga tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.